Bakar Aya Hausa Novel

Bakar Aya Hausa Novel 

Assalamu alaikum


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai, daya kawo mu wannan rana wadda na fara aikin sabon littafina mai suna Bakar Aya Hausa Novel dama masu iya magana sun ce rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya.

To masoya barkanmu da wannan rana mai cike da albarka, da fatan kun tashi cikin ƙoshin lafiya. A koda yaushe ina muku fatan alkhairi nasan cewa kuna son littafai na shiyasa koda yaushe nake zage dantse domin samar muku masu fadakarwa misalin wannan kenan Bakar Aya Hausa novel wanda zaku ƙaru da ilimin rayuwa da yawa a cikinsa. Ku kasance dani a kowane lokaci domin karatu dama sanin sirrukan rayuwa kuma ina fatan zaku ji dadin Bakar Aya Hausa Novel dana soma yau. 

Bakar aya Hausa novel

Yau shafinmu na tsamiya novels sun soma ɗora Bakar Aya Hausa Novel domin masu karatu ta yanar gizo wato idan bakya bukatar littafi a zahiri zaki iya karantashi a shafin nasu kyauta sannan ayi sani cewa za'a samu daidaitacciyar hausa ne a shafin domin muna ɗan yi masa gyara domin cigaban gudanar da shafin mun gode da karatun Bakar Aya Hausa Novel a shafin namu.


Ban amince wani ko wata ko wasu kungiya ta mutane su kwafarmin Bakar Aya Hausa Novel ba ta kowacce irin siga har sai an tabbatar an samu izinina saboda inada cikakken iko akan basirata kuma zan iya duk abinda doka ta tanadar domin bin haƙƙina. Sannan sani cewa akwai wasu halaye da ɗabi'u a cikin wannan littafi na Bakar Aya Hausa Novel waɗanda basu dace ba, da fatan za'a fahimceni sannan a ɗaukesu a matsayin wasu darasussuka masu isar da saƙo daga littafin.


Abu na ƙarshe shine ina neman afuwa idan wani ko wata yaci karo da abinda yayi dai-dai da irin rayuwarsa domin ban rubuta Bakar Aya Hausa Novel da niyyar yin hakan ba sam. Nagode sosai a ko yaushe ayi karatu lafiya.


Bakar Aya Hausa Novel part 1

Zaki iya ki ƙara daurewa kinji, ki ƙoƙarta zaki iya, kin kusa dai saura kaɗan kinji, daure-daure gashi_nan kan nashi ina hangoshi. Malamar asibiti ce take fada, wacce duk ta haɗa gumi shar_kaf saboda tsabar firgici.


Na fara gajiya wallahi nurse, jikina duk ya mutu ƙarfina ya ƙare! Share gumi tayi wanda ba'a ce ga adadinsa ba sannan ta kalli wata mace wacce take gefenta, ga dukkan alamu dai tafi waccan ɗin matsayi, saboda kayansu ma ba iri ɗaya_bane.


Ke! yi maza hanzarta ki ƙira likita yanzun-nan, kice ana nemansa cikin gaggawa a dakin haihuwa (labor room 24).


To ranki ya daɗe an gama cewar wannan mata, nan take kuma ta zuba da gudu. Bayan tafiyar matar sake mayar da hankalinta tayi kan hafsa, wadda take ta faman nishi amma kwata-kwata babu ko alamar haihuwa tana kusa, gashi jininta ya hau sosai bai kamata suyi mata CS ba.


Girgiza kanta kawai tayi cike da tausayi, domin duk wanda ya kalleta a wannan yanayin yasan tana shan wahala sosai.


Sannu kinji, bari ya ƙaraso ya duba ko akwai wata matsala, saboda ni gaskiya ban taba ganin irin wannan nakuda ba tunda muke aiki asibitin nan, komai lafiya lau amma kan yaron yaƙi motsawa sam tunda ya soma fitowa.


Malamar asibiti ki sake min allurar naƙudar, insha-allah yanzu sai kiga an dace wata kila,

a'a kiyi hakuri Please, a iya jiya da daddare zuwa yau munyi miki allura kusan biyar, gaskiya ba zae yiwu ki sake ɗaukanta ba yanzu, tanada haɗari ga lafiya sosai.


