Dubai Hausa Novel

Gargadi

Dubai Hausa Novel

Ban amince a juyamin Dubai Hausa Novel ta wata siga ko a ɗauka a karanta a wata kafar sadarwa kamar YouTube ko Tiktok ba tareda izinina ba, yin hakan ko ɗaukar nauyin hakan zunubi ne mai girma, idan har hakan ta kasance to inada yancin da zamu iya hadewa da mutum a gaban hukuma.

Tsokaci na farko:
Labarin Dubai Hausa Novel me ban tausayi ne, taba zuciya, da iya saka zubar da hawaye, labarine na yan safara a ƙasashen ƙetare, rayuwa me cike da ƙunci da baƙinciki.


Tsokaci na biyu:
Ayi sani cewa Dubai Hausa Novel ya kasance ƙirƙirarren labari ne wanda na rubuta da hannuna idan kinga ko kaga wani yanki yayi kama da labarin rayuwarki to ayi mini afuwa domin ba dake nake ba, saboda ban ma sanki ba arashine kurum aka samu.


Sadaukarwa
A matsayina na marubuciyar Dubai Hausa Novel na sadaukar da wannan rubutu nawa ga dukkan masoyana kuma a duk inda kuke rayuwa a fadin duniya, koda yaushe ina godiya da ƙaunarku a gare ni.


Jan kunne
Idan kin kasance mace me saurin sha'awa to kada ki karanta min Dubai Hausa Novel ballema kiji wani abu kice nice sanadi ni kam babu ruwana. Ba wai na hana budurwa karantawa bane amma kada ki zargeni ko ki kuka dani domin babu ruwana.

Dubai Hausa Novel bangare na farko 


DUBAI
Harabar Beachwood cike take da mutane dandazon matasa ne maza da mata sunata kaiwa da kawowa a wannan yammaci na ranar asabar wacce ke dai-dai da 6/2/2016.

Akasarin waɗannan samari da yan'mata yan safara ne ma'ana mutanenmu ne yan Afrika waɗanda suka tsallaka ƙasashen ƙetare domin neman abun duniya wato arziki, wani samfurin kiɗa ne ke tashi jefi-jefi kana jiyo shewarsu sunata cashewa.

Can ta ɓangare guda na hangi wata tsaleliyar matashiya doguwa me ƙirar irin ta Coca-Cola a baya, inda ta riƙe wani ƙarfe ta zubawa ruwan idanu tana kallon yadda yake tsiri yana tasowa sama yana fantsama tamkar zai yi ambaliya.

Lokaci zuwa lokaci kuma tana sauke ajiyar zuciya tana lumshe idonta saboda ruwan da yake watsuwa akan fuskarta ba ƙaramin dadin hakan take ji ba har ƙasan tafasasshiyar zuciyarta wacce kwana biyun_nan ta kasa hutawa da raɗaɗin tunani gamida damuwar da bata san dalilinta ba sam.

Ji tayi an rungumeta ta bayanta an sauke mata wani zazzafan sumbata a saman rantattsen dogon wuyanta, nan take ta lumshe idonu tareda sauke daddadan ajiyar numfashi, tallafo kansa itama tayi ta shafa domin ƙamshinsa kadai ya isa ta gane wanene.

Sanya hannunsa yayi cikin salo da nutsuwa ya juyota sannan ya ɗora dan_ƙaramin bakinsa na larabawan asali kan kyakkyawan Leɓanta, yasa hannu ya ɗago kanta yace cikin harshen_larabci “Habeey Menene yasa kika gudo nan kika ƙyaleni inata faman nemanki?"


Dubai Hausa Novel
Dubai Hausa Novel part 1

Cike da sanyin jiki ta janye jikinta daga nasa sannan taja hannunsa suka zauna a wata kujera suna mai fuskantar juna, ta motsa ɗan ƙaramin bakinta “naji rai na babu daɗi ne shiyasa tunanin mahaifana da yan'uwana yana damuna sosai inason tare da ummuna" murmushi yayi yana mai shafa doguwar fuskarta kana yace “kina tareda ni kina tunanin wasu Habeey, ni nayi tunanin baki da wani tunanin daya wuce nawa yanzu, ni dai don Allah kar kice min a'a, ki bini gidan_mu yau mu kwana tare zan baki kuɗaɗe masu tarin yawa sannan kuma zan siya miki kayan kwalliya masu kyau da gwala-gwalai masu tsada"

Kawar da kanta tayi yayinda gabanta ke cigaba da tsananta faduwa tace cikin karayar zuciya “ka sani Nazan ba wai bana son in bika bane, a'a kawai tsarina ne bana zuwa gidan saurayi idan har kana son rayuwa dani kayi  mana booking ɗaki a hotel muje mu kwana idan safiya tayi ka sallameni kurum na kama gabana"

Yarfa hannunsa yayi kana yace “ok...." Nufowar wata matashiyar budurwa_ne ya sashi hadiye maganarsa bayan zuwanta ta kamo hannun Habeey tana cewa “Gaskiya Habeey baki da kara ace ranar birthday dinki da gayenki Patrick ya shirya ni ƙadai na ƙawata wajen da rawa amma ke kuma kin koma gefe kin wani maƙale sai nemanki gayu suke tayi"

Janye hannunta Habeey tayi tace “ki ƙyaleni please Aysher yau na tashi kwata-kwata bana jindadi da ƙyar ma na fito wallahi sauƙintama na faɗawa Patrick ba zan koma da wuri ba sai zuwa safiya "janyeta Aysher tayi suka tunkari filin rawar suka kutsa kai suka fara jujjuya jikinsu a hankali, cikin shigarsu ta riga da wando wanda suka fito da asalin surar jikinsu me daukar hankalin namiji, musamman Habeey wacce komai na surar jikinta ke fuzgar duk wani namiji mai lafiya.

