Alamomin Shigar Ciki A Satin Farko

Alamomin Shigar Ciki a Satin Farko: Yadda Zaki Gane Kin Dauki Ciki Da Wuri:

Alamomin Shigar Ciki A Satin Farko

Alamomin shigar ciki a satin farko wasu manyan sauyi ne da suke faruwa a jikin mace, kuma yana da matukar muhimmanci mace ta gane alamomin da ke nuna cewa tana dauke da ciki tun daga makon farko. Yawancin mata ba sa lura da alamomin da ke bayyana a farko-farkon daukar ciki, sai har ya kai sati 4 zuwa 6.

A cikin wannan rubutun namu, za mu bayyana alamomin shigar ciki a satin farko, da yadda zaki iya gane kina da juna biyu tun kafin ayi gwajin ciki wato (pregnancy test).

Shin Ciki Na Nuna Alamomi Tun A Satin Farko?

Eh, wasu amaren sukan fara ganin canje-canje a jikinsu tun daga kwanaki 5 zuwa 10 bayan saduwa, musamman idan an samu haduwar maniyyi da kwai tun a saduwar farko (fertilization).

Satin farko na daukar ciki yana farawa daga ranar da aka sadu, ko kuma daga lokacin da kwan mace ya hadu da maniyyin mijinta a mahaifa. A wannan lokaci ne ciki ke fara nemo gindin zama a mahaifarki (implantation).

Muhimman Alamomin Shigar Ciki A Satin Farko

1. Gajiya da Kasala

Daya daga cikin farkon alamomin shigar cikia satin farko kenan.

Sinadarin Hormon na ɗiya mace (progesterone) na ƙaruwa da wuri, wanda ke sanya mata jin nauyi da kasala ko bacci.

Zaki iya jin kina son yawan kwanciya ko kina jin nauyin jiki ko kai.

2. Fitar Jini (Implantation Bleeding)

Hakan na faruwa ne kwanaki 6 zuwa 12 bayan saduwa.

Wannan jinin yakan zama bashi da yawa kuma ja mai haske ko kuma ruwan kasa, ba kamar na al’ada da yake fita da yawa ba.

Yana zuwa kwana 1 zuwa 2 kawai.

3. Jin Ciwon Ciki da Ciwon Baya

Na daga alamomin shigar ciki a satin farko samun ciwon da mace ke ji kafin al’ada.

Yana da ɗan sauki ko kuma yakan zo lokaci-lokaci.

Wannan yana faruwa ne yayin da kwai ke kama jikin mahaifa (implantation cramps).

4. Ciwon Nono ko Cikowar Nonuwa

Zaki iya fara ganin nonuwanki sun kumbura, suna kaushi ko suna da zafi fiye da yadda kike ji kafin al’ada.

Zasu iya yin duhu ko kumbura kadan.

Wannan na faruwa ne saboda karin hormones a jikinki.

5. Sauyin Zuciya da Saɓani a Halaye (Mood Swings)

Zaki iya jin kina dariya yanzu, amma daga baya kiji kawai kina jin kuka ko wata damuwa.

Wannan sauyin yana da alaka da canjin hormone a jikin mace.

6. Ciwon Kai da Jiki

Saboda karancin ruwa ko gajiya, mace kan fara jin ciwon kai.

Hakanan kuma zaki iya jin ciwon jiki ko.

7. Yawan Fitsari

Zaki ga kina jin fitsari sosai koda ba ki sha ruwa mai yawa ba.

Wannan yana faruwa ne saboda karin jini da ke ratsa cikin mahaifa da koda.

8. Jin Tashin Zuciya (Nausea)

Alamomin shigar ciki a satin farko a wasu matan yana farawa sa jin amai ko jiri.

Duk da yake, ba duka mata ne ke jin tashin zuciya ba wasu sai bayan sati 4 zuwa 6.

9. Ciwon Kai da Jin Zafi a Jiki

Saboda sauyin sinadarin hormone, jiki yana iya amsawa ta hanyar saka miki ciwon kai.

10. Ƙaƙƙarfan Zazzaɓi (Basal Body Temperature)

Idan mace na bin tsarin zafin jikinta, zata lura cewa zafin jiki yana karuwa ba kamar yadda ya saba kafin al’ada ba.

Wannan yana ɗaya daga alamomin shigar ciki a satin farko ko juna biyu.

Yaya Zaki Gane Wadannan Alamomin Ciki Ne, Ba Al’ada Ba?

Alamomin shigar ciki da alamomin zuwan al’ada suna iya kamanceceniya. Saboda Dukansu suna iya zuwa da:

ciwon nono

ciwon ciki

gajiya

sauyin halaye 

Amma bambanci shi ne:

Alamomin ciki suna da tsayi – wato suna ci gaba da karuwa.

Jinin implantation ba ya da yawa kamar na al’ada.

Idan al’ada ta makara kuma kina jin waɗannan alamomi, akwai yuwuwar ciki a jikinki da yawa.

Yaushe Zaki Iya Yin Gwajin Ciki?

Kina iya yin gwajin ciki na gida (pregnancy test) kwanaki 7 zuwa 10 bayan saduwa, amma yafi dacewa sai bayan kinga kin makara a al’adarki.

Idan al’ada ta makara fiye da kwana 3–5, ki yi gwaji da safe domin samun amsa mafi inganci.

Kammalawa

Alamomin shigar ciki a satin farko na iya bayyanuwa cikin sauƙi amma wani lokacin akwai ɗan tsauri, Wadannan alamomi sun hada da:

#Jin gajiya da kasala
# jini
#ciwon nono da kumburi
#Sauyin zuciya da jin tsoro ko damuwa
#Jin ciwon ciki mai sauki
#Yawan fitsari ko jin zafin jiki

Idan kina jin waɗannan alamomi kuma al’adarki ta makara, yana da kyau ki yi gwajin ciki ko ki je asibiti don karin bayani.
Previous Post Next Post