Yadda Ake Wasa da Nonon Amarya a Daren Farko:
Sanin abubuwan da ya kamata ayi a daren farko na aure ga amarya da ango yana da matukar muhimmanci, kasancewar hakan ne yasa mukai wannan rubutu na yadda ake wasa da nonon amarya a daren farko, wato domin ƙara danƙon soyayya da kauna tsakanin masoyan. Sanin yadda ake Wasa da nonon amarya a daren farko wani muhimmin abu ne da ya kamata ango ya sani, musamman idan an yi shi cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
A cigaba da karatu cikin nutsuwa domin a wannan blog post, za mu bayar da dalilin da yasa da yawa daga cikin ma'aurata ke son yin wasa da matansu na sunna, sannan kuma zamu nuna yadda ake wasa da nonon amarya a daren farko, idan ma ku ba amare bane to fa wannan rubutu zai ƙara koya muku yadda ya kamata ku dinga yiwa matanku cikin sauƙi. Domin kuwa kodayaushe yana da kyau namiji yasan hanyoyin da zai kula da matarsa don tabbatar mata da jindaɗi da gamsuwa a kowane lokaci.
Menene dalilin da yasa sanin hanyoyin da ake wasan da nonon amarya a daren farko yake da amfani?
Kuyi sani cewa wasa da nonon amarya a daren farko ba wai kawai ana yinsa bane domin jima’i ba; a'a domin ana yinsa ne da nufin ƙara alaƙa da ƙara kusanci, soyayya, da gina shaƙuwa mai ƙarfi a tsakanin ma’aurata. Ga wasu dalilan da yasa hakan ke da muhimmanci:
(1). Ƙara Jindadi da Shaƙuwa
Ko ban faɗa ba, Nonuwa suna ɗaya daga cikin wuraren da suke motsa sha’awar ya mace, kuma wasa dasu cikin salo na taimaka wa mace wajen samun kuzari da kuma jindaɗi yayin mu'amala da angonta.
(2). Rage Kunya da Fargaba
First Night a turance ya kasance lokacin da da yawa daga cikin amare ke jin tsoro da kuma kunyar angwayensu. Amma yin wasa da nonon amarya a daren farkon na iya taimakawa wajen rage yawan jin kunya da kuma fargabar amarya kai har ma da angon, abinda yasa nace hakan shine da yawa daga cikin angwaye suma suna jin kunya a darensu na farko.
(3). Ƙarawa ma’aurata kusanci
Sani da kuma ɗabbaka Shan nonon yana bawa ma’aurata damar samun kusanci da junansu ta jiki har ma tunani domin zasu ji cewa yau fa sun zama ɗaya, musamman idan anyi cikin so da kauna.
(4). Shiryawa domin yin Jima’i
Wasa da nonon amarya a daren farko na iya zama wani shiri domin soma aiwatar da sha’anin jima’i, domin yana taimaka wa amarya taji nutsuwa sannan ta shirya tsaf domin soma jindaɗi irin na kwanciyar aure.
Hanyoyin da ake bi domin wasa da nonon Amarya cikin natsuwa a darenku na farko. Ya kai ango mai girma ga abubuwan da ya kamata kayi.
1. Ka Fara Cikin Nutsuwa da Lallami
A daren farko, yana da kyau ango ka fara taɓawa gamida shan maman masoyiyarka cikin ladabi tareda nutsuwa, sannan da kwantar mata da hankalinta. Idan zai yiwu ma ka tambayeta idan tana jindaɗin abun kuma ka tabbatar bata jin tsoro. Ai wasu na iya cewa "kowace mace tana jin dadi idan ana sha mata nono, wannan ba haka bane domin shan nonon amarya ba tareda kwanciyar hankalinta ba aikin banza ne domin ba abinda zai ƙara mata ta fuskar jindaɗi"
2. Kayi a Hankali
Ango ya kamata ka fahimci cewa wasa da nonon amarya a daren farko yana buƙatar hankali da kuma natsuwa. Kada kayi garaje ko kayi abinda zai kawowa amarya rashin jin daɗi.
