Rundunar Tsaro Ta Katsina Ta Kashe Ƴan Bindiga 18 a Samame


Rundunar Tsaro Ta Katsina Ta Kashe Ƴan Bindiga 18 a Samame

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da nasarar kashe ƴan bindiga 18 a wani samame da rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro ta kai a ƙaramar hukumar Dutsinma. Wannan samame ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan ayyukan ƴan bindigar, wanda ya ba da damar kai farmaki da kawo tsaiko ga ayyukansu.



Nasarar Jami’an Tsaro

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dr. Nasiru Muazu, ya bayyana cewa, yayin wannan aikin, an kwato wasu shanu da sauran dabbobi da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su. Bugu da ƙari, jami’an tsaro sun samu bindigar AK-47 guda ɗaya da harsasai 11.


Dr. Nasiru ya ce, "An samu gagarumar nasara a wannan samamen, kuma wannan mataki zai ci gaba da rage matsalar tsaro a wasu yankunan jihar." Ya kuma bayyana cewa ana samun raguwar hare-hare a wasu ƙananan hukumomi idan aka kwatanta da shekarun baya.



A cikin wata tattaunawa da Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, ya yi da manema labarai, ya bayyana cewa dabarun tsaro da gwamnati ta fito da su sun fara yin tasiri. Gwamnan ya yaba da yadda wasu mazauna jihar suka tashi tsaye don kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga.


Ya ce, "Ba wai muna kira ga al’umma su ɗauki makami ba ne, sai dai mu na goyon bayan su haɗa kai domin kare kansu. Wannan ya zama wajibi saboda jami’an tsaro da muke da su ba za su iya kare kowa ba saboda ƙarancin su."



Gwamnatin jihar ta kuma bayyana nasarar kama mutane da dama masu bayar da bayanai ga ƴan bindiga. Wannan aiki, a cewar gwamna, yana daga cikin matakan kawar da masu tallafa wa masu aikata laifuka a jihar.


Gwamna Dikko ya ce, "Mun kama wasu mutane da bincike ya tabbatar suna bayar da bayanai ga ƴan bindiga, kuma hakan ya taimaka wajen gano sirrin ayyukan su." Wannan mataki, in ji gwamnan, ya taimaka wajen rage karfin ƴan bindigar da kuma dakile hare-harensu.


Matsalar Tsaro a Yankin Arewa Maso Yamma

Duk da irin nasarorin da jami’an tsaro ke samu, matsalar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya ta ci gaba da zama babban kalubale. Ƴan bindiga na kai hare-hare a ƙauyuka da dama, suna sace mutane da dabbobi, yayin da mazauna yankunan ke fama da tsoro da rashin kwanciyar hankali.


Duk da haka, gwamnati ta yi alkawarin ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali ga al’ummar jihar.



Samamen da ya kai ga kashe ƴan bindiga 18 da kwato dabbobi a ƙaramar hukumar Dutsinma ya nuna jajircewar jami’an tsaro wajen yakar ayyukan rashin tsaro a Katsina. Sai dai har yanzu akwai bukatar ci gaba da haɗin kai tsakanin gwamnati, jami’an tsaro, da al’umma domin kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.

Previous Post Next Post