Girman Nonon Budurwa

Girman Nonon Budurwa:


Girman nonon budurwa

Girman nonon budurwa wata babbar matsala ce dake damun yawancin 'yan mata, musamman matan da ke balaga ko kuma waɗanda ke shirin yin aure. Wasu suna jin damuwa idan nonuwansu basu girma ba, yayinda wasu yan'matan kuwa ke jin tsoro saboda kada nonon ya yi girma fiye da kima. Wannan sahihin blog post nawa ni malamar mata ta wannan shafi zai yi bayani mai gamsarwa kan abubuwan da suka shafi girman nonon budurwa, hanyoyin da za'a bi domin inganta girman nonon, da kuma maganganun da za'a iya amfani dasu domin magance matsalar girman nonon budurwa.

Menene Dalilan Da Suke Kawo Girman Nonon Budurwa?

Girman nonon budurwa ko mace yana da nasaba da abubuwa daban-daban wadanda suke faruwa a jiki dama yanayin mace, kamar haka:

Kwayoyin Halitta (Genetics)
Yar'uwata kiyi sani cewa idan uwa ko kakarki mace tana da manyan nono, akwai yiwuwar  kema ɗiyarta ko jikarta ta gaji girman nonon. Haka zalika kuma, idan danginki wato uwa ko kaka da sauransu suna da halittar ƙananan nonuwa, to akwai yiwuwar ita ma yarinyar tayi gadon wannan halitta. Wato dai girman nonon budurwa zai iya kasancewa Gado ne daga ahali.

Sinadarai (Hormones)
Hormones wasu sinadarai dake cikin jikin mace wanda suke sarrafa duk wata halitta ta balaga da girma tun daga haihuwarta irin su estrogen da progesterone, waɗanda suna da tasiri sosai wajen girman nonon budurwa. Wato idan har ubangiji yayi miki halittar wannan sinadarai da yawa kuma suna aiki yadda ya kamata tofa babu shakka girman nonon budurwa ze iya faruwa a jikinki. Haka zalika Idan mace tana da ƙarancin waɗannan hormones, nononta na iya zama ƙarami.

Abinci da Lafiyar Jiki
Ta'ammali da abinci mai gina jiki, musamman wanda ke da fats (kitse), proteins (Nama, kwai, kifi), da vitamins (Kayan marmari haka Lemo, ayaba), suna iya taimakawa wajen bunkasa girman nonon budurwa. Haka zalika rashin samun wadannan abubuwa na iya haifar da ƙananan nonuwa.

Yawan Kitsen Jiki
Tunda nonuwa suna da alaka da kitsen jiki, to fa akwai yiwuwar mace mai ƙiba na iya samun manyan nono fiye da siririyar mace.

Aiki da Motsa Jiki
Wasu motsa jiki kamar push-ups da bench presses na iya taimakawa wajen ƙarfafa tsokokin ƙirji, wanda hakan zai sa nono ya yi kyau da ɗaukar girma.

Hanyoyin Da Zaki Bi Domin Girman Nono Cikin Sauƙi:

Idan kina so nonuwanki su girma, ga wasu hanyoyi da za ki iya gwadawa:

1. Cin Abinci Mai Gina Jiki

Gyada, Avocado, Madara, Nama, Kifi, da Kwai suna taimakawa matuƙa wajen ƙara girman nonon budurwa.

Kayan marmari wato Fruits kamar Tuffa, Gwanda, da Ayaba suna taimakawa wajen daidaita sinadaran hormones.

2. Yin Wasanni (Exercise)


Ki dinga yin Push-ups – Domin na taimakawa wajen ƙarfafa tsokokin ƙirji.

Chest Press – Yana inganta tsayi da girman nonon budurwa.

Butterfly Press – shima yin wannan exercise yana ƙara ƙarfafa ƙirjin mace.

3. Amfani da Man Shafawa Na Tausa (Massage)

Zaki iya amfani da man kwakwa ko man zaitun domin suna taimakawa wajen daidaita fatar nono da kuma sa su yi girma.

Wato sai ki dinga shafa man tareda danna nonuwanki mulmula nonuwan in circular motion na kamar mintuna 10 a kowacce rana.

4. Yawan Shan Ruwa

Ruwa yana taimakawa wajen hana fatar nono ta ƙuƙunce wato yayi kamar na wata tsohuwa, ki dinga shan ruwa akai-akai domin yana sanya girman nonon budurwa da kuma sanya fatar nonon tayi luwai-luwai.

5. Gujewa Sanya Rigar Nono Matsattsiya

Sanya Rigar Nono wato Bra wacce take matse nono na iya hana girman nonon budurwa cikin sauƙi. Saboda haka ina bada shawarar ki dinga sanya bra wadda bata matsewa domin zata tallafawa nonuwanki suyi dai-dai.

Tambayoyin da Ake Yawan Yi Game da Girman Nonon Budurwa:

1. Shin da gaske akwai magungunan da ke ƙara girman nonon budurwa?
Babu ko shakka, akwai wasu magunguna da ke ƙara girman nonon budurwa, amma fa ayi sani cewa mafi yawansu na iya yin illa ga lafiyar mace, musamman idan kina yawan amfani dasu. Amma zaki iya amfani dasu bisa shawarar likita ko masana.

2. Shin girman nono yana tasiri a sha'awar maza?
Sosai ma kuwa, ai gaskiya girman nonon budurwa ko mace yana da tasiri wajen tayar da sha'awar maza, duk cewa kowanne ɗa namiji yana da abinda yafi so a jikin mace.

3. Idan nono bai girma ba, yana nufin ba za'a iya shayar da jariri ba?
Girman nono bashi da tasiri wajen shayar da jariri. Ko nonuwanki sun girma ko basu girma matsawar kina da ruwan nono to zaki iya shayar da jinjirinki. Domin rashin girma baya nufin babu ruwa.

Laifin Daɗi 

Girman nonon budurwa yana da alaƙa da abubuwa da dama kamar kwayoyin halittar jikin mace, sinadaran hormones, da kuma abinci mai gina jiki. Amma duk da haka, akwai wasu hanyoyi da mace zata iya amfani dasu domin samun girman nonon, ciki har da motsa jiki, da amfani da man shafawa. Abu mafi muhimmanci shine mace ta yarda da kanta kuma tayi godiya ga yadda Allah ya halicce ta.
Previous Post Next Post