Alamomin Nakuda: Yadda Zaki Gane Cewa Kin Kusa Haihuwa
Alamomin Nakuda ko ince Nakuda wani abu ne mai matukar muhimmanci ga kowace mace mai juna biyu ta sani, domin hakan yana nufin cewa haihuwa ta matso ko ana gaf da sauke nauyi. Sau da yawa, mata masu juna biyu kan fuskanci alamomin nakuda wanda suke nuni da cewa lokacin da zasu haihu yayi. To kasan yanayin rayuwa kowa da nashi saboda wasu na samun wahalar fahimta.
Saboda kore duk wata matsaniya dame ciki zata iya shiga shine dalilin daya saka sanin alamomin nakuda keda muhimmanci ga kowace mace mai juna biyu.
Ayi sani cewa wannan rubutu nawa na yau yana kunshe da ilimi mai matukar amfani ga duk wasu ma'aurata, domin zan tattauna kuma nayi bayani cikin nutsuwa akan alamomin nakuda na gaskiya, da bambancinsu da nakudar karya (false labor), da kuma duk wasu hanyoyi da mace mai juna biyu zata shirya domin haihuwa cikin salama.
Menene Nakuda? - Labor
Nakuda wani yanayi ne da ke nuna cewa jikin mace mai ciki yana shirin haihuwa. Nakuda tana zuwa ne da matsewar mahaifa (contractions), buɗewar bakin mahaifa, da kuma canje-canjen lamura da yawa a jikin mace wanda ke nuna jariri yana shirin fitowa duniya.
Alamomin Nakuda Na Gaskiya
Ga manya-manyan alamomin nakuda da ke nuna cewa tabbas mace na gab da haihuwa:
1. Ciwon Mara Da Baya Mai Tsanani
Nakuda ta gaskiya tana zuwa wa mace da ciwon mara da kuma ciwon baya, wanda suke somawa a hankali.
Ciwon marar yana ƙaruwa ne da sauri da sauri, sai dai kuma wasu lokutan yana iya lafawa har ki samu damar hutawa.
Idan har kin ji ciwon mara ko baya yana faruwa kowane minti 5 zuwa 10, to yana nufin cewa tabbas nakudar gaskiya kike yi.
2. Tsinkewar Ruwan Mahaifa
Babu ko shakka ɗaya daga cikin manyan alamomin Nakuda shine fashewar ruwan mahaifa, kiyi sani cewa hakan yana nufin lokacinki ya gabato sosai.
Ruwan mahaifar na iya fitowa duka a lokaci ɗaya ko kuma ya dinga fita a hankali.
Idan kin lura da hakan, yana da kyau ku garzaya asibiti.
3. Fitowar Jini (Mucus Plug Discharge)
Na daga alamomin nakuda ta gaskiya fitar wani ruwa mai kauri wanda yake haɗe da jini daga farjin mai ciki, hakan yana nuna cewa mahaifa tana buɗewa.
Fitowar jini ko ruwa mai kauri yana faruwa ne awanni ko kwanaki kaɗan kafin haihuwa.
4. Mahaifa Na Buɗewa (Cervical Dilation)
A lokacin da mace ke yin nakuda, bakin mahaifa yana buɗewa daga cm 1 zuwa cm 10 domin jariri ya samu isasshiyar kofar fita.
Likita ko ungozoma na iya duba buɗewar mahaifarki domin tabbatar da cigaban nakudar.
5. Jin Kamar Zaki Yi Bahaya
Wasu mata masu juna yayin Nakuda sukan ji kamar zasu yi bahaya, to ba bahaya bane, hakan yana nuna cewa jariri yana matsowa ƙasa sosai.
Wannan yanayin yana iya zuwa da zafi sosai idan lokacin haihuwa ya kusa. Dan haka uwa sai kin jure.
6. Gajiya Da Rashin Jindaɗi
Gajiya da Rashin jindaɗi suma na wasu alamomin Nakuda ne na musamman, domin masu juna na iya jin gajiya ko wani matsanancin rashin kuzari kafin haihuwa.
Wasu kuma na iya fama da yawan fitsari.
7. Canjin Yanayin Jikinki (Feeling Different)
Zaki iya jin zafi, sanyi, tashin zuciya, ko canjin yanayi kafin ki sauka. Hakan kuma yana faruwa ne saboda canjin sinadarin hormone a jiki.
Bambancin Nakuda Ta Gaskiya Da Nakudar Karya (False Labor)
Kuyi sani mace na iya samun ciwon nakuda na ƙarya (Braxton Hicks contractions), wanda bashi da wata alaƙa da haihuwa ta gaskiya.
Idan har kina shakka gameda alamomin nakuda da kike ji a jikinki, to yana da kyau ku je asibiti don duba lafiyarki data jaririn dake cikinki.
Yaushe Ya Kamata Ki Je Asibiti?
Ya kamata ku garzaya asibiti idan:
(1). Ciwon nakuda yana zuwa kowane minti biyar ko ƙasa da haka.
(2). Ruwan mahaifa ya fashe.
(3). Kin fuskanci zubar jini mai yawa.
(4). Kin fuskanci matsanancin ciwon baya ko ciwon mara.
(5). Kin ji cewa jaririnki yana motsi ba kamar yadda ya saba ba.
Yadda Zaki Haihu Cikin Doka da Oda.
Nasan wasu zasu yi dariya, amma ba abun barkwanci bane, wato a dokar ƙasarmu Najeriya akwai wasu abubuwa da ake bukata ga duk iyayen sabon jariri suyi.
A Shirya Kayan Haihuwa: Misali
(1). Takardun ID card, katin asibiti, da sauransu
(2). Kayan jariri da na Maijego.
(3). Pampers, da mayafin da za'a rufe jariri mai tsabta.
(4). A samu yan rakiyar mai ciki har zuwa asibiti, kamar kanwa, mahaifiya ko wani naki.
Ki Kasance Mai Kula Da Lafiyarki
Ki ci abinci mai rai da lafiya da ruwa, ke kar ma kisha ruwan pure water, kice ya samo Miki na gora.
Koda yaushe ki kasance cikin shakatawa domin rage damuwa, kuma dan Allah karki takurawa angonki da siyan agwaluma ko yalo 😂.
Kammalawa
Alamomin nakuda saninsu yana da matukar muhimmanci domin ki iya gane lokacin da haihuwa ta kusantoki. Idan kin ji alamomin nakuda na gaskiya kamar ciwon mara mai ƙarfi, fashewar ruwan mahaifa, da buɗewar mahaifa, yana da kyau ki garzaya asibiti domin samun agajin gaggawa.
Ki kasance cikin shiri domin samun haihuwa lafiya, kuma kada ki manta da yin addu’a. Allah ya sauke ku lafiya masu juna biyu!