Alamun Ciki a Watan Farko: Abubuwan da Amare Zasu Iya Fuskanta a Watan Farko Na Aure
Ciki ko juna biyu wata kyauta ce daga Allah, kuma mata da dama kan iya fara jin sauye-sauye a jikinsu tun daga makon farko na daukar ciki. Duk da cewa kowace mace tana da bambanci wajen jin alamun ciki, amma akwai wasu manyan alamun ciki a watan farko da yawancin mata ka iya fuskanta.
A cikin wannan rubutu namu, za mu yi bayani kan alamun ciki a watan farko, dalilan da ke haddasa su, da yadda zaki kula da lafiyarki yayin wannan jin waɗannan alamu na farkon daukar ciki.
Menene Alamun Ciki a Watan Farko?
A watan farko na ciki, jikin mace yana fara daidaituwa ne domin daukar jariri da kuma kula dashi. Hormones kamar hCG (human chorionic gonadotropin), progesterone, da estrogen suna ƙaruwa jikin mace, wanda ke haddasa mata wasu canje-canje a jiki. Kuma Waɗannan sune manyan alamun da mata ke fuskanta a watan farko:
1. Jinkirin Al’ada (Menstrual Delay)
Wannan shine mafi shahara a alamomin ciki.
Idan mace tana da cikakkiyar tsarin al’ada kuma ta ga ba ta yi ba har lokaci ya wuce, to fa yana iya yiwuwa kina da juna biyu.
2. Canje-canjen Mama
Nononki na iya yin nauyi, kumburi, ko yin zafi.
Ana iya ganin jijiyoyinsa sun bayyana fiye da yadda suke a da.
Areolar (wajen da ke zagaye da kan nono) na iya yin duhu, idan kuma naki yanada duhu zaki ga ya ƙara baki sosai.
3. Gajiya da Kasala
Mata da yawa yayinda suka samu ciki a watan farko na jin gajiya fiye da yadda suka saba, ko da kuwa basu yi aiki mai yawa ba.
Hormone mai suna progesterone yana da hannu wajen sanya mace jin gajiya.
4. Tashin Zuciya da Amai
Yawanci yawan tashin zuciya ko yin amai suna farawa ne daga mako na 4 zuwa na 6.
Wasu matan na jin amai da safe, rana, wasu kuma sai da daddare.
Wasu kuma basa jin wannan alamar ko kadan.
5. Canji a Sha'awar Cin Abinci ko Abin Sha
Wasu masu cikin suna daina jin dadin cin abinci, ko kuma mace ta fara jin tana son wasu abinci da bata saba ci ba.
Wasu matan ma na jin suna son wari, ko zarnin fitsari, wasu kuma yawan son ƙamshi.
6. Yawan Jin Fitsari
Na ɗaya daga cikin alamun ciki a watan farko, yawan fitsari akai-akai, musamman da daddare. Hakan yana faruwa ne saboda ƙarin jini a jiki da kuma matsewar da mahaifar uwa ke yi akan mafitsara.
7. Canjin Halaye da Jin Zafi a Ciki
Hormones na iya haddasawa mai ciki canjin halaye da saurin fushi, sai kaga matarka tana ta masifa ka rasa menene dalili, ko kuma abu kaɗan ta dinga neman yin kuka. Wannan ma na daga cikin alamun ciki a watan farko.
Jin zafi wasu lokuta ya danganta da jikinki ne domin wasu masu cikin basa ji wasu kuma suna yawan ji, zae fi a nemi shawarar masana.
8. Yawan Taruwar Yawu a Baki
Wannan ma yana ɗaya daga cikin fitattun alamun ciki a watan farko, domin kaso 80% na mata yawu yana taruwa a bakinsu lokacin da suka samu juna biyu, amma yana raguwa bayan wani lokaci.
9. Sauyin Jiki da Fuska
Lokacin da kika samu juna biyu fatar jikinki na iya zama ta ƙara haske (pregnancy glow), ko kuma mace ta fara samun ƙuraje a fuska a jiki.
10. Ciwon Kai da Jiri
Sakamakon canje-canjen abubuwa da yawa a jiki, motsin jini yana iya raguwa, wanda ke saka mai ciki ta rika jin jiri.
Hanyoyin Tabbatar da Ciki a Watan Farko
(1). Gwajin Ciki a Gida (Home Pregnancy Test) – Ana iya amfani da pregnancy test strip domin duba ciki da fitsari. Ana samun sahihan sakamako daga mako na 4 zuwa na 6 bayan jinkirin al'ada.
(2). Gwajin Jini a Asibiti (Blood Test) – Gwajin hCG na jini yana bada tabbaci tun daga mako na biyu ma.
(3). Yin Amfani da Ultrasound – Idan ciki ya kai mako 5-6, likita na iya ganin alamar jariri a cikin mahaifar uwa.
Abubuwan da Mai Ciki ke Bukata a Watan Farko
(1). Da bukatar ki dinga shan ruwa da yawa don hana bushewar jiki.
(2). Ki dage wajen cin abinci mai lafiya kamar kayan lambu, ‘ya’yan itatuwa, da abinci mai yawan iron da folic acid.
(3). Ki rage shan shayi da coffee saboda tasirin caffeine na iya shafar jariri.
(4). Ki Gujewa amfani da magunguna ba tare da shawarar likita ba.
(5). Ki dinga hutawa akai akai domin gujewa gajiya da matsalolin jiki.
Ayi Gaggawar Neman Likita Idan:
(#). Ki na jin zafi mai tsanani a cikinki.
(#). Kina zubar da jini mai yawa.
(#). Kina matsanancin amai.
(#). Kina yawan ciwon kai mai tsanani.
A Karshe
Alamun ciki a watan farko na iya bambanta daga mace zuwa mace, amma mafi shahara sune jinkirin al'ada, gajiya, ciwon nono, da amai.
Idan kina fuskantar waɗannan alamun, yana da kyau ayi gwajin ciki domin tabbatar da halin da kike ciki. Har ila yau, kula da lafiyarki da samun kulawa daga likita zai taimaka wajen samun lafiyayyen jariri.