Alamomin Cikin Ya Mace: Abubuwan Da Ya Kamata Mai Juna Biyu Ki Sani
Juna biyun mace yana ɗaya daga cikin muhimman yanayin dake kawo sauyi ga rayuwar mace, musamman a lokacin da take shirin zama uwa. Wannan yanayi yana zuwa tareda sauye-sauyen jiki da kuma alamomi daban-daban da suka shafi yanayi na lafiyar mai ciki da kuma yanayin bugun zuciya. Sanin alamomin cikin ya mace tun farko nada matukar mahimmanci domin ki samu damar kulawa da kanki da kuma tabbatar da lafiyar jaririn da ke tare da ke. Wannan rubutu zai bayyana miki alamomin cikin ya mace, tareda karin bayani akan yadda zaki kula da kanki a yayin renon ciki naki na musamman.
Meyasa Ake Bukatar Sanin Alamomin Ciki?
Sanin cewa kina dauke da juna biyu da wuri zai baki damar fara samun kulawa da kanki da kuma zuwa ganin likita akan lokaci, wanda hakan zai taimaka ƙwarai da gaske wajen kare lafiyar jaririn da ke cikinki da kuma lafiyarki. Haka kuma, yana rage matsalolin da ka iya tasowa a baya, kamar rashin cin abinci mai gina jiki, cututtuka, ko kuma wasu matsaloli da zasu iya shafar lafiyar mace da jaririnta.
Alamomin Cikin Ya Mace
1. Rashin Zuwan Jinin Al’ada (Menstruation)
Daya daga cikin alamomin cikin ya mace mafi bayyanuwa shine rashin ganin al’ada. Wannan na faruwa ne saboda jikinki yana dauke da kwai da ya narke a cikin mahaifa domin halittar sabon rai. Idan al’adarki ta saba zuwa lokaci guda wanda kin sani kuma amma ba ki gani ba, to wannan na iya zama farkon alamar ciki da zaki iya fahimta. Duk da haka, rashin ganin al’ada ba kullum ke nuna ciki bane, domin wasu dalilai kamar damuwa, gajiya, ko canjin yanayi na iya shafar al’adar mace.
2. Tashin Zuciya da Yawan Amai (Morning Sickness)
Tashin zuciya da yawan yin amai, musamman da safiya, yana daya daga cikin sanannun alamomin cikin ya mace. Wannan yana faruwa ne sakamakon karuwar hormone na hCG da kuma progesterone. Hakan kuma zai iya fara bayyana ne tun makonni biyu zuwa hudu bayan haduwar ƙwan ki da maniyyin namiji. Wannan alamar na iya kasancewa mai wahala ko kuma a wasu lokutan, mace ba zata fuskance ta ba.
3. Canjin Nonuwa
Daya daga cikin abubuwan farko da zaki lura da su lokacin da kika samu ciki shine canjin dake faruwa da nonuwanki. Zai iya zama yayi laushi, kumbura, ko jin zafi. Wasu lokutan kuma, za ki lura cewa kan nonuwa sun yi duhu fiye da yadda suka saba. Wannan duk saboda canjin hormone ne.
4. Yawan Samun Gajiya Mai Tsanani
Jin gajiya ba tareda dalili ba yana daya daga cikin abubuwan farko na alamomin cikin ya mace. Wannan yana faruwa ne saboda jikinki yana aiki tuƙuru wajen samar da sinadaran da jaririn da ke ciki yake bukata. Sinadarin progesterone yana matukar bada gudunmawa wajen kawo wannan gajiya.
5. Yawan Yin Fitsari
Idan kina jin yawan buƙatar yin fitsari fiye da yadda kika saba, wannan na iya zama wata alamar ciki. Wannan na faruwa ne saboda mahaifa tana fara girma tareda matse mafitsara. Bugu da kari, karuwar sinadarin hCG yana sa ƙoda ta rika tace ruwa fiye da yadda ta saba.
6. Canjin Yanayi da Sha’awa Akan Abinci (Kwadayi) (Cravings)
Yawancin mata suna jin sha’awar wasu abinci da ba su saba sha’awa ba, yayin da wasu kuma ke jin tsanar wasu nau’in abinci da suka saba ci. Wannan canjin yana hade ne da hormones na ciki wanda ke sauya yadda jikinki yake gane wasu dandano.
7. Zubar Jini Mara Yawa (Spotting)
A wasu lokuta, mace na iya lura da karamin zubar jini ko kuma jin radadi mai sauki a ciki. Wannan na iya faruwa ne lokacin da kwan ya narke a mahaifa (implantation bleeding). Duk da yake ba kowace mace ce ke fuskantar wannan ba, idan kika lura da hakan yana da kyau ki tuntubi likita.
8. Canjin Yanayi (Mood Swings)
Cikin yana kawo sauyin yanayi da sauyawar bugun zuciya. Za ki iya jin farin ciki na lokaci daya, sannan daga baya ki shiga damuwa ba tare da dalili ba. Wannan yana hade ne da canjin hormone a jiki wanda ke shafar yadda kike ji.
9. Jin Nauyi da Yawan Bacci
A farkon ciki, mace za ta iya jin nauyi a jikinta tareda jin yawan bacci. Shima hakan na daga cikin alamomin cikin ya mace. Kuma yana faruwa ne saboda canjin yanayin jiki da kuma karuwar hormone.
10. Canjin Jiki Kamar Ciwon Kai da Jin Zafi a Wani Sashe
Wasu mata na iya fama da ciwon kai, ciwon baya, ko kuma jin zafi a wasu sassan jikinsu saboda tasirin sinadaran ciki.
Yadda Ake Tabbatar da Ciki
Idan kina ganin wasu daga cikin alamomin da muka ambata a sama, yana da kyau ki tabbatar da ciki ta amfani da gwajin ciki na gida (pregnancy test) ko kuma ki kai ziyara asibiti don a tabbatar miki. Gwajin gida yana amfani da fitsari ne don gano sinadarin hCG wanda yake karuwa yayin ciki.
Abubuwan da Za Ki Kula Da Su Idan Kina Dauke da Ciki
Da zarar an tabbatar da cewa kina dauke da ciki, ki tabbata kina kula da kanki da kuma lafiyar jaririn. Ga wasu shawarwari masu mahimmanci:
Ziyarci Likita: Ki fara samun kulawar lafiya ta farko domin tabbatar da lafiyar ki da ta jaririnki.
Cin Abinci Mai Gina Jiki: Koda yaushe ki tabbatar kina cin abinci mai dauke da sinadarai kamar su protein, carbohydrates, da vitamin.
Shan Ruwa Mai Yawa: Shan ruwa zai taimaka wajen kiyaye lafiyar jini da kuma rage kumburi.
Guje wa Abubuwa Masu Hadari: Guji shan giya, taba sigari, ko kuma amfani da magunguna na babu gaira babu dalili ba tareda shawarar likita ba.
Rage Nauyin Jiki: Idan kina fama da kiba mai yawa ko kumburi, ki nemi shawarar likita don samun hanyoyin da za ki rage nauyin jikinki ba tareda shafar jaririn ba.
Rufe Wannan Rubutu Nawa na Alamomin Cikin Ya Mace
Cikin mace na zuwa da sauye-sauyen jiki masu yawa, wanda kowanne yana da alaka da yanayin jiki da hormones. Sanin wadannan alamomi yana taimaka wa mace wajen kula da kanta da kuma daukar matakan da suka dace domin tabbatar da lafiya. Idan kina da wata tambaya ko kuma kike son karin bayani, kada ki yi kasa a gwiwa wajen tuntubar likita.