Maganin Sanyi Na Budurwa: Abubuwan da Ya Kamata Yan'mata Ku Sani
Sanyi wato infection na budurwa yana daya daga cikin matsalolin lafiya da yan'mata ke fuskanta, musamman na wannan zamani. Wannan ne dalilin rubutun maganin sanyi na budurwa. Wannan cuta tana da matukar illa domin tana shafar sassan jikin budurwa kamar mahaifa, farji, ko mafitsara, kuma tana iya kawo rashin jindaɗi a jikin mace kamar ni'ima ko kuma rashin samun kwanciyar hankali, dalili kuwa yawan jin zafi lokacin yin fitsari. A wannan blog post namu na yau, zamu tattauna abinda ke haddasa shi kanshi sanyi na budurwa, alamunsa, da kuma yadda yan'mata har ma matan aure zasu magance shi cikin sauki ta bayar da shawara daga hukumar lafiya.
Menene Sanyi na Budurwa?
Sanyi na budurwa, wanda ake kira da "infection" a harshen likitanci, yana da nau'i ne daban-daban wato iri iri ne. Wasu daga cikin nau'ikan sanyi da suka fi yawaita a wannan zamani sune:
Sanyi na hanyar mafitsara (Urinary Tract Infection - UTI): Wato shi wannan sanyi yana kama hanyar da fitsari ke wucewa ne zuwa mafitsara wanda hakan ke faruwa sakamakon kwayoyin cuta da suka shiga mafitsara.
Infection na farjin Budurwa: Wannan shi kuma nau'in sanyi ne wanda ke faruwa sakamakon rashin daidaiton sinadarai dake farjin Budurwa (pH imbalance).
Infection na mahaifa: Wannan kalan sanyi ne wanda ke kama budurwa a mahaifarta, wanda ke iya haifar da zafi ko ciwo lokacin al’ada ko kuma lokacin saduwa.
Ga wasu daga cikin abubuwan dake Haddasa Sanyi na Budurwa
(1). Rashin tsafta yayin amfani da toilet.
(2). Amfani da sabulun wanka me ƙarfin sinadarai musamman na bleaching akan farji yayin yin wanka.
(3) Saduwa ba tareda kariya ba, wato Saduwa da me cutar ba tareda condom ba.
(4) Rashin yin tsabta lokacin al’adarki.
(5) Yawan amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta kamar irin su (antibiotics) ba tareda shawarwarin masana ko likita ba.
Alamomin Sanyi na Budurwa
Idan ke budurwa ce kuma kina tunanin kina da sanyi, ko kuma kina ganin wasu abubuwa wanda biki saba gani ba a tattare dake, to wasu alamomi na sanyi da zaki iya gani:
(1) Jin zafi ko ƙuna lokacin yin fitsari.
(2) Yawan jin ƙaikayi a farjinki.
(3) Jin wani wari yana fita daga gabanki kuma asali ba haka kike ba.
(4) Fitar ruwa mai kauri daga farji.
(5) Yawan samun ciwon ciki ko zafi.
Magungunan Gargajiya da Na Asibiti Wanda za'a Iya Magance Sanyi na Budurwa
Magungunan Gargajiya:
(*) Ruwan Zogale: Ki tafasa ganyen zogale, ki sha ruwan da ɗuminsa domin hakan yana taimakawa wajen kashe kwayoyin cutar sanyi dake jiki.
(*) Citta da Tafarnuwa: Ana iya amfani da tafarnuwa da citta wajen magance kwayoyin cutar ta infection saboda sinadaran antibacterial dake cikinsu.
(*) Ruwan Kanumfari: Zaki iya tafasa kanumfari ki sha domin shima na magance kaikayi da ciwon ciki.
Magungunan Asibiti:
Tuntuɓi likita domin samun antibiotics da suka dace da irin nau'in sanyin dake damunki yar budurwa. Kada kisha magani ba tareda izinin likita ba.
Likita na iya baki maganin ruwa wanda zaki dinga tsabtace farjinki dashi idan matsalarki tana da tsanani.
Hanyoyin Kariya Daga Sanyi na Budurwa
(*) Yan'mata ki tabbata kina amfani da bayan gida mai tsabta ko toilet.
(*) Kada ki dinga amfani da sabulu mai karfi wajen wanke gabanki lokacin yin wanka; amfani da ruwa musamman mai ɗumi shine yafi dacewa.
(*) Ki kula da tsabta lokacin da kike al’ada, ki rika sauya pad ko tsumman da kike amfani dashi a kai a kai.
(*) Bawai maganar iskanci ba, amma Idan za'a sadu dake yar budurwa ki tabbatar da lafiyarsa ko kuma ayi amfani da condom.
(*) Koda yaushe ki rinƙa shan ruwa mai yawa domin hakan na wanke mafitsara.
Daga karshe
Sanyi na budurwa matsala ce wadda za'a iya kaucewa ta hanyar tsafta da kula da jiki yadda ya kamata. Idan har kina fuskantar matsalar, ki gaggauta tuntubar likita domin samun magani mai dacewa. Kada kiyi amfani da magunguna ba tareda shawarar kwararre ba. Ki tuna, lafiyarki itace abinda ya fi muhimmanci. Nagode.