Coca Cola Na Zubar Da Ciki

Shin wai Coca Cola na  zubar da Ciki?

Coca Cola Na Zubar Da Ciki


A yau, anyi tambaya game da tasirin abubuwan sha kamar Coca Cola akan lafiyar jiki musamman ga mata masu juna biyu. Ko kuma nace batun ya ta'allaƙa ne ga batun shin Coca Cola na zubar da ciki. Wasu mutane suna ganin cewa shan Coca Cola na iya haifar da zubar da ciki ga mace mai juna biyu. Amma shin wannan batu gaskiya ne? Da izinin mai duka wannan blog post nawa na yau zai yi nazari akan wannan batu, domin na zurfafa bincike kuma na kawo bayani daga bangaren kimiyya da kuma fahimtar mutane.

Coca Cola da Juna Biyu

Coca Cola wani abin sha ne mai dauke da sinadarai daban daban kamar su caffeine, sukari, da kuma wasu abubuwan haɗe-haɗe. Duk da cewa shan Coca Cola bashi da wata matsala ga mata masu juna biyu, amma akwai wasu abubuwa da ya kamata a kula dasu:


Caffeine:

Coca-Cola yana dauke da sinadarin caffeine, wanda sinadari ne da zai iya kawo tashin hankali idan an sha shi da yawa. Masana sun bada shawarar cewa mata masu juna biyu su rage yawan amfani da caffeine domin gujewa yin tasiri ga cigaban jaririnsu a cikin mahaifa. Anan kai tsaye amsar wannan tambaya ta shin coca cola na zubar da ciki ta bayyana wato ayi sani cewa adadin caffeine da ke cikin kwalbar Coca-Cola guda daya ba zai iya zubar da ciki ba, sai dai idan ansha shi da yawan da ya wuce misali. Sai a kiyaye.


Sukari:

Yawan sukari a Coca-Cola na iya haifar da matsalolin kiwon lafiya ga mai juna musamman idan ansha shi fiye da ƙima, amma bashi da wata alaka kai tsaye da zubar cikin uwargida. Sai dai mata masu juna biyu su kiyaye shan abubuwan sukari domin guje wa cutar sikari wacce take iya kama masu juna biyu anan kiranta da suna (gestational diabetes).


Shin Coca Cola na Zubar da Ciki?

Bisa binciken kimiyya, babu wani tabbaci dake nuna cewa shan Coca-Cola yana iya haddasa zubar da ciki. Sai dai, akwai wasu abubuwa daka iya faruwa da suka shafi yawan amfani dashi Coca Colan da kuma yanayin lafiyar ita kanta mace, wadanda zasu iya haifar mata da matsaloli. Misali:


(*) Idan mace tana shan Coca-Cola fiye da kima har ta samu matsalar rashin abinci mai gina jiki.


(*) Idan mace ta kasance tana da wasu matsaloli na lafiya da ke iya haifar da barazana ga juna biyu.


Shawara Ga Mata Masu Juna Biyu

Duk da cewa Coca-Cola kai tsaye baya zubar da ciki, to ya kamata mata masu juna biyu su kula da abincinsu da abin sha da suke amfani da shi na yau da kullum. Ga wasu shawarwari daga masana:

Rage yawan shan sinadarin caffeine, ba kawai daga Coca-Cola ba, har ma daga coffee da sauran abubuwan haɗin shayi.


Zai fi kyau a maye gurbin shan Coca-Cola da ruwa ko ruwan ya'yan kayan lambu don samun sinadaran da ke taimakawa lafiyar jaririri da ita kanta mai juna biyu.


A koda yaushe yana kyau a tuntuɓi likita kafin shan wasu abubuwa idan akwai bukatar hakan.


Kammalawa

Gaskiya a takaice dai, babu wani tabbaci daga bangaren kimiyya ko wani masani wanda  yake nuna cewa shan Coca Cola na zubar da ciki. Amma, kamar kowane abu akwai bangarori mai kyau da mara kyau, don haka ayi amfani da Coca Cola ba fiye da kima ba, shi yafi alheri, musamman ga mata masu juna biyu. Shawara mafi kyau ita ce kiyaye lafiya ta hanyar bin tsarin abinci mai kyau da kuma shawarar masana. Mun gode.


Me kuke tunani game da wannan batu namu na Coca Cola na zubar da ciki? Muna farin cikin jin ra'ayinku a kowane lokaci!

Previous Post Next Post