Sunayen Larabawa Masu Dadi da Ma’anoninsu
Sunayen Larabawa masu dadi suna da kyau da kuma kyakkyawar ma’ana saboda yawanci suna da alaka da addini, dabi’u, ko kuma kyawawan halaye. Akwai sunaye masu kyau ga 'yan mata da kuma yan maza, waɗanda ake amfani da su a ko’ina na garuruwan larabawa, musamman a cikin Musulunci da al'adar Larabawa.
A cikin wannan blog namu na yau, za mu lissafa sunayen Larabawa masu dadi tareda bayar da ma’anoninsu da kuma irin mutanen da suka fi dacewa da a saka musu wannan sunaye.
Sunayen Larabawa Masu Dadi Ga 'Yan Mata (Mata)
Aisha
Ma’ana: Mai rai, mai lafiya, mai albarka
Dalili: Sunan matar Annabi Muhammad (SAW)
Zainab
Ma’ana: Sunan shuka mai kamshi gamida kyau
Dalili: Sunan ɗaya daga cikin 'ya'yan Annabi Muhammad (SAW)
Fatima
Ma’ana: Wacce ta tsarkake kanta daga miyagun halaye
Dalili: Sunan diyar Annabi Muhammad (SAW)
Maryam
Ma’ana: Mai tsoron Allah, sannan kuma mai tsarki
Dalili: Sunan mahaifiyar Annabi Isa (AS)
Khadija
Ma’ana: Wacce ta fi sauri, wacce ke da hikima
Dalili: Sunan matar farko ta Annabi Muhammad (SAW)
Hafsa
Ma’ana: Jarumar mace, mai ƙarfi
Dalili: Sunan ɗaya daga cikin matan Annabi Muhammad (SAW)
Samira
Ma’ana: Wacce ke bayar da farin ciki, mai ƙara nishadi
Dalili: Sunan da ke nuna farin ciki da kyakkyawar mu’amala
Yasmin
Ma’ana: Sunan fure mai kamshi
Dalili: Sunan da ke nuni da kyau da kum kamshi
Rukayya
Ma’ana: Mai daraja, mai ƙima
Dalili: Sunan ɗaya daga cikin ‘ya’yan Annabi Muhammad (SAW)
Amal
Ma’ana: Fata, buri, bege
Dalili: Sunan da ke nuna fatan alheri da bege
Sunayen Larabawa Masu Dadi Ga Maza
Muhammad
Ma’ana: Mai yawan yabo, wanda ake godiya gareshi
Dalili: Sunan Annabin Musulunci (SAW)
Ahmad
Ma’ana: Wanda aka fi yabawa
Dalili: Daya daga cikin sunayen Annabi Muhammad (SAW)
Ali
Ma’ana: Mai daraja, mai girma
Dalili: Sunan Khalifa na huɗu kuma ɗan gidan Annabi Muhammad (SAW)
Hassan
Ma’ana: Kyau, nagarta
Dalili: Sunan jikan Annabi Muhammad (SAW)
Husain
Ma’ana: Ƙaramin kyakkyawa, mai kyau da daraja
Dalili: Sunan jikan Annabi Muhammad (SAW)
Yusuf
Ma’ana: Kyakkyawa, mutum mai daraja
Dalili: Sunan Annabi Yusuf (AS)
Ibrahim
Ma’ana: Babban uba, uba mai alheri
Dalili: Sunan Annabi Ibrahim (AS)
Isma’il
Ma’ana: Wanda Allah ke jin kukansa
Dalili: Sunan Annabi Isma’il (AS)
Khalid
Ma’ana: Mai ɗorewa, wanda ba ya mutuwa
Dalili: Sunan shahararren jarumin Musulunci, Khalid bn Walid
Salim
Ma’ana: Lafiyayye, mai salama
Dalili: Sunan da ke nuni da lafiya da zaman lafiya
Yadda Ake Zabar Sunan Da Ya Fi Dacewa
Idan zaku zaɓi suna, yana da kyau kuyi la’akari da:
Ma’anar sunan – Shin sunan mai kyau ne kuma yana da kyakkyawan fassara.
Tarihin sunan – Yana da kyau a zaɓi sunayen Annabawa ko sahabbai domin suna da albarka.
Sauƙin furta sunan – Ya kamata ya kasance mai sauƙin faɗa da fahimta.
Kammalawa
Sunayen Larabawa masu dadi suna da kyau kuma suna da ma’ana mai kyau. Idan kana neman sunan da ya dace da ɗanka ko ‘yarka, yana da kyau ka zaɓi wanda yake da ma'ana mai kyau da daraja.