Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zuciya

Kalaman soyayya masu ratsa zuciya zuwa ga masoya

Kalaman soyayya masu ratsa zuciya

Soyayya tana da girma da daraja tun tali-tali, kuma a yawancin lokuta Allah yaba soyayya dama na ikon canza rayuwar jama'a da saka zuciyarsu ta sami kwanciyar hankali. Ba kawai neman gyara zance ba, amma soyayya hanya ce ta nuna jindaɗi da kulawa da masoyi koda yaushe. Ga wasu kalaman soyayya masu ratsa zuciya wanda muka haɗosu tun daga 2023, 2024. Yanzu muna 2025 kuma muna sa ran wannan kalaman soyayya masu ratsa zuciya zasu amfaneku a duk lokacin da kuka yi amfani dasu. Wato abun nufi ko wace shekara kuka karanta wannan rubutu nawa ni sarkin soyayya na wannan gida. Kuma inshallah waɗannan kalaman soyayya masu ratsa zuciya za su yi tasiri ga zuciyar masoyinki ko masoyiyarka, sannan su tabbatar da cewa kaunarku ta ƙarfafa a cikin zukatansu.

Ayi cewa mun raba waɗannan kalaman soyayya masu ratsa zuciya zuwa kashi uku, wato akwai sashi na farko akwai sashi na biyu. Har kuma zuwa sashi na Uku.

Ga kalaman soyayya masu ratsa zuciya kamar haka:

"Ranar dana fara ganinki, na ji zuciyata ta shiga wani yanayi da ban taɓa jin irin sa ba. Wannan ƙaunar da nake ji a kan ki ba zata misaltu ba; domin kin zamto tamkar haske a cikin duhu. Ko me duniya za ta bani Ni ban damu ba, zan tsaya tareda ke domin ni ke nake so, kuma ba zan taɓa barin ki ba."

"Ke ce tambarin farin cikina. Lokacin da nake tareda ke, gaba ɗaya ilahirin jikina yana yin shiru ne domin sauraron muryarki kawai. Kowace rana tareda ke a cikin rayuwata wata albarka ce. Ba zan taɓa daina ƙaunarki ba, domin kece ƙaddarar zuciyata."

"A duba min wannan ma domin ya cancanta a jerin kalaman soyayya masu ratsa zuciya. "Idan na duba idanunki, ina ganin ƙauna mai zurfi da ke haskaka zuciyata. Wannan ƙaunar tana ƙara min ƙarfin gwiwa a kowace rana. Ina fatan zan kasance tareda ke har abada, domin babu wani abu a duniya da zai maye gurbin soyayyarki."

"A duk lokacin da nayi tunani a kan ki, zuciyata tana jin tamkar naci nasarar duk duniya. Lokacin da nake cikin damuwa, ganin ki kawai yana faranta min rai. Kece tauraruwar da take jagorantar rayuwata. Ba zan taɓa iya daina son ki ba."

"Soyayyarki tana ratsa kowane sashe na jikina. Ba zan iya tuna lokacin da zuciyata ta daina bugawa saboda ke ba. Zuciyata tana yi miki alƙawarin kasancewa tareda ke, a lokacin farin ciki da kuma a lokacin baƙin ciki. Ina sonki ba tareda sharaɗi ba."

"Ke ce mace ƙwaya ɗaya tilo da ta canza rayuwata ta kowace hanya mai kyau. Ina ji tamkar duniya ba za ta taɓa isa ta bayyana yadda nake ji a gare ki ba. Soyayyarki tana min tamkar ruwa mai tsarkakewa da kuma iska mai bayar da numfashi mai kyau."

"Idan akwai wani abu da zan iya yi domin nuna irin yadda nake son ki, to da zan ciyar da duk rayuwata wajen yin hakan. Kece a rubutun rayuwata; ke ce labarina. Rayuwa bata da ma'ana ba tareda ke ba."

Wannan shine sashi na biyu kalaman soyayya masu ratsa zuciya domin masoya:

"Soyayyarki ta kasance tamkar waka ce dake ratsa zuciyata. Ɓata kowace rana tareda ke abun so ne, sannan buɗe kowace rana tareda ke tamkar sabon shafi ne a cikin rayuwata. Ina so mu zauna tare da murna har ƙarshen rayuwarmu."