Bari dai likita yazo muji abinda zai ce, insha-allah zaki haihu cikin koshin lafiya kar ki damu, ubangiji yana tareda ke. Karfafa mata gwiwa nurse ta cigaba dayi akan halin da take ciki, duk da cewa ita kanta ta sare da irin wannan lamari na Hafsa.


Bakar Aya Hausa Novel part 2

Waje ta leƙa nan take suka haɗa ido da hajiya Zeenah, wacce tun ɗazu take kaiwa da komowa a wajen. Ta jefo mata tambaya ya ake ciki malama, ta sauka ne?


Jinjina kai sister suwaiba tayi, wacce shekararta kusan ashirin kenan tana aikin karbar haihuwa, amma wannan kam ya caza mata kai ba kaɗan ba.


Wallahi har zuwa yanzu hajiya lamarin sai duda'i jiya i yau, ni har na soma tsoratama da abin, gashi tana ta faman naƙuda kuma babu haihuwa babu alamunta.


Kai subhanallahi, ni ban ma san menene abinda zanyi ba, ga iya Sayyada ma, sai da aka yi da gaske kafin sannan ta hakura da zuwa asibitin nan, yanzu nasan tana_can ta ɗagawa kowa hankali, gashi itama yarinyar tana shan wahala sosai to me zai hana ayi mata CS, shi me-gidan baya ƙasar, amma kuma ƙaninsa yana gari sai yasa hannu a madadinsa.


Shima hakan ba zai yiwu ba Hajiya, saboda a halin da ake ciki jininta yana cikin hatsari, a kowanne lokaci kuma hakan zai iya zame mata matsala. Suna cikin tattaunawar ne likitan ya ƙaraso wajen da coat ɗinsa, ga dukkan alamu zuwansa kenan.


Ya aka yine sister suwaiba, ance kina son ganina a ɗakin haihuwa, wane irin abu ne haka wanda ya gagareki?. Uhm yallabai wata babbar matsala ce, matar yau kwana uku kenan tana naƙuda, gashi kuma tana matakin ƙarshe, amma kuma jaririn ya gagara fitowa, idan kuma muka saka hannu sai ya koma da baya, sannan ga dukkan alamu yaron bashi da rai.


Bakar aya Hausa novel
Bakar aya Hausa Novel 2

Oh! to abinda zai fi a shirya shiga operation mana, ba zai yiwu a barshi a cikinta har zuwa wannan lokaci ba.


"Uhm-uhm yallabai jininta ya hau da yawa fah, operation ba zai yiwu ba shima" (kina so mu zuba mata idanu ta mutu) dole ne muyi wani abu, gaggauta muje na ganta yanzun-nan.


Naji kince mr Jabeer A Jaan ne ko?

"Eh hakane likita, yana shirin zuwa yanzun-nan" Juyawa yayi yana dudduba file nan suka haɗa idanu ta hajiya Zeena, wacce gaba ɗaya damuwa ta bayyana akan fuskarta.


Barkarki dai ranki ya daɗe?

Yauwa barka da shigowa likita, ya kamata kuyi abinda ya kamata, idan ta kama sai an fita da itane sai mu shirya private jet yanzun-nan, Kar ki damu hajiya, inshallah zamu yi iya bakin ƙoƙarin mu akan lamarin.


Daga nan suka shige bangaren da Hafsan take kwance. Wayar tace tayi ringing, hakan yasa ta koma wajen da su Lailah matar ƙanin mijinta (facalah) suke.


"Hello ina jinka Abdulmalik?"

"Hmm' Umma muna hanyar zuwa hospital ɗin, kuma ina tare da Iya Sayyada, tace wai dole  sai tazo taga halin da take ciki, na kawota ko kuma muyi ta wani gun?"


Sauke ajiyar zuciya Hajiya zeenah tayi sannan tace. "Shikenan ba_komai ka_kawota, idan kayi wani wajenma, kasan bazata haƙura_ba.


Ajiyar wayar tayi tana kallon Lailah wacce take danne-dannen waya. "Lailah Iya tana kan hanya, ya_kamata ki_saka alamar_damuwa a fuskarki, idan baso kike kuyi_ba"

Taɓe baki Lailah tayi gamida cewa.


