Bariki Auren Soja Complete

Bariki auren soja complete

Bariki Auren Soja complete is a compelling novel that weaves a rich tapestry of love, family, and military discipline. Written with a balance of intrigue and cultural depth, it introduces us to Lieutenant Colonel Kamal Ibrahim, a young yet accomplished soldier whose charisma and authority dominate the narrative. The story begins with a vivid scene, setting the stage for Kamal’s striking personality and the respect he commands among his peers.


The novel delves into themes of family bonds and societal expectations, particularly through the dynamic relationships within Kamal's extended household. From his father figure, Alhaji Ibrahim, to his siblings and cousins, the author paints a picture of unity, love, and the subtle tensions that arise in close-knit families. Kamal's mysterious demeanor and dual nature — stern yet caring — add layers to his character, making him both admired and feared.


What sets Bariki Auren Soja apart is its ability to merge the military world with everyday life, offering readers a glimpse into the discipline, challenges, and humanity of soldiers. The dialogue is engaging, and the narrative flows smoothly, blending humor, emotion, and suspense.


However, some readers might find the descriptive style slightly prolonged, but it enhances the immersive experience for those who enjoy detailed storytelling.


Overall, Bariki Auren Soja is a compelling read, especially for lovers of Hausa literature and those who appreciate stories with strong cultural and emotional roots. It promises both entertainment and insight into the complexities of family life and personal ambition.


Bariki auren soja complete part 1

Jinjina a gareku masoya. A koda yaushe ina muku jinjina irin ta ban girma domin kullum burin Golden pen writers Association shine saka ku nishaɗi da faɗakar daki, yau ma kuma bamu yi ƙasa a gwiwa ba domin mun zo muku da littafin bariki auren soja complete novel ga masu bukatar karatu.


Ko yaushe ina alfahari da ku domin mun amsa suna mai taken zama na Amana Allah ubangiji ya ƙara mana kauna da kuma son farantawa juna, ga bariki auren soja complete kamar haka:


A kofar gidan na hango jerin taron motoci kamar wasu sarakuna ko nace gwamnoni, amma abin mamakin shine samari ne matasa reras a sansanin kofar gidan.


Ko da kuwa na ɗan matsa kusa, domin na dakko labarin abubuwan da su ke faruwa, sai kawai naga wani abin mamaki. kuma wannan abu shine zai zama maƙogwaron tambihin bariki auren soja.


Wato wani matashin saurayi ne na hango a zaune kyakkyawan gaske ajin-farko wato irin waɗanda ake cewa first class wanda ko a ina aka nuna shi to fa ya kai.


Ba wai fari bane a’a wankan tarwaɗa ne wanda ake cema chocolate kala wato kala mai tsada, kai ka cikar zati sannan kuma da haiba. Ina dai baku labari amma bariki auren soja complete zai shine littafin dani kai na mai rubutu nake matukar so.


Ga dai samari rututu masu ji da samartaka da jini a jika amma fa duk cikarsu a wurin babu kaman shi domin shi na daban ne.


Nima kaina mamakina shine to wai shin wane wannan ɗin da samari suka zagaye shi haka?

Bariki auren soja complete
Bariki auren soja complete part 1

_KAMAL_

Lieutenant_colonel Kamal Ibrahim ne ƙaraminsu babbansu (the youngest_colonel)


Shine gaba-daya samarin suke zagaye dashi, shi kuwa gaba ɗaya hankalinshi ba abinda yake yi sai faman danna wata tsadaddiyar wayar dake hannunsa, babu shakka wannan ita ake cewa Smart phone yar yayi.


Ya wani kishingiɗa tamkar wani sabon sarki, saboda kana ganinshi kaga miskilin matashin soja ga wani irin kalai-laita se kace wata mace. yanzu nasan me karatu ya fara fahimtar labarin bariki auren soja.


Hirarsu kawai suke ta faman yi a tsakaninsu, wato su sauran samarin, amma shi Colonel hankalishi na kan wayarshi.


Can na hangi wani matashi wanda ba zasu wuce sa'anni da kamal din ba, ya karaso daf dashi.


