Soyayya Da Rainin Wayo: Labarin Soyayya Mai Ban Dariya
First Story
Akwai wani saurayi mai suna Nasiru, matashi ne mai bala'in son yan'mata, amma yana da wata matsala guda ɗaya, wato shi a rayuwarsa ba ya son kashe kuɗi! Duk inda ya je, yana ƙoƙarin ya samu budurwa wacce zata so shi ba tareda ya kashe mata ko sisi ba. Wato dai a takaice wannan labarin soyayya mai ban dariya ya tabbatar da cewa Nasiru mugun ɗan mammaƙo ne.
Ranar wata Lahadi, yana tafiya a kasuwa yana ƙwambo da wayarsa kamar wani mai kudi, sai ya hango wata kyakkyawar budurwa mai suna Zainab tana siyan kayan kwalliya. Haba wa! mutuminka bai yi wata-wata ba, ya nufi inda take tareda tura mata wani murmushi.
Nasiru: "Gaskiya yan'mata Allah ya halicce ki da kyau. Idan da za'a kwana a cikin ido, to ni da ke za mu kwana!"
Zainab: ("Wannan wani irin dan rainin wayo ne?") "Nagode, amma Malam ba'a kwana a ido, a cikin gida ake kwana."
Nan da nan Nasiru ya fahimci cewa Zainab ba irin waɗanda za a raina bace. Amma saboda ƙwarin gwiwa irin nasa haka ya ɗora da dabarunsa.
Nasiru: "Gaskiya tun da na hangoku zuciyata ta kama da wuta. In ba ki amince ba, wallahi yau kam ba zan iya cin abinci ba."
Zainab: " A'a, kaci abinci mana, ai bani ce maganin yunwa ba!"
Nan fa Nasiru ya ji kamar an watsa masa ruwan sanyi a fuska, amma haka ya daure. Ya tsaya tunanin hanya mafi sauki da zai ci ribar soyayyar Zainab ba tareda kashe mata kuɗi ba. Sai ya yanke shawarar nuna mata yana da hali.
Nasiru: "Ki bani lambar wayarki mana, ko ba komai dai zamu tattauna a WhatsApp."
Zainab ta lura da salon Nasiru, sai ta ƙyale shi. Ta ce, Tom "Bari na saka maka lambar a wayarka." Haka Zainab ta saka masa lamba ta wuce abinta.
Nasiru yana murna, bai sani ba, sai da ya koma gida ya nutsu wai shi zai kira yarinya mai kyau, Nan ya soma rangadawa lamba kira, yayi kira har ya gaji, ai mutuminka daga baya ya gane cewa lambar da ta saka masa ta ’Yan Sandan Kiran Gaggawa ce! 😂🙌
Sai kawai ya zabura yana faɗin, "Wannan wane irin rainin wayo ne?"
Kammalawa
Daga wannan labarin soyayya mai ban dariya, za mu fahimci cewa soyayya bata son ƙarya da rainin hankali. Idan kana son soyayya ta gaskiya, dole ne ka zama wanda yasan me yake, kuma ka san cewa ba komai ake samu da rainin wayo ba.
_________________________________________
Malam Tanko da Soyayyar Internet: Labarin Soyayya Mai Ban Dariya
Second Story
Malam Tanko, wani dattijo ne ɗan shekara 55, yana da aurensa har ma da yara shida. Bai taɓa yin soyayya da wata mace a rayuwarsa ba sai dai matarsa, Hajiya Indo. Yana zaune a garinsu dake karamar hukumar Kano yana sana’ar siyar da doya.
Wata rana, wani saurayi a kasuwa ya nuna masa wayar salula. Ya ce, “Baba, ga Facebook, za ka iya samun abokai har ma da budurwa.” Malam Tanko ya girgiza kai yace to, yana dawowa gida sai ya cewa ɗansa, Musa, ya bude masa asusun Facebook.
Bayan kwana biyu kacal, sai wata budurwa mai suna Queen Latifa ta turo masa saƙon soyayya. Ta ce, “Hello my love, I am from London, and I love you.” nan fa Malam Tanko ya shiga firgici. Ya dinga tunanin ya aka yi budurwa ‘yar Ingila ta kamu da sonsa haka?
Ba tareda bata lokaci ba, sai ya fara kwasar kalmomin soyayya daga waƙoƙin zamani. irin su , “Baby, you are the sugar in my kunu, without you, my heart is like fura without nono.” Queen Latifa ta yi dariya ta ce, “Awww, you are so romantic.”
Daga nan sai Malam Tanko ya fara yi mata kyauta. Ya sayi katin waya ya tura mata, ya ce, “Ki kira ni mu yi soyayya.” Ita kuwa sai ta ce masa tana son kudin jirgi domin ta zo wajensa Najeriya. Malam Tanko ya shiga tsalle-tsalle yana murna. Saboda shi kawai ya riga ya ji a jikinsa zai auri Baturiya.
Haka dai malam Tanko na labarin soyayya mai ban dariya ya cigaba da soyewa a facebook, wata rana bayan ya aika mata Naira dubu hamsin ₦50k, sai Queen Latifa ta ɓace kamar hayakin doya. Malam Tanko ya je ya shaidawa dansa Musa abinda ya faru. Musa ya kalli mahaifinsa ya dinga dariya 😂, malam Tanko ya ce 'kai bana son iskancin banza, kaga jairin yaro “Baba, ai an damfarke ka! Wannan ba Baturiya bace, yan damfara ce.”
Malam Tanko ya dafe kai, yana cewa, “Wayyo! Lallai an cuce ni! To da na biya sadaki, da ya ya zan yi kenan?”
Daga wannan rana, Malam Tanko ya daina Facebook. Kuma idan aka yi masa maganar soyayya, sai ya ce, “Ni dai yanzu doya kawai nake so, ba soyayya ba!” 😂