Menene Fa'idar Shan Nonon Amarya A Daren Farko:
Daren farko na aure ya kasance wani lokaci ne mai muhimmanci ga kowane sababbin ma’aurata, saboda anan ake kulla kyakkyawar dangantaka da kuma fara rayuwar aure ta soyayya da fahimtar juna. Daga cikin abubuwan da ma’aurata suke tattaunawa ko ma suke aikatawa a ranar farko shine shan nonon amarya a daren farko. Wannan yana ɗaya daga cikin al’amuran da ke janyo tambayoyi daga ma'aurata da dama, domin kuwa akwai fahimta daban-daban a tsakanin mutane kan batun na shan nonon amarya a daren farko.
A cikin wannan rubutu nawa ni sarkin soyayya na wannan gida na Aminiya, na binciko bayanai masu kyau kan batun shan nonon amarya a daren farko, dalilan da yasa angwaye ke son yin hakan, ra’ayoyin mutane, da yadda za'a kula da wannan lamari cikin ladabi da girmamawa domin shan nonon amarya a daren farko ga ango ba haramun bane.
Menene Ma'anar Shan Nonon Amarya?
Shan nonon amarya a daren farko wani nau’i ne na soyayya da ma’aurata ke yi a ranar daren farko ko kuma a lokacin da suke cikin shaukin soyayya. Hakan yana iya kasancewa wani bangare na ƙara jindaɗi tsakanin ango da amarya a yayin sha’anin jima’i, inda angwaye da dama suka ɗauki hakan a matsayin hanya ta nuna soyayya da kuma ƙarawa amarya ni'ima lokacin saduwa.
Ko da yake, ba kowane ango bane ke yin shan nonon amarya a daren farko, sakamakon hakan yana da alaƙa da al’ada, ra’ayi, ko fahimtar mutum.
Dalilan Shan Nonon Amarya A Daren Farko:
Nuna Soyayya Mai Zurfi
Ma’aurata musamman angwaye suna ganin shan nonon amarya a daren farko wata hanya ce ta kara kusanci da juna da kuma nuna cikakkiyar soyayya ga amaryarsu, domin kuwa mata suna son ayi musu hakan.
Fahimtar Juna
Shan nonon amarya a daren farko na iya zama wata sahihiyar hanya ta ƙara fahimtar juna da kuma koyon yadda za'a farantawa abokiyar rayuwa rai.
Kara Shaƙuwa A Tsakanin Ma’aurata
Babu ko tantama shan nonon amarya yana matukar taimakawa wajen ƙara kusanci tsakanin amarya da ango da kuma kawar da tsoro da kunya a tsakanin ma’aurata.
Sabon Abu
Aure sabon babi ne a rayuwar ma’aurata musamman amarya da ango, kuma mutane da dama daga cikin magabata suna ganin shan nonon amarya a daren farko wani sabon abu ne da zai ƙarawa dangantakar sabon aure armashi.
Ra’ayoyin Jama'a Da Addini Dangane Da Shan Nonon Amarya:
A Addinin Islama
Addinin musulunci ya yarda da duk wata hanya mai tsafta wacce miji zai iya jiyar da matarsa dadi ta fuskar zamantakewa da sha'anin jima'i, matsawar ba'a yiwa Allah shisshigi ba babu laifi a duk wata hanya ta ƙarawa juna jindaɗi da annashuwa a rayuwar aure tun daga daren farko. Shan nonon amarya a daren farko kuwa yana daga cikin hanyoyin ƙarawa juna jindaɗi wanda kuma ba haramun bane.
Gamsuwa
Ma’aurata suna ganin cewa shan nonon amarya na kara musu jin daɗi da gamsuwa sosai a lokacin kusanci da juna, hakan kuwa yafi daɗi musamman idan an fahimci juna kuma babu matsin lamba.
Kunya Ko Ƙin Yarda
A al’adun malam bahaushe akwai kunya da kawaici, wato amarya na iya jin kunya ko kuma rashin amincewa da wannan lamari na shan nono, musamman idan bata saba ba.
