Jiddatul khair complete novel
Jiddatul Khair Complete Novel is an engaging Hausa narrative that takes readers on an emotional and thought-provoking journey. The novel skillfully blends themes of love, societal values, and personal growth, creating a story that is both relatable and enriching.
The author showcases remarkable creativity in crafting vivid characters like Ahmad and Captain, whose contrasting personalities bring depth to the narrative. Ahmad's simplicity and empathy are evident in his interactions, while Captain's cynicism adds a layer of complexity to the story. Their dialogue is witty and reveals the cultural tensions between modernity and tradition.
The novel doesn't shy away from addressing societal issues, such as the struggles of the underprivileged, as seen in the character of the awara seller. This element gives the story a reflective tone, prompting readers to ponder the realities of life in a challenging environment.
However, the story occasionally veers into lengthy dialogues and repetitive arguments, which could be trimmed to maintain a smoother pace. Additionally, while the love story is central, some readers might feel that it overshadows other potential plotlines, like the exploration of Ahmad's educational pursuits or societal reform themes.
Overall, Jiddatul Khair Complete Novel is a commendable work that balances entertainment with cultural and moral reflection. It is a must-read for lovers of Hausa literature who appreciate stories that intertwine romance with real-life challenges.
Jiddatul khair complete novel part 1
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, mai kowa mai komai wanda ya bani dama na soma rubutun wannan labari mai taken jiddatul khair complete novel, godiya ta musamman zuwa ga abin alfaharina wato momina Hajiya Hajara tareda aunties ɗina wanda nake musu kallon momina domin aunty itama mai iya rawar momy ce, haka_zalika da sauran yan'uwa da abokan_arziki duk bazan barku a baya_ba. Hajiya Adama matar Garban ƙauye ina miƙo gaisuwa da fatan alkhairi da fatan anyi sallah lafiya.
Chamo da tawagarta su ma ba zan bar su a baya ba yayin rubutun wannan littafi na jiddatul khair complete novel. Sophiena nasan ba lallai kiga wannan gaisuwa tawa ba amma dole ne nasa dake, jiddo naji dake Dear, Masoyana abin alfaharina na kawayena koda yaushe ina muku fatan gamawa da duniya lafiya. Da kuma fatan gamawa da iyaye lafiya daga nan har na gama rubutun jiddatul khair complete novel. Nagode.
Kafin dai na soma posting din jiddatul khair novel, ina so na kowa ya sani cewa, duk da wasu da dama daga cikin masoya sun san cewa ni dalibar jami'a ce wacce ke ajin karshe na kammala karatu. In dai taƙaice muku labarin wata biyu da mu soma jarabawar karshe aka shiga yajin aiki, Idan ubangiji Allah ya shiga lamarin Federal government tayi abinda ya kamata to zan koma domin soma jarabawa. Duk da cewa ma nasan na rubuta ɗan abinda ba'a rasa ba daga cikin littafin jiddatul khair complete novel. Ina yi muku godiya da fahimtana.
A hankali yake tuƙin motar yayinda idonsa a kan titi kuma yana sauraron abokinsa, amininsa, sannan ɗan-uwansa da yake zaune a kujera me zaman banza dake cikin motar. Can kuma sai yaja tsaki tareda girgiza kansa, cikin magana a hankali yace "Ni fa dama ka sauya wannan labarin naka Ahmad, domin ta kowace siga ban ga wani amfaninsa ba..."
Dariya friend ɗin nasa Ahmad yayi sannan yace "Toh ai ni yana da matukar amfani gareni tunda ina sonta kuma ina son na aurenta, kaga Captain ka yiwa Allah ka cire son rai ka gayamin menene aibun Maryam wanda ni ban ganshi ba" Wanda ya kira da Captain ya ɗan sa hannu ya shafa gashin kansa mai laushi, yace "Kasan menene?" Kallonsa_kawai_Ahmad_yake_saboda jiran_jin abinda zai_faɗa, nan_Captain_yace "Inason ka_sanar dani da Allah meyasa_ku_hausawa baku_da_wani_zance_wanda_ya_wuce_na_soyayya, ga_abubuwan_ilimi iri-iri_masu_amfani da_ma'ana_wanda_mutum_zai_iya_karuwa_dasu a_duniya.
