Addu'ar Janyo Hankalin Saurayi

Addu'ar janyo hankalin saurayi ko namiji complete post 


Addu'ar Janyo Hankalin Saurayi

Idan ubangiji Allah ya nufa yau zamu yi bayani mai gamsarwa akan hanyoyin da mace zata bi domin jan hankalin namiji, har ma kuma da bayar da addu'ar janyo hankalin saurayi ko mijinki wadda muka samo daga malamai, wato magada annabawa. 


Yana ɗaya daga cikin manya-manyan alfaharin mata suga cewa koda yaushe mijinsu ko kuma saurayinsu yana under their control wato abun nufi shine su kasance namijin da suke so yana biye dasu a kowane lokaci wasu suna yin haka domin so da kauna wasu matan kuwa suna yin hakan domin wata manufa tasu ta duniya. Kaso casa'in 90% na mata na neman yadda zasu janyo hankalin saurayi yanda zasu mallaki zuciyarsa dama gangar jikinsa. 


Kasan ance kowa da kiwon daya karbe shi, maƙwabcin mai akuya ya siya kura, abinda yasa nayi wannan salon magana shine da yawa daga cikin mataye janyo hankalin saurayi ko namiji kan ba wasu wahala saboda wajen rashin gane hanyoyi na yadda zasu bi su mallakin zuciyar namijin cikin sauki. Amma akwai wani abu ɗaya da kuke mantawa dashi a kodayaushe wannan kuwa ba wani abu bane face halaye, kuyi sani cewa halayen maza sun bambanta, abinda nake nufi shine kowane namiji yana da Irin nashi halaye, wannan shine dalilin da yasa zaki ga wata bata yiwa mijinta abinda kike yiwa naki amma kuma koda yaushe hankalinsa yana kanta, hmm, komai zai iya faruwa wata ƙila ta fiki sani na siddabarun mata ko kuma ta fiki sani na addu'ar janyo hankalin saurayi ko namiji masu yawa. Sai dai kuma a koda yaushe akwai abubuwan da dole sune suke zama saurayi ko mijinki yana matukar so. To sai laƙance su sannan ki dinga amfani dasu a kanshi ko Allah zai sa a dace yadda ya kamata.


Uwargida ko nace yan'mata ga wasu hanyoyi har ma da addu'o'i masu sauki da zaku iya bi wajen janyo hankalin saurayi ko miji wanda aka tsarasu bisa koyarwa ta addinin musulunci, Kamar yadda da yawa daga cikin malaman addini ke nasiha da tunatarwa cewa, Aljannar mace na karkashin tafin kafar mijinta ga mata masu aure kenan.

Daga cikin waɗannan halaye na jan hankalin namiji ana so mace:


(1). A kullum ya kasance duk wata magana da zata fita daga bakinki uwargida ko yan'mata mai dadi ce a kunnen mijinki, duk da ance magana zarar bunu ce amma duk da haka ki dinga tankaɗe da rairaya ga kalamanki ga masoyinki, wanda hakan zai saka shi murmushi da jindadi har ma kuma da son kasancewa dake kowane lokaci.


(2). Yar uwa ki kasance mai yawan sakin fuska ga mijinki koda kuwa kina ɓacin rai, kar ki biyewa wata yasasshiyar magana ta cewa "AI GWANDA KI NUNA MASA RANKI YA ƁACI DOMIN YASAN KEMA BA ABAR RAINAWA BACE" wallahi haƙuri shine zai zama silar dorewar zamanki a gidan mijinki, a duk lokacin da ya dawo gida ya same ki cike da farinciki ina miki tabbaci ko ba daɗe ko ba jima sai kin kasance cikin ransa.


(3). Sannan kuma ya kasance a koda-yaushe ki dinga ɗaukar mijinki kamar sarki ne wato shine shugabanki akan komai da zaki aikata, musamman ta wurin mutuntashi domin maza na matukar son a girmamasu fiye da basu abinci, kuma ki dinga yawan juriya wajen daukar laifinsa saboda kawai ki bashi girma koda kece da gaskiya.


(4). Yan'mata kar ki kasance kullum a cikin rashin nuna jindaɗi ko fushi da masoyinki, domin fushi shine kofar kowane sharri. Kar ki ba shedan dama ya saki dana sani.


(5). Kada ki kasance mai ɗagawa da girman kai wajen bashi haƙkokin zaman aure domin kuwa ya cancanta har wajen Allah, abinda yake so koda bakya so matuƙar wannan abu bai saɓawa addini ba kiyi hakuri kiyi mishi.


(6). Na daga hanyoyi na janyo hankalin saurayi ko mijinki ki nuna masa ke wayayyiya ce ta fannin abubuwan kirki, wato kar ki zama sakarai domin maza ko samari na saka ido akan wannan, sannan  ki nunawa masoyinki cewa komai naki mallakinshi ne amma komai nashi wanda ya mallaka miki komai naki ne kar ki raina duk abinda sannan ki so danginsa to kwarai da gaske zai nuna miki so, sannan koda yaushe ki nuna baki da iko akan wani abu sai abinda yayi umarni.


