Lallen Gam Na Zamani: Kyawawan Zanen lalle masu kyau
Babu ko shakka lalle yana daya daga cikin tsofaffin al'adun mata a duniya, musamman a Afirka da Asiya. A gida Najeriya ma ba'a bar su a baya ba domin matan aure, yan'mata, har ma da zawarawa, na Arewa suna yin ado da lalle domin yin kyau, domin masu iya magana sun ce Idan kana da kyau to ka ƙara da wanka. Lalle yana da matukar muhimmanci, musamman a lokutan bukukuwa kamar biki, suna, da sauran al'amuran farinciki na taron jama'a.
A wannan lokaci da muke ciki, lallen gam na zamani ya shahara sosai saboda kyawunsa da kuma saukin aikinsa. Saboda yana da bambanci da lallen gargajiya ta launinsa da saukin haɗawa, haka zalika yana da tsawon karko a fatar mace, kuma yana fitowa da cikakkiyar sifa da kyau.
A cikin wannan bayani namu, za mu yi bayani dalla-dalla kan lallen gam na zamani, nau’ikansa, yadda ake amfani da shi, da kuma wasu kyawawan zane da ake yi da shi.
Menene Lallen Gam?
Lallen gam na zamani wani nau'in lalle ne da mata suke amfani da shi domin yin zane a hannayensu ko kafafu mai daukar hankali. Ana samunsa a cikin mazubin tube ko cone, kuma yana da launi mai duhu fiye da lallen gargajiya. Wato lallen gam na zamani yana yin duhu sosai fiye da lalle da kakanni suke amfani dashi wato na gargajiya.
Babban bambancinsa da lallen gargajiya shine:
- Yana bushewa cikin kankanin lokaci.
- Launinsa yafi duhu kuma yana daɗewa a fata.
- Ana iya amfani da shi wajen yin zanen zamani masu jan hankali wanda na gargajiya ba zai iya aikata hakan ba.
Nau’ikan Lallen Gam Na Zamani
Akwai nau’ikan lallen gam na zamani da ake amfani da su, daga cikin su akwai.
1. Lallen Gam Mai Launin Baki
Wannan shine lallen gam na zamani mafi shahara kuma mafi dacewa domin yin zane ga amarya ko Uwargida mai tarewa. Yana ba da launi mai duhu sosai, wanda ke kara sanya hannun mace ya fita sosai yayi kyau fiye da yadda bakwa tsammani.
2. Lallen Gam Mai kalar Ruwan Zinariya
Wannan nau’in lallen gam na zamani shima yana da ɗan karen kyau, musamman idan ana so a hada shi da wasu kalar kamar fari ko ja mix kenan.
3. Lallen Gam Mai Launin Ja
Yawancin matan aure na amfani da wannan don kara ado a hannuwa ko kafa.
4. Lallen Gam Mai Launin Fari
Ana amfani da wannan lallen gam na zamani don yin zane mai ɗan karen kyau shima. Kuma ana iya hada shi da wasu launuka domin karin kyau. Kowace kala tana da kyau, sai dai kuma wata kalar zata fi miki kyau akan wata. Sai ki gwada kiga wacce tafi Miki.
Yadda Ake Yin Lallen Gam Na Zamani
Ga matakai masu sauki da zaki bi wajen yin lallen gam domin yayi yadda kike so, wato yayi kyau canca-rancas a jikinki.
Abubuwan Da Zaki Bukata
- Lallen gam (cone ko tube)
- Cotton wool (domin tsaftace zane)
- Man shafawa (kamar Vaseline ko olive oil)
- Tissue ko auduga
Matakan yinsa cikin sauƙi
Mataki 1: Tsabtace Hannunki ko Kafa
Kafin ki fara zanen lallen gam na zamani, yana da kyau ki tabbatar da cewa hannunki ko ƙafarki da za'a yi zanen a kai kin wanke su sun bushe, babu ko alamar datti.
Mataki 2: Zabi Zanen da kike so
Akwai kalar zane daban-daban da ake iya yi, daga cikinsu akwai na Indiya, Larabawa, da kuma na Hausa. Za ki iya kallon hotuna ki zaɓa ko kuma a kirkiri naki na musamman ayi miki.
Mataki 3: Fara Zanawa
A bude lallen gam a hankali, sannan a fara zana layi kan layi cikin nutsuwa domin samun cikakken zane mai kyau.
Mataki 4: Jira Ya Bushe
Lallen gam yana daukar mintuna kamar 30 zuwa 60 kafin ya bushe sosai yayi yadda ake so. Idan kuma ana so ya fi yin kyau, to a barshi na tsawon awa daya ko fiye da haka.
Mataki 5: Wanke Lalle
Bayan ya bushe raƙayau, zaki iya share shi da auduga ko tissue ko ki saka ruwa ki wanke. Zaki iya shafa man shafawa baya wankewa domin ya ƙara karko.
Ire-iren Zanen Lallen Gam Na Zamani
Ga wasu daga cikin kyawawan zanen lalle na wannan zamani da ake yi:
1. Zanen Indiya
Wannan nau'in zane yana dauke da tsari mai rikitarwa da layuka masu santsi da kyau. Wanda sai kwararriyar mai lalle take iya shi kuma yana da tsada.
2. Zanen Larabci
Zanen Larabci yafi sauki, yana dauke da furannin ado da layuka masu kyau.
3. Zanen Hausa
Zanen Hausawa yana da saukin fahimta, kuma yafi mayar da hankali kan geometric patterns da siffofin hausawa masu kyau.
4. Zanen Zamani
Ana hada lallen gam na zamani da glitters ko gems.
Shawarwari Domin Lalle Yayi Kyau
- Kada ki wanke hannu da ruwa bayan yin lalle har sai bayan awanni 6 wato ya bushe sannan raƙayau kenan domin samun launi mai kyau.
- Ki shafa man shafawa domin ƙara karfafa launin lalle.
- Ki zaɓi lallen gam mai inganci domin samun kyakkyawan sakamako.
- Idan kina son karin launi, kina iya shafa man kwakwa ko man zaitun bayan an cire lallen.
Ko Shakka Babu
Lallen gam na zamani yana kara kyau da ado ga mata. Yana da bambanci da lallen gargajiya saboda yadda yake da launi mai duhu, kuma yana bushewa da sauri, sannan yana da dadin amfani.
Idan kina son yin ado mai kayatarwa, to lallen gam shine zabin da ya dace. Ki gwada sabbin nau’ikan zane don samun sabon salo da kyau mai jan hankali.