Cikakkiyar Bita Da Inda Za'a Karanta Littafin Gidan Uncle
Littafin Gidan Uncle daya ne daga cikin fitattun littattafan Hausa Novels na zamani da suka karade shafukan yanar gizo tareda haddasa muhawara mai karfi tsakanin jama'a da jin tausayin rayuwar yara, musamman marayu da wadanda ke fama da rashin gata da kulawa. Littafin gidan uncle ya tabo wani bangare ne na rayuwa wanda da dama ke fuskanta kamar – cin zarafi, rashin kariya, da zalunci daga hannun wadanda ya kamata su kare su.
Takaitaccen Bayani Akan Littafin Gidan Uncle:
Littafin Gidan Uncle na dauke da labarin wata yarinya mai suna Fareeda, wacce ta rasa iyayenta tun tana karama, aka tura ta gidan dan uwan mahaifinta (uncle) domin a kula da ita. Duk da cewa an dauki matakin da ake ganin zai taimakawa rayuwarta, amma lamarin ya canza zuwa wani abu mai ban tsoro da bayar da mamaki.
A gidan Uncle, Fareeda ta fuskanci rayuwa mai cike da tashin hankali, cin zarafi, da rashin kulawa, inda ya kamata ace zun zamar mata kariya da bayar da kulawa da tausayi gareta. Amma a Maimakon haka, Uncle ɗinta ya riketa tamkar baiwar gida, sannan daga bisani ya fara cin zarafinta ta fuskar jiki har ma da tunani.
Jaruman Littafin Gidan Uncle:
Fareeda: Jarumar da littafin gidan uncle ya tattauna a kanta. yarinya ce mai hakuri, nutsuwa da tausayi. Duk da wahalhalun da ta fuskanta, ta nuna jarumtaka da dagewa.
Uncle: Kawunta kenan Wanda aka dora masa nauyin kula da Fareeda, amma ya zama barazana gareta. Ya nuna halin rashin imani da rashin tsoron Allah.
Aunty Binta: Matar Uncle wacce ta kasance tayi gum da bakinta (shiru) duk da ganin abinda ke faruwa. Ita irin matan nan ce masu son zama shiru-shiru saboda tsoron kar su lalata zaman aurensu.
Hassan: Yaro ne da ya fahimci halin da Fareeda ke ciki, kuma daga baya ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakonta.
Jigon Labarin Gidan Uncle
Littafin gidan uncle ya kunshi jigon da ya shafi cin zarafin yara, rayuwar marayu, da rashin adalci a cikin gida. Har ila yau, yana magana akan yin shiru-shiru ga mata masu zaman aure, da yadda rashin daukar mataki ke kara ta'azzara rayuwa da darajar mutum.
Darussa Daga Littafin Gidan Uncle
Karamin yaro ba abun wulakantawa ba ne: Yara na da hakkinsu kamar manya. Dole ne a kula da su da adalci.
Yin shiru akan cin zarafi bashi da kyau: Daga lokacin da mutane suka fara yin shiru akan abubuwan da suka san ba daidai ba, to wannan lokaci sun zama wawaye kuma hakan kesa rashin adalci ke karuwa.
Hakkokin yara sun fi komai muhimmanci: Wannan littafin gidan uncle yana nuna cewa kulawa da kare yara ya fi komai muhimmanci, musamman marayu.
Dole ne mata su tashi tsaye su kare kansu da sauran yan'uwansu mata: Aunty Binta wakilci ce a littafin gidan uncle ta mata da ke barin zalunci ya cigaba saboda tsoron mutuwar aure ko rashin ilimi.
Rayuwa bayan wahala tana yiwuwa: Duk da wahalhalu, Fareeda ta samu mafita daga baya, wanda ke nuni da cewa rayuwa ba ta tsayawa kullum cikin wahala dole ne wata rana mutum zai samu mafita.
Salon Rubutun Littafin Gidan Uncle:
Littafin Gidan Uncle an rubuta shi cikin harshen Hausarmu mai sauki da fahimta. Marubuciyar ta yi amfani da kalmomi masu taba zuciya da kwararan misalai don bayyana cin zarafi a gidan da ake kira "na dangi ko yan'uwa." Salon rubutun yana matukar taba zuciyar mai karatu har ya dinga jin zafin halin da jarumar ke ciki.
Tasirin Littafin Gidan Uncle Ga Al’umma:
#Yana kara fahimtar illar cin zarafin yara a cikin gida.
#Yana karfafa gwiwar yara da matasa su fadi gaskiya.
#Yana koyawa mutane su kula da marayu da hakkin da Allah ya ɗora musu a kansu.
#Yana dora nauyin alhaki a kan mata da maza wajen kula da dangi.
Kammalawa
Littafin Gidan Uncle ba wai labari bane kawai don nishadi, a'a wani ilimi ne mai girma da ke bukatar tunani. Domin yana bayyana yadda wasu ke amfani da amanar da aka basu don cutar da wadanda suke kasansu wanda hakan ba dai dai bane, koda yaushe yana kyau muji tsoron Allah. Littafin yana kira ga iyaye, ‘yan uwa, da al’umma gaba daya su daina yin shiru akan zalunci da cin zarafin yara. Yana koya mana cewa rayuwa tana da daraja, kuma kowa yana da hakki – ko yaro ne, ko maraya, ko mace ko namiji koma wanene matsawar ɗan Adam ko dama dabba ce.
Idan kana neman littafin da zai taba tunaninka, ya koya maka darasi, sannan ya faranta ranka da karshe mai dadi – to Littafin Gidan Uncle ya dace da kai mai karatu.