(7). Idan kina so Addu'ar janyo hankalin saurayi ko mijinki tayi aiki sosai, tofa ya kamata kibi dokokin Allah, in har kika girmama abinda addini ya karantar to inshallah kina tareda nasara. Sannan ki zama mai kula da abubuwan da mijinki yake dubawa a jikinki idan ya dawo gida, wato ina dubansa yake yawan kallo a jikinki musamman bayan kinyi kwalliya. Idan kirji ne sai ki dinga a gyarashi da kyau. Idan baya ne wato mazaunai yake yawan kallo sai a gyara domin a janyo masa hankali. Idan kuma kin fahimci duk lokacin daya dawo yana yawan neman buta ne, to sai ki kula sosai da zuba ruwa a butar.


To yanzu kuma ga jerin ADDU'AR JANYO HANKALIN SAURAYI KO NAMIJI muna fata Allah ya karɓa cikin gaggawa.


Arabic Text: وَإِذَا رَأَيْتَ ثَمَّ رَأَيْتَ نَعِيمًا وَمُلْكًا كَبِيرًا

Transliteration: WA, IZA RA, AITA SAMMA RA, AITA NA, IMAN WAMULKAN KABIRA


Idan kina so ubangiji ya juyo da hankalin saurayinki ko mijinki, ki rubuta wannan ayar  WA,IZA RA,AITA SAMMA RA, AITA NA,IMAN WAMULKAN KABIRA kafa 41 sannan ki saka  sunan saurayin da zaki yiwa aikin a cikin MIMUN wato MIIM sannan a samo gishiri a saka dai-dai sunan wanda zaki yiwa sai kuma a barshi ya bushe tareda gishirin gaba ɗaya, a wanke asha to insha-Allahu Allah zai juyo miki da hankalinsa zuwa gareki yaji yana matukar ƙaunarki.


Arabic Text: إِنَّهُ عَلَىٰ رَجْعِهِ لَقَادِرٌ

Transliteration: INNAHU ALA RAJA'IHI LAƘADIRIN


Addu'ar janyo hankalin saurayi ko namiji ta biyu kuma wuridi ne, ki daure kiyi wuridin ( INNAHU ALA RAJA'IHI LAƘADIRIN ) sau (33313) sannan ana so a kammala wannan wuridin aikin a cikin kwana (7) sannan bayan an gama sai ayi sadaka da waina/masa mai zafi guda (19) Insha-Allahu ta'alah hankalin ko waye zai dawo ana farawa a rana irin ta yau juma'a.


DOMIN SAMUN INGANTACCIYAR SOYAYYA MAI DOREWA


Idan kina son magance matsalar yaudara ko ha’incin soyayya, ko kuma dawo da masoyinki, ko karuwar soyayyarki a zuciyarsa, abu na farko shine wannan abu da zamu bayar amana ce. Kada kiyi shi domin tozarta wani ko cin zarafinsa.


Nemi fararen takardu marasa layi guda 7, sai ki rubuta wannan sirri a jiki sannan ki dinga kona takardun daya bayan daya.


Don Allah, kada a yi wannan abu dan ramuwar gayya ko don wulakanta mutum, sirri ne mai karfi.


Da tawadar midadul’ishq ake rubutun, idan an gama, sai a tura da tiraren nadilhabib.


MUHIMMAN ABUBUWAN DA KE JAN HANKALIN MIJI ZUWA GA MATARSA


Ba wai kwalliya da iya magana kadai ke janyo hankalin saurayi ko namiji zuwa ga mace ba, musamman ga matan aure, akwai abubuwa da yawa da suke jan hankalinsa.


Misalan abubuwan dake jan hankalin miji sun hada da tsafta, biyayya, hakuri, girki, iya kwalliya, iya sarrafa harshe wajen magana, da kuma girmamawa.


Wadannan abubuwan suna kara dankon soyayya da kaunar juna a tsakanin ma’aurata.


Ki sani idan ke budurwa ce addu'ar janyo hankalin saurayi tana da muhimmanci amma kuma ke ma dole sai kin jajirce wajen yin abinda ya kamata.


Wasu mata suna da sanin yadda za su janyo hankalin saurayi ko mazajensu amma basa yin hakan saboda wasu dalilai kamar rashin so ga wadanda aka yiwa auren dole ko kuma malalaciyar mace me son jiki.


Shawara ga mata masu lalaci: Ki tashi ki gyara domin lalacinki zai iya sa mijinki fita waje ya nemo wadda za ta yi masa abinda kike kasa yi.


Idan aka yi miki auren dole, ki karbi kaddararki, ki daura damarar gyara aure domin samun farin ciki da kwanciyar hankali.


NASIHAR GYARAN RAYUWAR AURE


Duk da cewa kwalliya da iya magana nada tasiri, akwai muhimman abubuwa kamar ladabi, biyayya, hakuri, kawaici, da kuma girmama abin da mijinki yake so.


Wasu mata suna jin tsoro, kunya, ko girman kai, don haka ba sa nuna soyayya ko kulawa ga mazajensu. Wannan yana iya zama matsala.


Kiyi kokari ki gyara, domin zamanin yanzu matan waje na kokarin janye hankalin mazajen gida.


A batun aure, babu kunya ko boye-boye, domin kun zama daya. Gyaran aure yana hannunki.


ZANCE NA KARSHE


Duk matar data san hanyoyin farantawa mijinta ko budurwar data san hanyoyin janyo hankalin saurayi to fa zata samu farinciki a gidanta.


Aure wata dama ce ta samun farin ciki da nuna soyayya ga juna. Don haka, mu yi kokari wajen gyaran zamantakewa domin samun ingantacciyar rayuwar aure.
Previous Post Next Post