Abubuwan Da Suke Karya Azumi:
Azumi yana ɗaya daga cikin ginshikan musulunci guda biyar kamar yadda addini yazo dashi, kuma yana da matukar muhimmanci ga kowanne musulmi ya azumci watan Ramadan. Duk da haka, akwai wasu abubuwan da suke karya azumi idan aka aikata su, suna karya azumi kuma suna iya hana ubangiji ya karɓi ibadar. Sanin wadannan abubuwan da suke karya azumi yana taimakawa Musulmi domin kiyaye azuminsa da kuma tabbatar da cewa ibadarsa ta zama karbabbiya ya samu lada kamar yadda yake fata.
A cikin wannan bayani namu na yau, zamu tattauna kan abubuwan da suke karya azumi, sannan mu yi bayani kan abubuwan da basa karya azumi duk da cewa mutane da dama suna ganin suna iya karya azumin.
1. Cin Abinci da Shan Ruwa
Cin abinci ko wane iri, ko shan duk wani abun sha suna daya daga cikin sanannun abubuwan da suke karya azumi. Idan mutum musulmi ya ci abinci ko ya sha ruwa da gangan (wato da saninsa), azuminsa ya karye. Amma idan mutum ya manta ne yana azumi ya ci ko ya sha, to wannan azuminsa yana nan bai karye ba, bisa koyarwar Annabi Muhammad (SAW).
Abun Nufi:
Cin abinci ko shan wani abun sha da gangan yana karya azumi.
Cin abinci ko shan abun sha da mantuwa baya karya azumi.
2. Jima’i ko (Saduwa da Iyali)
Idan mutum yayi jima’i da matarsa, ko mata ta sadu da mijinta yayinda suke azumi, yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke karya azumi, kuma dole ne suyi kaffara (farilla ta musamman) domin neman gafara. Wannan kaffara na iya haɗawa da azumin wata biyu a jere ko kuma ciyar da miskinai.
Abun Nufi:
Saduwa da iyali da gangan yayinda ake azumi yana karya azumi.
Idan saduwa ta faru da mantuwa ko a cikin mafarki ga baligai, wannan baya karya azumi.
3. Fitar Mani da Gangan (Fitar Maniyyin Namiji)
Fitar maniyyi ta hanyar wasa da gaba da niyyar kawo gamsuwa (masturbation) ko kallon abubuwa masu tayar da sha’awa kamar blue films ko sauraron labaran banza yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke karya azumi. Amma fitar maniyyi lokacin mafarki baya karya azumi.
Misali:
Yin wasa da azzakari, ko kallon fina-finan banza masu tayar da sha’awa har yasa maniyyi ya fita babu shakka yana karya azumi.
Fitar da maniyyi lokacin bacci a mafarki kenan baya karya azumi.
4. Fitar Jini da Yawa
Fitar jini ga mai azumi da yawa kamar jini bayan fitar hakori, zubar jini daga rauni ko yin hijama (cupping) na daga abubuwan da suke karya azumi, musamman idan hakan yasa mutum ya raunana sosai. Amma fitar jini kadan baya karya azumi.
Misali:
Hijama ko fitar jini mai yawa yana karya azumi.
Fitar jini kadan daga yatsa ko karamin ciwo baya karya azumi.
5. Yin Amai da Gangan
Idan mutum da gangan ya janyo amai da kansa, to tabbas azuminsa ya karye. Amma idan amai yazo da kansa ne ba tareda mutum ya tsokano shi ba, to azumin mutum bai karye ba.
Misali:
Yin Amai da gangan yana karya azumi.
Amai idan yazo da kansa ne ba tareda niyya ba to hakan baya karya azumi.
6. Shigar Abubuwa Zuwa Ciki Ta Kowace Hanya
Shigar abinci, ruwa ko duk wani abu zuwa ciki ta baki, hanci, kunne ko dubura suna daga abubuwan da suke karya azumi. Wannan ya hada da shaƙar ko yin amfani da sinadaran kimiyya kamar su allura ko shigar da ruwa ciki ta hanyar likitanci.
Misali:
Shan magani ko ruwa ta baki ko ta hanci yana karya azumi.
Amfani da allurar da bata ciyarwa ba (misali allurar riga kafi) baya karya azumi dangane da fahimtar wasu malamai.
7. Shan Sigari Ko Shakar Abubuwa Masu Ƙamshi Sosai
Shan sigari ko shakar abubuwan da ke da kamshi mai karfi (kamar turaren wuta) na daya daga cikin abubuwan da suke karya azumi domin yana shiga cikin jiki.
Misali:
Shan sigari yana karya azumi.
Shakar kamshin turare daga nesa ba zai karya azumi ba, amma shakarsa da gangan yana iya karya azumi.
8. Fitar Hankali
Idan Musulmi ya fada cikin halin rashin hankali ko yayinda yake azumi, wannan na iya karya azuminsa. Domin azumi na bukatar mutum ya kasance cikin hankalinsa daga farawa har zuwa faduwar rana.
Abubuwan Da Basa Karya Azumi
Kurkura da Wanke Baki:
Kurkura da wanke baki lokacin yin alwala baya karya azumi, muddin ba'a hadiye ruwa ba.
Fitar Mani a Mafarki:
Idan mutum ya fitar da maniyyi yayinda yake bacci (mafarki), hakan baya karya azumi.
Allura:
Amfani da allura domin magani da ba ta ciyarwa (kamar allurar rigakafi ko allurar ciwon jiki) baya karya azumi bisa ra’ayin wasu malamai.
Amfani da Man Feshi ko Turare:
Amfani da turaren feshi a jiki ko shakar kamshi daga nesa ba tareda an niyyar shakarsa a ciki ba baya karya azumi.
Hana Kai Daga Amai:
Idan mutum ya hana kansa yin amai kuma ya fito da kansa, to baya ɗaya daga cikin abubuwan da suke karya azumi.
Abubuwan da suke karya azumi suna taimakawa kwarai da gaske wajen kiyaye wannan ibada. Dole ne Musulmai su kasance masu kula da ayyukansu domin kada su aikata abubuwan da zasu rushe ibadarsu ba tareda sani ba.
Allah ya karɓi azuminku, ya sa mu dace da rahamar watan Ramadan! .. a koda yaushe Tsamiyanovels.com.ng taku CE.