Ya matsa dai-dai saitin kunnenshi, yace "Don" ya kamata kayi wani abu fa, gayun_nan su watse domin kasan Alhaji na jiran isowarka ko.


Cikin wata ƙaramar izza ta sojoji kamar kuma baya so yayi maganar, yace “do something?"


Gayen yayi masa murmushi gamida girgiza kai, nan take ya ciro wasu bandir ɗin 'yan dubu-dubu ya miƙawa daya daga cikinsu. 


”Gashi kuyi hakuri da wannan yan canjin kafin ya gama ganawa da mahaifinshi zuwa gobe. Cikin matukar farinciki samarin suka fara yi mishi godiya kai har da masu yi masa kirari “Allah yayi ma general shugaban_matasa sannan suka watse.


Bariki auren soja complete part 2 

Ya rage daga Kamal sai wannan gayen da naji wani a cikin matasan na kiranshi da Samir.


”Don yanzu zaka iya_tsayar da danne-dannen wannan wayar mu shiga_daga cikin gida ko kuwa ya fada cikin kulawa.


Bai ce komai ba, mikewa kawai yayi cikin kuzari irin na sojoji ya kama hanyar da zata kai shi izuwa cikin gidan.


Hmm, wani ajiyar zuciya na sauke ni mai daukar labarin bariki auren soja, domin sai yanzu ne na kare mishi kallo da kyau wato dogo ne sosai wanda ya amsa sunanshi cikakken namiji.


Ubangiji gwanin halitta, domin Allah yayi masa ƙira irin ta sadaukan sojoji Masha Allah.


Abin ne ya bani mamaki domin nasan sojoji basa mu'amala da manyan kaya amma shi gashi har da hula ga wani kuma lafiyayyan nice agogon Rolex a hannunsa tareda takalminshi wow.


_He is damn handsome my fans_


Nan dai suka nufi cikin wannan katafaren gida kai tsaye, kai tsaye wani ɓangare naga sun shiga saboda na lura gida ne mai dauke da bangarori da dama.


Wani lafiyayyen dattijo na hango kishingiɗe a cikin wani madaidaicin falo wanda aƙalla shekarunsa zasu kai sittin koma fiye da hakan.


Yana da cikar zati irin ta manyan mutane da kuma haiba, duba da irin littattafan dake cikin wannan falo ne yasa na tabbatar da cewa eh malami ne.

Bariki auren soja complete
Bariki auren soja complete part 2 

Suka yi saurin ƙarasawa wajenshi bayan sun yi sallama, Kamal ne naga yayi saurin cire hular dake kanshi cikin girmamawa ya durƙusa a gaban dattijon.

Baba mun sameku lafiya? Cikin tsananin farinciki wannan dattijo ya amsa "sannu kamalu" kun samu ƙarasowa ai tun dazu nake so in fita saboda ka fada min zaka iso shine na tsaya jiranka.


Samir ma ya gaisheshi.


Dattijo_yace "Allah ya muku Albarka sannan ya kare ku daga dukkannin_sharri.


Nan suka amsa da faɗin ameen cike da girmamawa.


”nasan_mutanenku na jiranku saboda_haka zaku iya tafiya_bayan kun_huta zamu iya magana.


Cikin tsananin ladabi da biyayya yace “Baba ai mun sallamesu, to duk da haka ku shiga daga ciki ku gaishe da sauran jama'ar gidan ko.


Nan mai rahoton bariki auren soja wato ni, naga sun mike cike da nutsuwa tareda yima dattijon godiya yayinda shi kuma yake binsu da kyawawan Addu’o’i.


Alhaji Ibrahim_Khalil malami ne wanda yasan abinda ya kamata.


Yana zaune ne a cikin garin birnin zaria a unguwar ban_zazzau, gidan babban gida ne, da yake bashi kadai ne a ciki ba, yana tareda kannenshi.


Alhaji Ibrahim shine babban gidan sai kuma mabiyinsa wato Alhaji Suleiman sai kuma ɗan autansu mai suna Alhaji Umar.


