Sirrin Tabbat Yada Don Mallaka

Sirrin Tabbat Yada Don Mallaka: Abinda Ya Kamata Ku Sani

Sirrin Tabbat Yada Don Mallaka

A cikin al’adun rayuwa da addini, mutane da yawa suna neman hanyoyin da zasu iya samun soyayya, tarairaya, ko kuma mallakar zuciyar wani mutum. Duk da haka, yana da muhimmanci a fahimci cewa komai da mutum yake yi, dole ne ya kasance a cikin tsarin da ya dace da tsoron Allah da sanin alhakin rayuwa. Wannan rubutu nawa na yau zai yi bayani akan sirrin tabbat yada don mallaka, tareda jaddada muhimmancin tsoron Allah da kuma amfani da hikima wajen amfani da irin wannan ilimin.

تَبَّتْ يَدَا أَبِي لَهَبٍ وَتَبَّ

مَا أَغْنَىٰ عَنْهُ مَالُهُ وَمَا كَسَبَ

سَيَصْلَىٰ نَارًا ذَاتَ لَهَبٍ

وَٱمْرَأَتُهُۥ حَمَّالَةَ ٱلْحَطَبِ

فِى جِيدِهَا حَبْلٌۭ مِّن مَّسَدٍۭ


Sirrin Mallakar Zuciyar Mutum

Wannan sirri yana magana ne akan mallakar zuciyar wani, mace ko namiji, domin ya zama mai tsananin son ka ko kuma son ki. Duk da haka, yana da kyau ayi amfani da wannan hanya bisa kyakkyawan dalili kuma cikin tsoron Allah. Ga yadda ake gudanar da wannan sirrin:

Abubuwan da ake Bukata:

(1). Tsakuwa guda 41.

(2). Karanta “Tabbat Yada” kafa 7 a kan kowace tsakuwa har sai an gama duk tsakuwowin.

(3). Bayan haka, sai a kona tsakuwowin a wuri kamar murhu ko tukuba.

Ka’idar Yin Amfani Da Wannan Sirri:
Wannan sirri na bukatar ayi shine kawai domin halastacciyar soyayya ko kuma domin kyautata alaka. Duk wani amfani da bashi da dalili mai kyau na iya jawo matsala ko kuma cutarwa ga wanda aka yi dominsa. A kiyaye.

Sirrin Kama Barawo ko Maƙiyi

A wani lokaci, ana iya fuskantar matsalar sata ko kuma ɓatan kaya. Wannan sirrin zai taimaka sosai wajen gano barawo cikin kankanin lokaci.

Abubuwan Da Ake Bukata:

Allon ƙarfe.

Barkono guda 6.

Kitsen zaki.

Yadda Ake Yin Sirrin:

(1). A rubuta Assariqu (barawo) a tsakiyar allon.

(2). A shafa kitsen zaki a allon da kuma barkono.

(3). A kona allon a wuta yayinda ake karanta “Tabbatyada” kafa 1,000.

Ayi Sani Cewa: Idan barawon ya bayyana amma ba'a son ya mutu, to dole ne a cire allon daga wuta sannan a shafe shi da ruwan sanyi.

Sirrin Tarwatsa Maƙiya

A rayuwa, ba dukkan mutane ne suke son ganin ci gabanka ba. Wannan sirri yana amfani domin kawar da mugun nufi daga maƙiya.

Abubuwan da Ake Bukata:

(*). Aduwa guda 21.

Yadda Ake Haɗawa:

Kullum za'a yi amfani da Aduwa guda 7, tareda yin alwala da addu’a kafin amfani dasu.

Bayan sallar magriba, a tara ƙwallayen Aduwar da aka yi amfani dasu sannan a tofa “Tabbatyada” kafa 1 akan kowanne kafin a ƙona su.

Yi da Yaƙini da Tawakkali:

Ya kamata a kasance da tsoron Allah kuma a bar komai ga ikon sa. Idan mutum ya nemi taimakon Allah da zuciya mai gaskiya kuma idan mutum ya dogara ga Allah to ubangiji ba zai bawa maƙiya iko a kansa ba.

Muhimman Gargadi

Tsoron Allah: Duk wanda yake amfani da irin wannan sirri ya kamata ya tabbatar da cewa yana yin haka ne kawai bisa dalili mai karfi da adalci. Duk wani abu dake da nufin cutarwa ko ha’inci na iya jawo bala’i.

Sadaƙa: Ana bada shawara cewa duk wanda zai yi amfani da irin wannan sirri ya bayar da sadaƙa domin neman albarka daga Allah.

Daga Karshe 

Sirrin tabbat yada don mallaka, kama barawo, da tarwatsa maƙiya, duk suna da amfani ne idan aka yi su tareda niyyar alheri da kuma neman yardar Allah. Amma fa, babu wani abu da yafi dogaro da Allah da kuma yin addu’a a cikin dukkan lamarin rayuwa. Duk yadda muke son magance matsalolinmu, ya kamata mu kasance masu tawakkali da hakuri.

Idan kuna da wata tambaya ko karin bayani, sai a tuntuɓi mai bayar da shawara na wannan shafi na tsamiya novels. Allah ya bamu dukkanmu kariya da masoya na gari. Ameen.

Lura: Wannan rubutu yana da manufar ilmantarwa ne kawai. Duk wani amfani da zai iya cutarwa ko sabawa doka, tofa alhakin yana kan wanda ya aikata.
Previous Post Next Post