3. Amfani da Hannunka cikin salo da nutsuwa
Yin amfani da hannuwa cikin salo zai taimaka wajen bawa amarya jin daɗi. Wato kana mulmulawa da matsawa a hankali yadda zata ji ni'ima sosai. Kada ka matsa mata nonuwa da ƙarfi sai kace ka samu biredi, domin hakan zai kawo rashin jindaɗi har ma bata mata rai.
4. Amfani da Baki
Ango yana da kyau kayi amfani da baki wajen wasa da nonon amaryarka a daren farko, wato kamar taɓa su da harshe sannan kana tsotsa. Wannan yana matukar kara danƙon soyayya da son kasancewa da kai a kodayaushe.
5. Ka kula da ita sosai
Malam ango ka kula da yadda amarya take amsawa yayinda kake wasa da nononta. Idan kaga ta nuna damuwa, to zai fi kyau ka dakata sannan ka tambayeta abinda ya kamata ka yi mata.
Abubuwan da ya kamata a gujewa yayin tarayya da amarya a daren farko.
Kada kayi mata tilas
Wasa da nonon amarya a daren farko wani lamari ne da ya kasance duka ma’aurata suka amince dashi. Tilasta mace ko amarya yin abinda bata so zai iya kawo matsala a dangantakarku. "Abun dariya ko, duk da nasan cewa yarinyar da take sonta ba zata hana ka ba, amma dai ba tilastawa duk da haka"
A guji matsawa da ƙarfi
Matsawa ko taɓa nonon amarya da ƙarfi zai iya janyo ciwo ko rashin jindaɗi. Sabida haka ka tabbata kayi abun cikin tausasawa da nutsuwa.
Ka guji cizon nonon amarya
Idan matarka amarya take to fa ka guji cizar mata nonuwa ko wani yanayi da zai iya kawo mata rashin jin daɗi, ba wai kar ka cizi nono ba a'a kar kayi da mugunta, yana da kyau a guji wasan da zai haifar da ɗa mara ido.
Rashin Natsuwa
Ka tabbata ka kula da yanayin uwar yayanka. Idan ka fuskanci tana nuna damuwa ko rashin jin daɗi, ka tsaya sannan ku tattauna.
Amfanin Wasa da nonon amarya a daren amarci
Ƙara Soyayya da Kusanci
Wannan yana taimaka wa ma’aurata wajen ƙulla kyakkyawar soyayya da fahimtar juna.
Ƙara Jindaɗi a yayin Jima’i
Wasa da nono ya kan taimaka ƙwarai da gaske wajen motsa sha'awa da kuma sanya mace cikin yanayin da zata ji daɗin jima’i.
Kwanciyar Hankali
Lokacin da aka gudanar da wasan shan nonon amarya a daren farko cikin ladabi, yana taimakawa mace ta samu kwanciyar hankali a daren farkonta domin zata daina jin nauyi da kuma kunyar mijinta.
Ga wasu shawarwari domin Ma’aurata
Zan iya cewa yana da kyau kayi magana da matarka kafin ka soma wani abu. Saboda haka zai taimaka wajen samun amincewa da fahimtar juna.
Ka kasance mai kula da lafiyarta da jin daɗinta a duk lokacin da kake wasa da ita.
Kada ka yi abu domin kaji daɗi kawai; ka tabbatar cewa itama tana jindaɗin abinda kake yi.
Ka kasance mai tausayawa amarya kuma ka nuna mata ƙauna a duk lokacin da kake sha mata mama ko saduwa da ita.
Wasa da nonon amarya a daren farko wani bangare ne na soyayya da kuma nuna shaƙuwa tsakanin ma’aurata. Amma duk da haka, yana da muhimmanci ka tabbatar da cewa kayi komai cikin fahimtar juna da tausayi.
Kuyi sani cewa daren farko ba wai lokaci ne na matsawa juna lamba ba, musamman ta fuskar jima'i wato lokaci ne na gina kyakkyawar dangantaka da amaryarka mai cike da soyayya, fahimta, da natsuwa. Idan ka kula da hakan, zai taimaka wajen tabbatar da rayuwar aurenku ta fara cikin jindaɗi da farin ciki da junanku.