Kowannensu yana zaune da iyalinsa duka dai a cikin wannan gida dake cikin birnin zazzau.


Yana da kyau ni mai rubutun bariki auren soja complete nayi bayani, bangarori hudu ne a gidan, bangare na farko shine na Alhaji Ibrahim bangare na biyu kuma na Alhaji umar, bangaren Alhaji Suleiman kuma shine na uku sai kuma ɓangaren karshe na mahaifiyarsu.


Wato tsohuwa mai ran_ƙarfe, hajiya Rabi’atu wadda suke kira da suna gwaggo.


Bariki auren soja complete last part 

Ba wai gidane irin na attajirai ba, amma suna da rufin asiri ba abinda yafi karfinsu a wannan rayuwa tun kafin ma yaransu su girma har su zama wani abu.


Gida ne mai cike da haɗin kai da girmama juna gamida kuma zumunci, sun tara iyali babu laifi amma kusan ko wane lokaci ba zaka taba gane wane ya haifi wani ba saboda tsabar hadin kansu da kuma rashin nuna wariya, gasu tamkar sun fito daga ciki ɗaya gaba ɗayansu saboda tsabar zumunci.


Dukkaninsu suna da matar aure amma banda Alhaji Ibrahim, wato tunda matarsa ta rasu shekaru_biyu da suka gabata, kuma dama duk tsawon zamansu a rayuwa, ubangiji Allah bai basu haihuwa ba har ta kwanta dama.


'Yan uwanshi sunyi ta fama dashi ya ƙara aure amma yaƙi amincewa yace “ya’yansu sun ishe shi a rayuwa.


Idan ba an faɗa maka ba, tofa ba zaka taɓa sanin cewa bai haihu ba a gidan domin komai na yaran gidan ya dauke tun daga karatunsu har zuwa hidimominsu.


Musamman kuma ɗan lelenshi wato Kamal gaba ɗaya yaron ya tashi a gaban shine, shi kanshi kamal din sai daga baya ya gane cewa ba sune suka haife shi ba.


Colonel Kamal ɗane ga Alhaji Suleiman wato ƙanen Alhaji Ibrahim mai binsa, su hudu ne a dakinsu, kuma shine babba duk a cikin gidan sai Safwan, Bilal sai kuma yar autarsu Zainab.


Alhaji umar kuma yayanshi uku duka mata, biyu a ciki sunyi aure sai autarsu wadda take sa'ar Zainab ce mai suna Asma’u wadda suke kira da Husna.


A takaice dai gida ne amma ba wai mai yawan cikar ya’ya ba.


To bari kuma ni marubuciyar bariki auren soja na dawo kan uban gayyar, wato Kamal.

Bariki auren soja complete
Bariki auren soja complete last 

KAMAL_

Wato "Don" kamar yanda abokansa suke ce masa ya samu shiga aikin sojane sakamakon tsananin kaunar aikin soja da yake ne, tun tasowarshi.


Bayan ya kammala Diploma nashi ya samu shiga makarantar horar da sojoji dake cikin garin Kaduna wadda muke cewa N.D.A kuma ya fito da babban matsayi.


Ga shi kuma yanzu har ya kai ga matsayin lieutenant_colonel a cikin aikin cikin shekara talatin da y’an kai.


Kamal akwai girman kai wanda ba wai kannenshi mata kawai ke shakkarshi ba, har ma da kannenshi maza wanda suke y’an Jami’a.


Zainab da Husna kuwa sun tsani ace yau gashi ya shigo garin, ba duka ba zaginsu amma kallo kaɗai ya ishesu.


Husnah_

Tafi kowa tsanar lamarin Kamal saboda tafi kowa sanin waye shi tun tasowarta, a cewarta fuska biyu ne dashi wato annabi a fuska fir'auna a zuciya. 


Wannan shi ake cewa taɓa ka lashe na wannan littafi bariki auren soja complete, domin yanzu muka fara ɗora shi. Amma kar ku damu zamu cigaba da kawo shi a hankali.

Previous Post Next Post