Al’ada
Shin kun san cewa a wasu al’ummomi, hakan haramun ne wato basu yarda da shan nonon amarya a daren farko ba, wasu kuma bama wani batun shan nono a al'adarsu wannan abu kuma yana da alaƙa da tarihinsu ko fahimtar rayuwar aure irin nasu.
Abubuwan Da Ya Kamata Ayi Kafin Shan Nonon Amarya A Daren Farko:
Fahimtar Juna
Yana da matukar muhimmanci ka tabbatar da cewa ka fahimci matarka amarya kafin shan nonon amarya a daren farko. Kada ka tilasta mata ko yin wani abu da bata yarda da shi ba koda yaushe ka zamto sarkin hakuri da son abinda amarya take so a daren farko.
Tsabta Da Lafiya
Tsabta tana da muhimmanci sosai kafin shan nonon amarya a daren farko domin gujewa duk wata cuta da rashin tsabta zai iya haifarwa. Idan akwai wani abu da ke iya kawo illa, yana da kyau a guji yinsa domin cigaban lafiyarku.
Banda Matsin Lamba
Daren farko ba lokacin da za a matsawa juna lamba bane. A maimakon haka, yana da kyau ya zama lokaci na fahimtar juna cikin natsuwa da nunawa juna tsantsan soyayya.
Hanyoyin Da Za Su Taimaka Wajen Kulawa Da Lamarin Na Shan nono:
Tattaunawa
Kafin a fara shan nonon amarya a daren farko, yana da kyau ma’aurata su yi magana kan abubuwan da suke so da waɗanda ba sa so. Wato yana muhimmanci kowa yaji ra'ayin kowa, shin kina So? shin kaima kana So?.
Yi a Hankali
Ango kabi a hankali wajen shan nonon amaryarka domin hakan zai ƙara mata jindaɗi da son abun, Ya kamata ayi abun cikin ladabi da natsuwa ba tareda sauri ko matsin lamba ba.
Nuna Girmamawa
Yana da kyau ango ka fahimci yanayin matarka a lokacin shan nonon amarya a daren farko sannan kuma ka mutunta ra’ayinta. Ita kuma ta kasance mai bayyana abinda take so da yin biyayya a gare ka. In dai akwai girmama juna a auratayya to za'a samu zaman lafiya mai ɗorewa.
Shin Shan Nonon Amarya A Daren Farko Nada Amfani?
Kwarai kuwa babu Ja a wannan batu, Shan nonon amarya a daren farko yana da muhimmanci kuma addinin musulunci ya yarda da haka. Koda yaushe yana da muhimmanci a gane cewa aure abu ne na soyayya, fahimtar juna, da kuma kulawa. Babu wani abu da ya zama dole sai dai idan duka ma’aurata sun yarda da yin hakan. Shan nonon amarya a daren farko abu ne da yake da alaƙa da ra'ayi, kuma babu dalilin yin hakan idan daya daga cikin ma’aurata baya so.
Angwaye Ku Sani Cewa:
Shan nonon amarya a daren farko wani lamari ne mai kyau kuma ya kamata ka fahimci duk wani reaction na matarka lokacin da kake yi mata, shin tana son hakan ko kuma a'a. Daga nan sai ka yanke hukuncin cigaba ko kuma dakatawa, shine dalilin da yasa tattaunawa kafin aiwatar da hakan nada tasiri. Shan nonon amarya ko mace ba'a daren farko ba kowane lokaci ma yana bukatar yardar mace, fahimtar juna, da kuma nuna soyayya cikin nutsuwa.
Aure abu ne na haɗin kai da kuma gina dangantaka mai ƙarfi, don haka, yana da muhimmanci a tabbatar da cewa duk wani abu da za a yi yana ƙara wa soyayya armashi ba tare da matsin lamba ba. Duk abin da ya shafi rayuwar aure, ya kamata ya kasance cikin soyayya, da kulawa.