Amma kullum ku dai soyayya kaɗai kuka saka a gabanku, shin kasan cewar a yan kwanakin nan ina karatu nayi wani bincike kuma har na gano cewa Airplane water is riddled with some bacteria, baya ma da wannan, jiya-jiyan nan na samo cewa.." Ahmad dake masa wani samfurin kallo irin na mamaki ya dakatar dashi ta hanyar faɗar "Wannan kai da duk masu tunani irin naka ku ya shafa, abinda kake faɗa yanzu ba wani abu da zai ƙara min dama sauran mutane irina. "Captain-ya-mayar hankalinsa-gaba-daya kan-driving ɗin-da-yake.
Jiddatul khair complete novel part 2
Ahmad_yace "Duk lokacin_dana kawo_maka magana_akan_Maryam_sai_ka_samo_wata hanya_da_zaka shashantar_da_maganar ko mene_dalili?" Captain yace "Oh! Ok you asked me abinda nake gani a tattare da ita idan banyi kuskure ba ko? " Ahmad yace "Eh fa" Captain yace "To yanzu zaka ji.... da farko dai ita yar ƙauye ce, na biyu kuma bata da wasu abubuwa na burgewa wanda zai sa ka makale mata_malam, da_Allah jifa_undergraduate yarinya_fa?? Abinda yafi komai ɓata min rai shine ita ba wata kyakkyawa ajin farko ba, gatanan gatanan kawai. Haka labarin littafin jiddatul khair complete novel ya cigaba.
Ga dai manyan yan'mata nan a garin da ka baro Abuja, sannan..... tsaftarta kwata-kwata ga tanan dai, amma ba wani abun faɗa a ciki, ina nufin ba wani abun so a ciki ... Shine_ma_babban_abinda_ke_damuwata" Cike_da_mamaki_Ahmad_ke_kallonsa, da_farko dai_kasa_furta_masa_komai_yayi, zuwa_wani_lokaci_kuma_yace "Wani_rashin_tsaftar kaga_tayi??" Captain ya ɗan saci kallonsa sannan yace "Oho, wata rana zaka gani da idonka" Ahmad girgiza kansa yayi yace "You are talking off hook, Maryam tana da abubuwan da ni nake buƙata, ina tunanin wannan shine kawai? Kuma dama halinka idan baka son abu to fa ba zaka taɓa ƙaunar abun ba, ka dinga kashewa mutum ƙwarin gwiwa kenan" Captain ya gyada_masa kai kuma yace "Ehh haka ne, Please a rufe maganar"
Ahmad na ƙoƙarin yin magana ya hango inda ake suyar awara a gefen_titi, da hanzari yace "Captain Please ka ɗan dakata, Ina son siyan abin nan, na manta yaushe rabona da inci awara, tun kafin naje UK fa..." Captain ya ɗan dubi inda ake tuyar awaran ya ƙarawa motarsa sauri yace "Allah kiyaye, saboda na je dauko ka daga railway_station baya nufin zaka mayar da mu gantalallu a hanya.
Menene kuma awara?" Ahmad yace "To malam ka ajiye ni, ai dama ban ce sai kazo ka daukeni a tasha ba, kai kaga dama kasa kanka" Captain yayi kasa da murya yana rage gudun motar yana faɗin "Yanzu Ahmad kasan ta yanda suka sarrafa abun_nan da kake kokarin dole sai ka ci? Kan_titi_ne fa_nan, ka bari_idan_ka_ƙarasa_gida_kasa_ayi_maka, ni wallahi_bana_son_locality_halin_nan_naka"
Cikin murya mai sauƙi Ahmad yace "Su 'yan hanyar ba mutane bane Abu_turrab?" Captain yace "A'a bawai haka nake nufi ba, ina nufin tsaftar abun, basa wani daraja abun, ka gane ai" Ahmad cewa yayi "Kai komai sai kace tsafta, to sannu sarkin malaman 'yan tsafta, ba ruwanka a haka kuma nake son in siya" Captain bai sake cewa komai ba, ganin wani gurin da ake suyan yasa yayi parking, kafin ya karasa yace "To_ai_sai_kaje_ka_siya, amma_a gaskiya_baka_amsa_suna_doctor_ba.
