NCC Ta Amince da Karin Kuɗin Kiran Waya


Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da buƙatar kamfanonin sadarwa na ƙara kuɗin kiran waya, bayan tattaunawa da ƙarin bincike kan tasirin hakan a kasuwancin.


A cikin sanarwa da aka fitar ranar Litinin, kakakin hukumar, Reuben Mouka, ya bayyana cewa wannan ƙarin an amince da shi bisa doka, musamman sashe na 108 na Dokar Sadarwar Najeriya ta 2003 (NCA), wanda ke ba da damar daidaita farashin da kamfanonin sadarwa ke caji.


Sanarwar ta bayyana cewa kamfanonin sadarwa sun gabatar da wannan buƙatar ne saboda canje-canjen da aka samu a kasuwar sadarwa. Duk da haka, NCC ta bayyana cewa ƙarin kuɗin ba zai wuce kashi 50 cikin 100 ba, wanda ya yi ƙasa da ƙudurin kamfanonin sadarwa na ƙara kuɗin har zuwa kashi 100 cikin ɗari.


Wannan ƙarin ya zo ne saboda canje-canjen da aka samu wajen gudanar da ayyuka da kuma kula da ƙimar kasuwancin,” in ji sanarwar.


Hukumar ta bayyana cewa wannan ƙarin farashi na farko tun daga shekarar 2013, kuma an yanke wannan shawarar ne domin ƙara daidaita tsakanin tsadar gudanarwa da kuma farashin da ake cajin masu amfani.


“An ɗauki wannan mataki ne domin daidaita haɗarin dake tsakanin tsadar gudanar da al'amura da kuma kuɗin da ake cajin masu amfani da wayoyi,” a cewar NCC.


Bugu da ƙari, NCC ta tabbatar da cewa wannan shawara ta samu ne bayan tattaunawa mai zurfi tare da masu ruwa da tsaki a cikin gwamnati da sassan masu zaman kansu, domin tabbatar da cewa ƙarin ya kasance cikin daidaito da bukatun masu amfani da sadarwa.


Previous Post Next Post