Hausa Novels Complete To Read
Hausa Novels Complete Post Muna yi muku lale maraba da zuwa wannan gida namu na Novels, a yau idan ubangiji Allah ya nufa zamu yi magana akan wasu daga Hausa novels complete wanda za'a iya samun su kyauta, musamman ma ta yanar gizo wanda bloggers ke ɗorawa domin masu karatu su karanta, ko nace masu nema su samu abinda suke buƙata na littafi.
Su dai wadannan littafai suna da matuƙar yawa, domin bayan wanda zan lissafo a ƙasa akwai wasu da dama wanda za'a iya samu a karanta kyauta wala a wannan gida namu ko kuma a wasu kafofin na yanar-gizo. Kamar yadda sunan ya nuna romantic hausa novels complete Littattafan soyayya wanda marubuta masu tsantsan basira suka zauna cikin zurfin nazari da hangen nesa suka bayyana a rubuce, dalilin yin hakan kuwa shine domin a ilmantar, nishaɗantar da kuma hankantar da mai karatu akan wasu lamura na rayuwa musamman ta fuskar soyayya.
Bayan dogon bincike dana gabatar akan Hausa novels complete masu ɗan karen daɗi, shine na rufe da wannan ƙasaitaccen rubutu nawa domin na baka shawara ko ince doraku akan littafin daya kamata ace kun karanta a matsayinku na masu son romantic hausa novels kuma kuma dukkanninsu complete wanda aka ɗora a shafin Wattpad wasu kuma har a kafar sadarwa ta Facebook za'a iya samunsu cikin sauƙi.
Mashahuran Hausa Novels Complete dana kawo a wannan rubutu nawa sun haɗa da:
(1). A jinina take
(2). Gidan gandu
(3). Rabo inya rantse
(4). Yaran mijina
(5). Yayan asali
(6). Captain Sadiq
Babu shakka waɗannan littafai na sama sun amsa sunansu Hausa Novels zafafa wanda kuma a cike suke da gagarumar soyayya, masu iya magana suka ce gani ya kori, kuma nima na aminta abinda ya rage shine mai sauraro ko mai karatu yayi nasa ganin domin tabbatar da labarina.
(1). A jinina take
Wani sashe daga cikin littafin:
Shin me karatu me kake tunanin zai faru a wannan rayuwar aure tsakanin miskili da kuma masifaffiyar matarsa Zeenah? Dama tun a farkon haduwarsu saida ya kaita bango har ta sharara masa maruka guda biyu. Kakakara-kaka to bilal wanda ya kasance tun bayan mutuwar mahaifiyarsa duk abubuwa suka sane masa, shin zai iya budewa wata sabuwar mace zuciyarsa har ta iya kula dashi.
Bari na baku kadan daga cikin wannan Hausa novel complete mai take a jinina take: Tafiya suke cikin sauri tamkar wanda aka yiwa busharar bakin ciki, kasancewar lokacin sallar magariba yayi domin masallatan unguwa har sun soma kiran sallah. Haka ta ƙara nannade kafar wandonta domin suyi saurin tsallaka titi. Wai ke Zeenah kinata faman jana, shin bakya ganin yan kilisa sunata dawowa?
(2). Gidan gandu
Wani sashe daga littafin:
Marubuciyar tace 'Wannan labari nawa kirkirarre ne, wata kila zai iya cin karo da labarin wasu amma ayi sani cewa ban rubuta domin sanin wannan mutane ba, illa iyaka da rubuta ne kawai da zallan tunani da hasashena' Gidan yayi shiru babu wata hayaniya sakamakon kowa ya kama harkokin gabansa, sai kawai kofar kawunmu Shehu wanda dama su wannan kullum cikin rigima suke. Wato inna Larai ce da inna Karima. Can kuma dakin yanmatan gidan, wata zankadediyar budurwa ce ke more barcinta. Shima dai wannan romantic novel yana tareda chakwakiya kala-kala.
(3). Rabo inya rantse
Wani bangare na littafin:
Jerin yan wasan dake cikin wannan novel sun hada da: Faaris Tafida, Sahresh lameedo, Saifullah Tafida, Lailah Turaki, Suhail Turaki, Mia maleek da dai sauransu. Chapter ta farko ta wannan littafi. tikk, tikk, tikk, sautin amo ne keta faman buga alarm, hannunsa ya mika gamida buga saman, alarm ya mutu ba tare da ya mike ba. Yaja bargo ya cigaba da baccinsa.
'Get up real quick bro' Haaris ya faɗa tareda bude labulen dakin. Yatsine fuska ya soma..
