Azabar Daren Farko: Abubuwan da Suke Haddasata da Yadda Ake Maganinsu
Daren farko yana ɗaya daga cikin muhimman darare a rayuwar kowace sabuwar amarya, musamman idan budurwa ce wadda ba ta taɓa yin aure ba. Yawancin mata sukan ji tsoro ko damuwa game da abin da zai faru, wasu kuma suna jin labaran ciwo da Irin azabar daren farko da ke faruwa.
A wannan blog namu mai taken azabar daren farko, zamu ƙaryata wasu abubuwan wanda ba gaskiya ba game da azabar daren farko, sannan mu bayyana dalilan dake haddasa ciwo a daren farkon wanda shine dai ake nufi da azabar daren farko ba wani abu ba. Idan kuka biyo mu ma har da yadda za'a rage duk wani radadi domin jindaɗin wannan dare mai muhimmanci ga sabon aure.
Shin Azabar Daren Farko Dole Ce?
A gaskiya, babu wata doka dake cewa dole sai daren farko ya kasance miki mai azaba ko samun wani ciwo yayin hulɗa da angonki. Sai dai kawai abinda muka sani shine wasu matan sukan fuskanci ɗan jin zafi, wasu kuma basa jin wani zafi sosai.
Dalilan dake haddasa jin zafi sun haɗa da:
Tsoro da Kuma Fargaba – Idan mace tana cikin tsoro ko kuma fargabar azabar daren farko, to fa tsokokin gabanta suna matsewa ne, wanda hakan ka iya haddasa mata ciwo.
Rashin Shiryawa – Idan ba'a samu isasshen Wasanni tsakanin amarya da ango ba kafin saduwa, yana iya haddasa jin ciwo.
Rashin Lubrication (Ruwan Ni'ima) – Idan mace ba ta gama shirya jikinta ba da kayan mata, to babu shakka gabanta zai iya kasancewa a bushe, wanda ke haifar da azabar daren farko.
Budurci (Hymen) – Idan amarya tana da budurci mai kauri, to akwai buƙatar ƙarin lokaci ko bi ta sassaukar hanya domin a warware, ba tareda radadi mai yawa ba.
Yin Gaggawa – Idan angon bai bi hankali ba yayin shigar mace, hakan yana iya haddasa azabar daren farko.
Matsalolin Lafiya – Wasu amaren na fama da matsaloli kamar vaginismus (tsokar gaba na rufe sosai) ko rashin lafiyar mahaifa, wanda sukan iya sanyawa amarya azabar daren farko ko rashin jindaɗin saduwar ma gaba ɗaya.
Yadda Ake Rage Azabar Daren Farko
1. Kwanciyar Hankali da Natsuwa
Kada ki kasance a daren farkonki da tsoro ko fargabar saduwa da ango.
Ki tabbatar da cewa kin samu isasshen hutu kafin daren.
Yin numfashi a hankali lokacin saduwa yana taimakawa wajen rage azabar daren farko ta ciwo.
2. Yin Wasa da Shiryawa
Yin wasa tsakanin ma’aurata kafin saduwa yana taimakawa jiki da motsa sha'awa sosai, yadda jiki zai amsa abinda ake bukata.
Domin hakan yana sa gaba ya yi laushi kuma ya fitar da isasshen ruwan ni'ima (lubrication).
Ana iya amfani da natural lubricants kamar man kwakwa ko man shafawa don rage bushewar gaba.
3. Kada ayi Gaggawa yayin saduwa
Ba tilas bane ace an kammala komai a ranar daren farko ba.
Idan anga akwai wahalar jin Azabar Daren Farko, yana da kyau a jinkirta har sai mace ta shirya.
4. Salon Kwanciya Masu Sauƙi
Kwanciya a gefen juna ko amarya ta kasance a sama na iya rage jin ciwo.
Yana da kyau a nemi waje mai laushi yayin saduwa domin samun sauƙi da gujewa radadi.
5. Amfani da Magunguna Idan Bukata Ta Taso
Idan amarya tana jin tsananin ciwo, za ta iya shan ƙwayar ibuprofen kafin saduwa domin rage radadi.
Idan matsalar tayi tsanani, yana da kyau a nemi shawarar likita.
Shin Dole Ne Zubar da Jini a Daren Farko?
Akwai kuskuren fahimta da yayi ƙamari a tsakanin al’umma da dama, cewa wai dole sai mace ta zubar da jini a daren farko. A gaskiya, ba haka ba ne!
Dalilin da wasu matan basa zubar da jini sun haɗa da:
Budurcinsu ya yi laushi tun kafin aure sakamakon wasanni ko yawan motsa jiki.
Siffar budurci daban-daban ce – Wasu mata ba su da budurci mai rufe gaba gaba ɗaya wasu kuma suna da.
Idan anyi a hankali lokacin saduwa, yana iya kasancewa ba za'a zubar da jini ba.
Saboda haka, ba dole bane a zubar da jini ba a daren farko, kuma hakan ba yana nufin cewa amarya ba budurwa bace. Saboda haka a kula sosai.......
Idan Azabar Daren Farko Ta Yi Yawa, Me Ya Kamata a Yi?
Idan Azabar Daren Farko tayi yawa fiye da kima ko kuma mace na jin ciwo sosy ko yawan zubar jini, yana da kyau a dakata kuma a nemi likita bada jinkiri ba.
Idan mace tana fama da matsalolin infections wato sanyi ko fibroid, yana da kyau ayi gwaji a asibiti tun kafin aure.
Kammalawa
Azabar Daren farko ba dole ba ce. Idan an bi a hankali da nutsuwa, za'a samu jin daɗi da farinciki. Amma abu mafi muhimmanci shine:
* Ki yi shiri tun kafin aure – Karanta ko ki nemi shawara, kan yadda jiki ke aiki.
* Kwantar da hankalinki – Kada ki ji tsoro ko damuwa.
* Ku kasance cikin nishaɗi da juna – Kada ku yi gaggawar somawa, hakan zai sanya ku ji daɗin juna.
* Ango kabi a hankali – Kada kayi gaggawa ko amfani da ƙarfi.
* A nemi likita idan matsala ta taso ko kuma Idan azabar daren farko tayi yawa, ko idan saduwa ta gagara, a nemi shawara daga kwararru da masana.
Idan an bi waɗannan shawarwari namu da muka bayar a sama, to tabbas za'a iya kaucewa azabar daren farko kuma ma’aurata zasu more farin ciki a sabuwar rayuwar aurensu.