"Lokacin da nake cikin haɗari, tunanin ki ne yake ba ni kwarin gwiwa. Ke ce sirrin nasarata da farin cikina. Rayuwa ba zata taɓa zama cikakkiyar ba idan ba tareda ke a cikinta."

"Ranar da bana tareda ke, yana kasance min tamkar rana ce ba tare da haske ba. A cikin muryar ki, na kanji nutsuwa; a cikin dariyarki, na kan ga haske. Ke ce mafi darajar abin da na taɓa samu a rayuwata." Wannan ma ko ban faɗa ba ya cancanta a jerin kalaman soyayya masu ratsa zuciya.

"Duk yayinda na rungumeki, na kanji tamkar duniya bata da wata_matsala. Hasken soyayyarki yana canza yanayin zuciyata daga damuwa zuwa farinciki. Babu wanda zai iya canza yadda nake ji a gare ki."

"Soyayyarki ta zama tamkar hasken fitila mai jagoranci a cikin duhu. Duk lokacin da nake jin damuwa, tunaninki ne yake sauƙaƙa min komai. Ki sani cewa, ba zan taɓa daina ƙaunarki ba."

"Kece abin alfaharina, abin tunanina, kuma silar farin cikin rayuwata. Kece hasken da ya kawo mini dumi a cikin sanyin rayuwa. Babu abinda ya fi farinciki a gare ni kamar kasancewa tareda ke."

"Koda yaushe Zuciyata tana bugawa ne saboda ke. Rayuwa bata da ma'ana idan babu ke a cikinta. Soyayyarki tafi kowace dukiya daraja a gareni, kuma bazan taɓa daina godewa Allah saboda samun ki da nayi a rayuwa."

"Lokacin da nake tunaninki, zuciyata tana bugawa_da_sauri. Lokacin da nake kusa da ke, duniya tana cika da kwanciyar hankali. Soyayyarki tanamin tamkar numfashi, kuma bazan iya rayuwa ba tareda ke ba."

Ƙarin Kalaman soyayya masu ratsa zuciya sashi na karshe: Wannan ma dai da zafinsu.

"Duk lokacin da na ganki, zuciyata tana jin tamkar tana cikin wani sabon wuri mai cike da kwanciyar hankali da nutsuwa ne. Ina jin tamkar duniya bata isa ta bayyana yadda nake ji a gareki ba. Ina yi miki alƙawarin kasancewa tareda ke har abada, kuma a duk tsawon rayuwata."

"Idan aka tambayeni meyasa nake ƙaunarki, bazan iya kawo dalili ɗaya ba, domin soyayyarki tana da yawa kamar taurari a sararin samaniya. Kowace rana tareda ke tamkar wata albarka ce da ba zan taɓa mantawa da ita ba."

"Kece silar farinciki da karfina. Lokacin dana dubi idanunki, ina ganin duniya mai cike da bege da soyayya mai kyau. Ke ce mai gina ginin rayuwata, kuma na tabbata ba zan taɓa samun wata tamkar ki ba." Wannan gaskiya ya cancanta a jerin kalaman soyayya masu ratsa zuciya.

"Soyayyarki tana bayyana a cikin duk abinda nake yi. Lokacin da nayi dariya, ke ce silar wannan dariyar. Lokacin da zuciyata take jin nutsuwa, kece hasken da ya kawo wannan nutsuwar. Nayi godiya da samunki a rayuwata."

"Ko ma me wannan duniya za ta kawo, babu wani abu da zai sa na daina ƙaunarki. Ina jin tamkar na same ki ne daga cikin mafarkina, kuma yanzu na tabbata cewa kece mafarkin da nake jira a tsawon rayuwata."

Karshen Zance:

Kalaman soyayya masu ratsa zuciya suna da tasiri sosai wajen janyo hankalin saurayi ko budurwa. Daga cikin kalaman dana lissafa a sama ka ɗauki duk wanda yayi ma sai ki canja zuwa yanda kike so zuwa ga sahibinki. Ayi cewa soyayya tafi kyau idan aka bata lokaci da kulawa. Waɗannan kalamaan soyayya masu ratsa zuciya suna da ƙarfi wajen bayyana abin dake cikin zuciyar masoyi. Kada ku taɓa mantawa cewa soyayya tana buƙatar zurfin fahimtar masoyi da kuma juriya.
Previous Post Next Post