(4). Yaran Mijina
Tsokaci daga cikin littafin:
Tashin Madina kenan jiri ya kwashe ta ta fadi kasa a sume. Hafsat na ganin hakan ya faru taja wani tsaki sannan tace "ni dama zaki mutu shegiya".
Can hafsat na zaune sai ta hango ' babansu ta window yana tahowa ai sai ta kwalla wani mufukin kara wayyo Allah! Sannan ta soma jijigata tana fadin Anti madina!! Anty madina!! Anti. Dan Allah ki tashi ai kuwa alhaji jin wannan ihun na hafsa yasa ya shigo da sauri ba tareda yayi ko sallama ba. A rude yake
magana lafiya hafsa bari in kira likita ya juya da hanzari ya nufi ofishin doctor.
Alhaji da shiga ya fara magana a rude likita matata ta suma, likita na jin haka shima cikin hanzari ya tashi ya dauki kayan aiki ya bi bayan shi. Suna shiga Alhaji ya dauki Madina ya dora a saman gado, likita ya soma dubata ya gwada blood pressure yaga yayi sama sosai, nan da nan ya kira malamar asibiti ta mata allura. ya fara yiwa Alhaji bayani na cewa jininta ne ya hau kuma ba'a so mace ta samu matsalan eclampsia dan kashi hamsin sukan iya rasa ransu. An fi buƙatar haka ta faru kafin haihuwa amma kar ka damu idan ubangiji ya yarda zata samu lafiya. Wannan hausa novel nada abin tausayi, soyyaya da ilimin rayuwa.
(5). Ya'yan Asali
Hausa Excerpt:
Amatullah tashi mana, ba zaki tashi ba?, ita dai kara shiga cikin mayafi tayi ta lullube kanta kamar ba ita bace ake cewa ta tashi. Madam Laura mai aikinsu ta kara jan mayafin tana cewa tashi mana amatullah, zaki makara zuwa makaranta fa. cikin shakakkiyar muryar bacci tace "madam Laura baccin minti biyar ba zai cutar dani ba, dan Allah ki barni nayi " tab, aiko ba zai yiwu na barki kiyi ta bacci, kuma ba'a karshen mako ba, ko dai ki tashi ki shirya ko kuma yanzu na kira mamanku. Mikewa Amatullah tayi daga kwanciyar da take ranta duk a bace, sannan tace "shikenan na tashi ba sai kin kira mamanmu ba, yanzu zan shirya sannan na sakko kasan", " shi dai yafi miki, kiyi da sauri saboda karki makara", ba tareda ta kula ta ba ta mike daga kan gadon ta shiga bayan gida ta sakarwa kanta ruwan shower. Wannan complete romantic hausa novel yana da matukar ban sha'awa, tausayi, da jajircewar rayuwa.
(6). Captain Sadiq
Hausa Excerpt:
Karamar yarinya ce wacce ba zata haura shekara goma ba na hango, tana tafe tana faman sharar kuka yadda kasan an mata mutuwa, fara ce sosai ita ba siriri ba, sannan kuma ita ba lukuta ba, ɗan kwalinta ne a hannu hakan ya bani damar na kalli gashin kanta, baƙi ne siɗik, amma saboda tsabar dattinsa yayi jajur, kallo dayan dana yi masa na gane mai laushi ne, rashin kula ne kawai yasa yayi ja haka. Hancinta kuwa shima ba'a barshi a baya ba, domin yayi dama-dama da majina, yarinyar akwai manyan idanu, tana wannan tafiya tana rusa kukan, dan ba tsayawa tayi ba, dai-dai wani matsakaicin gida ta tsaya, gidan kasa ne na talakawa sosai, dan hatta kofar gidan bata samu wni ishashiyar kofar shiga ba, wani uban ihu ta kara saki tamkar an watsa mata ruwan zafi, innarta dake kuryan daki ta fito tana gyara zaninta, wannan labari akwai abin tausayi, soyayya, al'ajabi da kuma darasin rayuwa.
Rufewa
Hausa Novels complete da muka bayyana a sama, sun samu ingantaccen rubuta daga marubutansu wanda suka taka rawa gani kwarai da gaske domin tabbatuwar aikin mai kyau. Hikima tayi aiki haka zalika tunani da hangen nesa sunyi aiki yadda ya kamata a wannan romantic hausa novel. Idan kina bukata zaki iya ziyartan kasuwa domin siyan littafin a zahiri idan kuma kinfi son karatu da waya to wannan gida namu ya taka rawar gani wajen kawo littattafai masu armashi.
Yanzu kawai abinda ya rage muku shine bincike a wannan shafi namu ko kuma a yanar gizo domin kashe ƙwarƙwatan idanunku muna godiya a kullum da ko yaushe ni naku mai gudanarwa nace a huta lafiya da more romantic hausa novels complete.