Girman Nono da Hulba, Domin Kara Girmansa
Girman nono abu ne da yawancin mata ke yawan tambaya a wannan gida namu, musamman idan suna son samun ƙarin ƙiba a mamansu. Wasu mata suna da ƙananan nonuwa saboda yanayin halitta, nau’in jiki, ko hormones, yayin da wasu matan ke son su ƙara girman nono da Hulba ta hanyar magungunan gargajiya.
Daga cikin hanyoyin da mata ke amfani da su domin ƙara girman nono, akwai hulba (fenugreek) saboda tana daga cikin mafi shahara. Hulba tana ƙunshe da sinadaran da ke taimakawa wajen hawan hormones da kuma ƙara girman halittar nono.
A yau, zamu tattauna:
(#1). Matakan girman nono da yadda ake auna su
(#2). Amfanin hulba wajen girman nono
(#3). Yadda ake ƙara girman nono da Hulba.
Matakan Girman Nono (Breast Sizes)
Ana auna girman nono ta hanyar girman bireziyya, wanda ke ƙunshe da band size (ƙirji) da cup size (tudun nono da kansa).
Hanyoyin Auna Girman Nono
(1). A auna girman ƙirji (Band Size)
(2). Ayi amfani da ma’aunin likita a zagaye ƙarƙashin nonon dashi (ƙugun ƙirji).
(3). Idan adadin ya nuna 32, 34, 36, 38 da dai sauransu, to shine band size wato girman kirji.
#1. A auna tudun nono (Bust Size)
#2. A saka ma’aunin a tsakiyar nono sannan a auna shi.
Idan akwai bambanci tsakanin tudun nono (bust size) da kugun ƙirji (band size), to ana samun cup size kamar haka:
***Misali, idan band size ɗinki 34 ne kuma bust size ɗinki 37, to bambanci shine 3 inches, wato kamar ace 37-34 kinga uku kenan zai rage, to hakan yana nufin cup ɗinki C (34C).
Yadda Hulba Ke Taimakawa Wajen Kara Girman Nono
Hulba tana da phytoestrogens, wato sinadaran da ke kwaikwayon aikin estrogen a jikin mace wajen cikar duk wasu halittun mace a jikinta kamar Murya mai daɗi, girman nono da kuma girman ƙugu.
Amfanin Hulba Wajen Girman Nono
(+). Tana ƙara hormone na estrogen da prolactin, wanda ke haɓaka girman nono har ma hips.
(+). Tana haɓaka nono ta hanyar ƙara nama a cikinsa.
(+). Tana hana nono ya shanye ko yayi yaushi, musamman ga mata masu shayarwa.
(+) Tana sa nono ya yi ƙiba da kyau ba tareda wata illa ba.
Yadda Ake Amfani da Hulba Don Girman Nono
1. Shan Ruwan Hulba
∆> Ki tafasa hulba a cikin ruwan zafi na tsawon minti 10, sannan ki sha.
∆> Za ki iya ƙara zuma ko madara a ciki don ƙarin daɗi.
∆> Ana sha sau 1-2 a rana.
2. Yin Tausa Da Hulba (Massage)
∆> A hada garin hulba da ruwa ko man zaitun.
∆> A shafa a nono sannan a yi tausa a hankali tsawon minti 10-15.
∆> Yin hakan kullum na taimakawa wajen ƙara girman nono da Hulba.
3. Shan Hulba Da Madara
(₦). Hulba da madara suna aiki tare domin girman nono.
(₦). Ki zuba hulba a cikin garin madara, sannan ki sha a kowacce rana kamar sau uku.
4. Amfani Da Kayan Hadin Hulba A Abinci
Ana iya amfani da Hulba a cikin abinci kamar shayi, tuwo, da sakwara.
Ana iya amfani da ita cikin ɗan-wake, faten wake ko doya, ko cikin miya.
Yaushe Za'a Ga Canji?
Samun girman nonon da hulba yana buƙatar hakuri da cigaba da amfani akai akai. Amma da yawa, zaki iya ganin canji cikin sati 2 zuwa wata 1, amma wasu na iya ɗaukar lokaci mai tsawo.
✔ Mafi kyau shine ayi amfani da hanya ta biyu ko ta uku domin samun sakamako cikin sauri, kamar girman nono da hulba ta hanyar tausa.
✔ Ki cigaba da amfani da ita domin samun cikakken sakamako.
Illolin Hulba (Side Effects)
Duk da cewa hulba tana da amfani sosai, yana da kyau a san tana da wasu illolinta:
(1). Yawan shanta na iya haddasa ciwon ciki ko gudawa.
(2). Mata masu ciki su guji amfani da ita sosai, domin tana iya haddasa ciwon ciki mara dalili.
(3). Zai fi kyau a nemi shawarar likita kafin fara amfani da ita, musamman idan kina da wata matsala ta lafiya.
Kammalawa
Hulba tana daga cikin ingantattun hanyoyin gargajiya da mata ke amfani da su don ƙara girman nono da Hulba. Ta hanyar shan ruwan hulba, yin tausa da ita, da amfani da ita cikin abinci, mace na iya samun girman nono ba tare da amfani da magunguna masu illa ba.
✔ Idan kina son hanyoyi marasa cutarwa don ƙara girman nono, to hulba hanya ce mai sauƙi da inganci.
✔ Kiyi amfani da ita da hankali, domin gujewa matsalolin da ke tattare da yawan amfani da ita.