Bakar Aya Hausa Novel last 

"Ni gaskiya nagaji da zama a wajen_nan wallahi, kawai akan wata_mace zata haihu ace sai_kazo, da muka_zo ɗin uwar-me muka tsinana, idan matsalar_wanine a sakoka a ciki, idan taka ce kuma kai kake magance da kanka"


"To wannan_habaicin naki dani_kike ko kuma da me-gidanki da yace_kizo? ki bar ganin ina cikin wannan jimami ki samu dama a kaina, kin dai fi kowa sanin halina bani da daɗi, batun zama kuma dama ai babu wanda ya riƙeki ki tashi ki kama gabanki, daɗinta-ma kema naki yaran ba lafiya_ƙalau suke ba, shanyayyen ɗanki ma ya isa shara"


"Eh naji shanyayyene, amma surukata bata kashe kishiyoyinta ko, matsala kam ai tana nan a gindinki, surukarki matar ɗan cikinki ta zame miki alaƙaƙai, kowa ya shaida ita ta kashe_kishiyarta, wannan_ma kar ace_komai, saboda biri yayi_kama da_mutum"


Bakar aya Hausa novel
Bakar aya Hausa Novel last 

"Lah ilah! ni Sayyada Tatin, yanzu me zan gani, me zan gani haka, yar jikar tawa tana ciki ranta a hannun Allah, ku kuma kuna-nan kuna fama da hali, ke Zeenatu, wato surukarki bata da lafiyama amma ba zaki daina ɗiban rashin albarka ba ko."


"Amma iyah Sayyada itace fa ta soma, kuma......." "Dallah rufe min baki mutuniyar banza, sai kunyi abu nayi magana sai ku nunamin ku yan zamanin nasara ne, kalleku da Allah kunci kun koshi kun zama tula-tula daku, yayanku na ƙasar masu jajayen kunnuwa suna ta faman holewa, ni kuma yar jikar tawa ƙwaya ɗaya ni kaɗai take da a wannan duniya, amma an kasa yi mata gatan magani, sai paracetamal kuke banka mata tana sha dan rashin imani"


Dukkansu jugum suka yi kamar shaho yaci shirwa suna jinta, ta riƙe yar ƙafarta data ke mata ciwo tanata faman zuba tamkar yayan kanya, idon nan sai ficcincinashi take yi, kaman na ƙwarƙwata.


"Haba Iyah kiyi hakuri, bakya ganin yanda kika tara mana jama'a sai faman kallonki suke, ni gaskiya nayi nadama, dana sani na baroki kin cigaba da kukanki ban taho nan tare take ba"


"Haka Abdulmalik yace yana yatsine fuska" wani uban duka ta kai masa a gadon baya tana cewa. "Gaton uwarka dake tsayen-nan Audu lolo, a gidan uwarwa kaga ina kukan, ko sharri zaka_yimin saboda ka rainani?"


Five lessons from the excerpt of the Bakar Aya Hausa novel:

1. The Strength of Women in Difficult Times: The novel emphasizes the resilience and determination of women, especially during childbirth. Hafsa's ability to endure pain and struggle despite the challenges highlights the inner strength women possess.


2. The Importance of Support Systems: The interactions between Hafsa, the nurses, the doctor, and family members show how crucial support is during critical moments. Encouraging words, prayers, and physical presence can provide comfort and hope in dire situations.


3. The Value of Expertise and Teamwork in Healthcare: The medical team’s collaboration and quick thinking underlines the importance of professionals working together to solve complex medical issues. The story demonstrates the critical role of communication and shared decision-making in emergencies.


4. Challenges of Societal Expectations: Family dynamics and societal pressure are evident, especially through the interactions among Hafsa’s family members. These moments reveal the strain cultural norms and expectations can place on individuals during crises.


5. The Need for Compassion and Patience: The novel calls for empathy and understanding, especially in moments of adversity. The nurse, doctor, and some family members display patience and compassion, which are essential traits in both healthcare and personal relationships.


Wannan shine abinda zamu iya kawowa daga wannan littafi na Bakar Aya Hausa Novel kuma zamu cigaba da aikinsa.

Previous Post Next Post