Nan fa gaba ɗaya fili ya kacame da shewar samari da sauran yanmatan da suka riga suka sallama rayuwarsu a harkar kamar yanda Habeey ta zabawa kanta.

Ji tayi an wani fizgota da ƙarfi an curota daga tsakiyar dandazon samarin da suka zagayeta suke ta mata likin kudade bana kaɗan ba, idanuwanta a rufe suke gaba ɗaya domin feshin madarar da ake yi duk ya ɓata mata fuska, kuma bata samu ta goge ba sai ma faman turjewa da take yi.

Beyi wata-wata ba ya sungumeta ya nufi inda motarsa take ya jefata a ciki sannan ya kulle ya zagaya ya shiga dai-dai lokacin data samu damar goge madarar fuskar tata, bude manyan lumsassun idanu tayi a kansa, gabanta ne yayi wata muguwar faduwa domin ba tayi tsammaninsa a dai-dai wannan lokacin ba, iyakar saninta dashi shine sunyi sallama sati uku da suka gabata akan ya tafi Qatar zai shigo da wasu kayansa. Cikin yanayin tsoro cewa tayi “Taheer yaushe_ka_dawo? kuma taya kasan inda nake?"...

Dubai Hausa Novel bangare na biyu 


Kuyi sani cewa idan kinsan kinada saurin sha'awa to kada ki karanta Dubai Hausa Novel ballema kiji wani abu kice nice sanadi nikam ina ƙara nanatawa babu ruwana. Ban hana kowa karanta Dubai Hausa Novel ba amma kada ayi kuka dani wannan shine.


DUBAI
Haɗiye wani yawu da ya tsaya masa a baki me daci yayi ya dora hannunsa saman sitiyarin motar ya soma tuƙawa cikin iyawa yana sauke numfashi lokaci zuwa lokaci har suka fice daga Beachwood din gaba ɗaya kana ya furzar da iska ya lumshe idanunsa haɗi da sake taka motar a guje yana cije Leɓansa na ƙasa.

Sarai tana sane cewa ba sabon abu bane tashin hankalinsa domin haka ta soma shirya irin maganganun da zata gaggaya masa idan ya fiye takurawa rayuwarta.

Shi dai bai yi magana ba har suka isa harabar wani katafaren Hotel wanda a samansa aka rubuta Island, dagowa tayi dai-dai lokacin da shima ya dago nan suka haɗa idanu kowannensu na karanto wani saƙo a idon dan uwansa.

Babu abinda Taheer yake ganowa cikin idanun Habeey face wata tsan_tsar rashin gaskiya, inda ita kuwa Habeey ke karanto tsananin tuhumarsa a cikin idon nasa gareta.

Bata iya juriyar kallon ƙwayar idonsa na tsawon lokaci wannan dalilin ya saka Habeey yin ƙasa da kanta yayi wata ajiyar zuciya tareda girgiza kai sannan ya bude ƙofa ya fice itama fitowa tayi tabi bayansa.

Kai tsaye linta suka hau wacce zata kaisu sama suka dan yi tafiya ta karamin lokaci kana suka tsaya a jikin wata ƙofa nan ya kara hannunsa take kofar ta bude ya shiga, tana mai bin bayansa sannan ya mayar da ƙofar ya kulle tareda jingina bayansa a jikin kofar.

Dubai Hausa Novel
Dubai Hausa Novel last part 

Sai a wannan lokaci ya shirya magana yana motsa ƙaramin bakinsa cikin natsuwa tareda lumshe idonta fuskarsa babu annuri yace “tun wace rana kika bar dakin nan?" Kallonsa_tayi cikin_razana saboda_tambayar ta faɗo_mata ba_shiri kuma_bata shirya_amsawa ba.

Sake matsawa yayi kusa da ita taja-da-baya cikin zafin nama ya shaƙota yace “ba kowane kalar iskancin ballangaza zuciyata take iya jurewa ba mafi munin abinda zaki yimin na tsaneki shine rashin riƙe alƙawari, eh na yarda ni dan bariki ne amma nasan muhimmancin riƙe alƙawari dan haka Wallahi sai kin fada min uwar me ya fitar dake daga cikin hotel din nan?"


Tattara ƙarfinta waje guda tayi ta tureshi tace “dakata Taheer bana son shisshigi cikin lamarin rayuwata sannan kuma bana son tuhuma ta rainin wayo, Ina ruwanka da ko wane lokaci nabar ɗakinka dama munyi da kai cewa zan zauna yin gadin room naka ne..."

Yanda taga ya tunkarota a fusace yasa taja-baya da sauri, hakan yasa ya tsaya yana huci tamkar wani baƙin kumurci itama Habeey tana huci yace.

“Naji ba muyi_alƙawari dake cewa_zaki zauna kimin gadin_daƙi ba, amma ai munyi tsakanina dake_cewa ba_zaki ƙara_sauraron wani_saurayi ba, idan bani ba meyasa_yanzu zaki_tafi club har ki shiga tsakiyar fili kina rawa wasu yan'iska suna miki liƙi suna shasshafeki? cikin ɗaga murya taheer yace Inahhh! inahhh!! inahhh!!! Habeey ba zai yiwu ba dole ne ki bar waɗannan yan'iskan mazan naki ki tsaya iya ni kadai domin muyi rayuwa ingantacciya wacce zata kaimu ga alfahari a gaba wai menene laifina menene na gaza biya miki meye kike so na kasa yi miki shi gayamin ko mene a faɗin wannan duniya"

A tara a post namu na gaba domin cigaban Dubai Hausa Novel cikin sauƙi.
Previous Post Next Post