Sababbin Rahotonni Kan Halin Da Jihar Zamfara Ta Tsinci Kanta a Shekarar 2025
A shekarar 2025, jihar Zamfara ta cigaba da kasancewa daya daga cikin jihohin da suka fi daukar hankali a arewacin Najeriya. Duk da matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal Dare ta kawo sauye-sauye ta fuskar inganta rayuwar jahar dama al’umma gaba ɗaya. Wannan rahoto nawa ya tattara manyan abubuwan da suka faru a jihar Zamfara a cikin 2025 da karshen shekarar 2024.
1. Kasafin Kudi na Naira Biliyan 545:
A karshen shekarar 2024, Gwamna Dauda Lawal ya gabatar da kasafin kudi na Naira biliyan 545 ga Majalisar Dokoki na Jihar domin aiwatar da ayyukan 2025. Kasafin yafi mayar da hankali kan tsaro, kiwon lafiya da ilimi, ciki har da:
(1). Gina tituna a sassan jihar
(2). Kammala aikin filin jirgin sama na Gusau
(3). Tallafawa asibitoci da cibiyoyin lafiya
(4). Fara sabon tsarin daukar malamai da horar dasu
2. Biyan sabon Albashi: Naira 70,000 Ga Ma’aikata
Gwamnatin jihar ta tabbatar da fara biyan sabon albashi na ₦70,000 daga watan Maris 2025. Wannan matakin yazo ne bayan kammala tantance ma’aikata domin kawar da ma’aikatan bogi da kuma bunkasa walwalar masu aikin gwamnati.
3. Ma’aikata: Daukar Malamai 2,000
A watan Janairu, gwamnatin jihar ta bayyana shirin daukar malamai 2,000 don bunkasa ilimi, musamman a makarantu masu fama da karancin malamai. Wannan ya hada da malaman darussa kamar:
(#Lissafi
(#Kimiyya
(#Fasaha
(#Turanci
4. Cigaban Ma’adanai: Da Dage Takunkumai
Gwamnatin Tarayya ta dage haramcin da aka saka a hakar ma’adinai a Zamfara tun 2019. Wannan mataki yana nufin cewa masana’antu da kamfanoni za su iya komawa aiki, wanda zai kara samar da ayyuka da habaka tattalin arzikin jihar.
5. Matsalolin Tsaro: Harin Jirgin Sama da Sace Mutane
Koda yake an samu cigaba a wasu fannoni, har yanzu matsalar tsaro na cigaba da kasancewa babbar barazana. A watan Janairu, rahotanni sun tabbatar da cewa fararen hula da dama sun mutu a wani harin jirgin sama da aka kai bisa kuskure.
Haka zalika, 'yan bindiga sun sace sama da mata da yara 50 a karamar hukumar Maradun a watan Disamba 2024. Wannan ya haifar da fargaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
6. Sarakunan Gargajiya a Harkar Mulki
Gwamna Lawal ya yi kira da a hada sarakunan gargajiya da shugabannin kananan hukumomi domin samun ingantaccen shugabanci da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma. Wannan na daga cikin dabarun rage tasirin ‘yan ta’adda ta hanyar hadin kai da masu ruwa da tsaki.
7. Lambar Yabo da Goyon Bayan Matasa
Gwamna Dauda Lawal ya samu lambar yabo a Kigali, Rwanda saboda jagoranci mai dorewa, yayin da kungiyar matasa ta Arewa ta bukaci a mayar da hankali kan kyakkyawan shugabanci domin magance matsalolin tsaro.
8. Bincike Kan Ma’aikatan Bogi
Gwamnatin jihar ta bayyana cewar bata da cikakken bayani akan adadin ma’aikatanta saboda yawaitar ma’aikatan bogi, lamarin da ya tilastawa gwamnatin tantancewa daga tushe kafin fara biyan sabon albashi da daukar aiki.
Kammalawa
sabon labarin zamfara - bbc hausa shine abinda muka kawo. Zamfara ta fuskanci kalubale da nasarori daban daban. Gwamnatin jihar na kokarin dawo da amana da cigaba a bangarori da dama, yayinda ake cigaba da fuskantar kalubalen tsaro. Matakin dage takunkumin hakar ma’adinai da daukar malamai ya haifar da canji mai dorewa, musamman idan an hada da goyon bayan al’umma da hukumomi.
A matsayin jihar dake da albarkatu masu yawa da karfin matasa, Zamfara na bukatar cigaba da kulawa da tsare-tsare masu kyau domin cimma burin zaman lafiya da cigaba mai dorewa ga kowa da kowa.
Tushen Wannan Rahotonni Na sabon labarin zamfara - bbc hausa:
BBC Hausa
Daily Post Nigeria
Guardian Nigeria
Reuters
AP News
Zamfara State Website