Alamomin Cikakkiyar Budurwa

Alamomin Cikakkiyar Budurwa: Wato Wacce Ta Balaga

Alamomin cikakkiyar budurwa

Alamomin cikakkiyar budurwa a cikin al’adar Hausawa da sauran al’ummomi, ma'anar cikakkiyar budurwa? shine ana nufin yarinya ko mace wadda bata taba saduwa da namiji ba, wato tana da mutuncinta (budurcinta), kuma ta tsare kanta har zuwa lokacin aure. Yayin da wasu suke tambaya ko akwai wani tabbaci ko alama da ke nuna haka, wasu kuma suna jan kunnen cewa ba duka alamu ne ke zama na gaskiya ba.

A wannan blog post nawa na wannan lokacin, za mu tattauna kan:

#Menene Alamomin cikakkiyar budurwa?

#Alamomin da wasu ke ganin sune alamomin cikakkiyar budurwa 

#Wani abu daya kamata ku sani game da jikin mace

#Abubuwan da mata da maza ya kamata su sani

(#) Menene Ma’anar Cikakkiyar Budurwa?

Cikakkiyar budurwa a al’ada da al’adar gargajiya na nufin:

Mace wadda bata taba saduwa da namiji ba

Wadda ta tsare mutuncinta da jikinta

Wadda ta tsabtace zuciyarta da rayuwarta kafin aure

A cikin fannin kimiyya, ana kiran cikakkiyar budurwa da kalmar "virgin", wato mace wadda ba a taɓa shigar da azzakarin wani a gabanta ba.

Wasu Daga Cikin Alamomin Cikakkiyar Budurwa:

Duk da cewa babu wata hanya tabbatacciya 100% da za a gane mace budurwa ce, akwai wasu alamomi da ake dangantawa da budurci, koda yake ba kowane lokaci suke aiki ba. Amma dai ga wasu daga ciki:

1. Zaman Fatar Budurci (Virginity Seal/Hymen)

Hymen wani karamin yanki ne na fata da ke cikin farjin mace.

A mafi yawancin mata, idan sun fara jima’i ko kuma sun yi wasu abubuwa kamar tseren keke ko motsa jiki, hymen ɗin na iya tsagewa.

A al’ada, ana cewa idan mace budurwa ce, za a iya ganin jini a daren farko (amma ba duka mata ne ke zubar da jini ba, wasu ba su da hymen tun suna yara).

2. Tsabtar Jiki da Kamun Kai

Na ɗaya daga alamomin cikakkiyar budurwa ta zama mai tsafta da nutsuwa, gamida da kunya da kamun kai.

Ba lallai ba ne wannan ya shafi jima’i kai tsaye, amma yana iya nuna fitar yarinya daga kanta da kuma tarbiyya da mutunci.

3. Tsoron Jima’i ko Jin Kunya a Kai

Wasu yan'mata sukan ji kunya ko jin tsoro da batun jima’i ko wani abu mai kama da haka.

Hakan yana nuna cewa ba su saba da irin wannan magana ba kuma sun tsare kansu.

4. Tsauraran Ra’ayi Akan Soyayya

Cikakkiyar budurwa na iya nuna karancin sha’awar mu’amala da samari ko kuma ta fi tsare kanta da sa hannu cikin sha'anin soyayya.

Hakan yakan faru ne saboda ta san matsayin mutuncinta kuma tana so ta jira aure.

5. Fitar Halittar Nono 

Na daga cikin manya-manyan alamomin cikakkiyar budurwa, wato fitar nono a kirjinta, hakan yana nufin ta isa shayarwa.

6. Murya Mai Dadi 

Canjawar muryar mace zuwa mai daɗi da laushi na daga cikin alamomin cikakkiyar budurwa, hakan kuwa na faruwa ne sakamakon sinadarin hormone mai suna oestrogens wanda.

7. Fitar Gashi 

Tsirowar gashi a gaba ko a hammata da daga cikin alamomin cikakkiyar budurwa.

8. Budewar Kwankwaso 

Matsawar budurwa ta cika to babu shakka kwankwasonta yana budewa.

Shin Dukkan Wadannan Alamomin Cikakkiyar Budurwa Gaskiya Ne?

A'a, ba duka alamomin da ake dangantawa da budurci suka kasance gaskiya ba. Misali:

*Matar da ta zubar da jini a daren farko ba lallai ba ne budurwa ce.

*Matar da ba ta zubar da jini ba a daren farko ba lallai ba ne ta taba jima’i ba.

*Hymen na iya tsagewa ba tare da jima’i ba – kamar ta hanyar wasanni, motsa jiki, ko wasu dalilai.

Budurci ba wai jikin mace bane kadai ya nuna shi, har ma da halayya, tarbiyya da amana.

Yana Da Mahimmanci Mu Guji Hukunta Mace Bisa Jikinta Musamman A Makarantu

Akwai mata da suka tsare mutuncinsu har aure, amma saboda hormonal changes ko dalilai na likitanci, jikinsu ba zai nuna alamomin cikakkiyar budurwa ba.

Hakazalika, budurci ba yana nufin kyautatawa mace ba ne kawai, har ma da namiji. Namiji shima zai iya kasancewa saurayi wato ba shi da tarihin jima’i kafin aure, kuma wannan abu ne na girmamawa da daraja.

Yadda Zaki Kare Kanki a Matsayin Budurwa

(1). Ki guji yin soyayya da samarin shaho Maryama wanda ba aure ne a gabansu ba

(2)  Ki kauracewa kallon fina-finan batsa da yawan cudanya da maza

(3) Ki karanta littattafan tarbiyya na soyayya dake sanar da ilimi akan zaman aure

(4). Saka hijabi da tsafta da nisantar abubuwan da ke iya janyo sha'awa 

(5) Ki dinga yin addu’a da neman kariya daga jaraba wato ta jima'i 

Kammalawa

Alamomin Cikakkiyar budurwa sune mace da ta tsare mutuncinta da jikinta, ba wai sai jiki ya nuna ba. Duk da cewa akwai wasu alamomi dake da alaka da budurci, amma a sani ba dukan sune gaskiya ba.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne:
✅ Tsoron Allah
✅ Tarbiyya
✅ Tsabtace zuciya
✅ Fahimtar darajar kai

Budurci ko Samartaka gaba daya daraja ne ga mace da namiji, kuma ana samun lada mai yawan gaske daga Ubangijin halitta idan an tsare kai har zuwa lokacin aure.
Previous Post Next Post