Yadda Amarya Zata Yi A Daren Farko Ga Budurwa

Yadda Amarya Zata Yi a Daren Farko Ga Budurwa 

Yadda Amarya Zata Yi A Daren Farko Ga Budurwa

Babu ko shakka daren farko yana da matukar muhimmanci ga kowace amarya, musamman ga budurwa da ba ta taba yin aure ba. Daren farko yana iya kasancewa da farin ciki, tsoro, da jin kunya ga wasu amaren, amma dai muhallid-shahid shine ki kasance cikin shiri, ki cire duk wata fargaba wato samu natsuwa, da fahimtar angonki.

A cikin wannan bayani namu na yadda amarya zata yi a daren farko ga budurwa, za mu tattauna shawarwari da dabaru da za su taimaka miki a matsayinki na sabuwar amarya wacce bata taɓa yin aure ba, domin ki fuskanci daren farko cikin kwanciyar hankali da jindadi.

1. Fahimta Da Shiryawa Daren Farko

Yana da matukar kyau budurwa ta samu ilimi da bayani gameda aure da kuma yadda ake gudanar da zamantakewar aure. Ana iya samun wannan ilimi daga:

(*). Karanta littattafai ko blog posts akan aure da zamantakewa musamman a wannan gida namu na tsamiyanovels.

(*) Neman shawara daga matan aure masu sanin ya kamata da gogewa ta fuskar iya zama da namiji.

(*) Yin bincike akan lafiyar jikinki da yadda dangantakar aure take kasancewa.

(*) Sanin hakkin aure da yadda zaki sauke haƙƙin, yana taimakawa budurwa ta samu kwanciyar hankali a daren farkonta.

2. Kasancewa Kwanciyar Hankali

Na ɗaya daga cikin matakai na yadda amarya zata yi a daren farko, shine ki kwantar da hankalinki, domin daren farko ba ya nufin dole sai an sadu da juna. Yana da kyau budurwa ta:

(*) Kasance cikin farinciki da nutsuwa – Kar ki cika tunani da tsoro ko kuma damuwa.

(*) Kada kiyi gaggawa – Idan ba ki shirya ba kwanciyar aure ba, to babu matsala a ɗan jinkirta sai jiki ya saba.

(*) Tattaunawa da angonki – Fahimta tsakanin ku ita ce mafi muhimmanci. Idan kina jin tsoro ko fargaba, ki gayawa sahibinki domin muna kyautata zaton zai fahimceki.

3. Tsabta da Shirya Jikin Budurwa 

Domin samun cikakken jindaɗi da samun sauƙi a daren farko, yana da kyau budurwa ta:

(*) Yi wanka da sabulu mai kamshi domin samun isasshiyar tsafta, sabulai kuwa a wannan zamani masu ƙamshi basu da iyaka.

(*) Shan ruwa da cin abinci domin samun kwanciyar hankalin jiki, wato kar ki zauna da yunwa.

(*) Yi amfani da man shafawa mai kyau domin samun ƙamshi mai ɗorewa a jikinki.

(*) Sanya kaya masu kyau da jan hankali domin karawa daren farko nishadi, wato kananan kaya na jeans zasu taimaka matuƙa.

4. Hanyoyin Za'a Magance Jin Zafi Yayin Kwanciya.

(*) Ga duk wata budurwa, yin jima’i a karon farko yana zuwa da ɗan karamin zafi, saboda yayin shigar angonki dole gabanki zai dinga budewa a hankali, wannan shine dalilin dake kawo ɗan karamin jin zafi. Yana da muhimmanci abi a hankali cikin Nutsuwa. Saboda haka:

+ Kiyi wasa da angonki kafin saduwa

+ Amfani da man shafawa (lubricant) idan da  buƙata domin shiga cikin sauƙi.

+ Ango yayi a hankali – Babu bukatar gaggawa domin hakan na iya haifarwa da amarya rauni.

+ Yin numfashi a hankali kuma ki saki jikinki domin rage jin ciwo.

Note:::::::  Idan zafin ya yi yawa ko jini ya yi yawa fiye da yadda aka saba, yana da kyau a nemi shawarar likita.


5. Rage Tsoro da Jin Kunyar Magana da Ango 

A wasu al’adu, ana koyawa budurwa ta ji kunyar angonta a daren farko, amma aure yana buƙatar fahimta da yarda tsakanin ma’aurata. Yana da kyau amarya ta:

+ Yi magana da mijinta

+ Fahimci cewa soyayya da tausayi su ne ginshikin zaman aure.

+ Kada kiji kunyar tambayar mijinki abubuwan da baki fahimta ba.

+ Fahimtar juna suna taimakawa wajen samun farinciki da jin daɗin rayuwar aure.

6. A Nemi Likita

A wasu lokuta, budurwa na iya fuskantar matsaloli kamar:

+ Zafin da ba ya ƙarewa ko yawan jini bayan daren farko.

+ Fargaba da ke hana saduwa da ango a karo na gaba, shiyasa yana da kyau ayi a hankali.

+ Yawan bushewar gaba dake haifar da ciwo.

Idan irin waɗannan matsaloli sun taso, yana da kyau a nemi shawarar likita domin samun shawara da magani.

7. Muhimmancin Addu’a

A matsayinmu na musulmai ko masu bin addinin Musulunci, yana da kyau ma'aurata su fara da addu’a da niyyah mai kyau a daren farko. Yin addu’a yana kawo albarka da samun ya'ya na gari. 

Kammalawa

Wannan shine yadda amarya zata yi a daren farko ga budurwa Post, ayi cewa daren farko baya bukatar gaggawa ko matsin lamba. Abu mafi muhimmanci shi ne:

+ Kasancewa cikin shiri..

+ Kada ki damu da kowane irin ra’ayi na mutane – aurenku naku ne, ku fahimci junanku.
Previous Post Next Post