Very careless Doctor wanda baya girmama tsafta" Ahmad na hararansa yace "Ai ba dankali nace maka zanci ba me gida, Awara nace nan wajen kuma dankali suke siyarwa" Captain ya kalli masu suyan yace "Toh ai bansan yanda Awaran take bane, bashi bane wnny din?" Ahmad yace "Bashi bane" Captain yaja mota yana tuki a nutse, can a ƙasan zuciyarsa ya ja tsaki, wallahi Ahmad is just too local for his_liking, Ahmad yace "ga wani wajen can"
Ta ɓangaren wajen da ya nuna masa Captain ya gangara da mota sannan yayi parking, yana duban yarinyar dake suyan awaran yana ɓata fuska, a ranshi cewa yake "shi wannan ko yunwa zata kasheshi anya zai iya cin abinda take yi kuwa?, Shi dai Ahmad ya bude motar ya sauka ya nufi wajen ta, ita kadai ce a wajen sai yara da kuma almajirai dake tsaye a kanta suna jira a basu awara.
Ahmad_yace "Malama_me_awara nawa-nawa ne_awaran_naki?" Ba tareda ta kalleshi ba tace "Ɗaya_Ashirin" Ahmad ya zare idanu ya riƙe waist ɗinsa sannan yace "Ikon Allah, sai kace dai muna faɗa dame awara irin wannan amsawa haka" mai_awara_dai_bata_kalleshi ba ta_cigaba_da_sallamar_yara_da almajiran dake_gabanta, ta_gilashin_mota_Captain ya tsura_musu_ido_yana_kallonsu, shi_dai Ahmad_na_tsaye a gaba ba tareda yace komai ba ganin yanayinta.
Sai da ta sallami yaran dake gabanta sannan ta daga kai ta kalleshi "Na nawa za'a sa maka?" Ahmad ya daga kafaɗa sannan yace "Na dari biyar kawai" Tace " gaskiya ba zata kai ba, sai dai idan zaka jira a soya" Yace "To zan jira a mota" Daga_nan_ya_juya_ya_nufi motar_ya_shiga_yana_kallon_Captain_wanda ya_kau_da_kai_da_sauri_yana_kallon_ɗayan ɓangaren.
Jiddatul khair complete novel last part
Leda guda biyu tayi sannan ta haɗa su gaba_daya a wata ledan_daban, yajin ma ta sashi a wani ledan sannan ta mike ta nufi wajen motar ta mika masa ta gilashin dake bude, amsa yayi yana kallonta cike da murmushi fuskarsa yace "Kamar dai an ɓatawa me awara rai" Ita dai ba abinda tace mishi, nan ya ciri dubu biyu a aljihunsa ya mika mata yace "to gashi" ta daga kai tana duban kudin tace "Na dari biyar kace" Yace "Ehh sai ki rike ragowar canjin ko"
Mai awara ta sauke idonta kasa sannan tace "A'a ka dai bani dari biyar din awaran kawai" Ya bude idanu yace "Dama ana mayar da hannun kyauta baya" ta girgiza kai tace "Ban san waye zance ya bani a gida ba" Cike da sanyin murya ta karasa maganan, Ahmad yayi murmushi yace mata "Sai ki boye kayanki" Daga_haka ya saki_kudin_kasa_yace "sai_anjima_me_awara, Allah_ya_bada_Sa'a" captain_dai_dake_cikin mota_yana_kallonsu_ya_tada_motar_yayi_gaba. Kar dai a sha'afa a karanta littafin jiddatul khair complete novel a tsamiya novels.
Sai da suka kusa fita a titin hayi Ahmad ke cewa "Ina tunanin ko wane condition ne yasa yarinyar nan mai tuyan awara, ƙasar tamu is getting tougher and tougher akan marasa galihu a kullum....." Captain dai yayi, Ahmad yayi kasa da muryarsa yace "a gaskiya ina jin tausayin talaka a kasar nan, yanzu banda yanayin rayuwa me zai saka iyayenta su bar ta a bakin titi tana Irin wannan wnn sana'a?
Ubangiji Allah dai ya rufawa kowa asiri" Still Captain, bai ce ƙala ba, har suka shigo Unguwan_Sarki, ya kalli Ahmad yace "Mu je can gida ne?" Ahmad ya gyara zama kuma yace "Aa kai ni in ga Ummata sannan, da yamma zan_shigo insha_Allah" Captain dai bai ce masa komai ba ya tuƙa har zuwa gidan kanwar momynsa wato Hajiya Ramlah wacce itace mahaifiyar Ahmad.
To aka ce laifin dadi karewa, anan muka kawo abinda ya sawwaka daga cikin jiddatul khair complete novel da muka soma aikinsa yanzu, a tara a lokaci na gaba domin cigaba da karatun littafin jiddatul khair.