Mijin yarinya hausa novel
Barka da shigowa gidan littattafai Mijin yarinya hausa novel ne wanda muka ɗora shi bayan karbar izini daga marubuciya, mun godiya.
English Version
Mijin yarinya hausa novel part 1
"A village-girl-is-daring-me, I swear-she-will learn-her-lesson. She will know who she's talking to," he said, exhaling a heavy breath.
Hafiz, sitting and watching him, said, "Calm down, my man! Now, where did you meet this girl that made you so upset? And what exactly did she do to you?"
He took about five seconds before opening his eyes, then closed one in frustration. "She is my wife," he said.
Hafiz's eyes widened in shock. "What? Do you even know what you're saying? Your wife? Are you serious? When did you get married without telling me?"
Saif waited for his question to settle before answering, biting his lower lip slightly. "Yes. When I returned from America, Dad visited a village, and that’s where they matched me with her."
He then narrated the events that led to his marriage, including what Fatima did before he left the house.
Hafiz burst into laughter, holding his stomach. "Are you serious, man?"
Saif shot him a dirty look. "Oh, it’s funny to you, huh? That girl said she needs a massage. Can you imagine?"
He clicked his tongue in frustration and added, "May God forbid me from touching a girl who isn’t even 15 years old. What would I do with her? She's just a child! And you’re here suggesting I give her a massage? You must be out of your mind."
Hafiz, still amazed, said, "You mean she isn’t even 15, but she said that to you? My friend, this is what they call ‘a girl’s husband.’ Seriously, you need to stay strong and be patient." He tried to suppress his laughter, seeing the irritation on Saif’s face.
Saif shot him another sharp look. "It’s easy for you to laugh. Of course, it didn’t happen to you. I swear, if I want to, I’ll tell Mom to force you into marriage so you can feel my pain. And don’t let Baby hear about this!"
Mijin yarinya hausa novel part 2
Hafiz laughed again. "Ah, the drama of love, my man. My advice? Stay calm, respect your parents, and let things play out. One-day, you’ll be-proud-of-your-decision."
Saif looked away in annoyance. "God-forbid I ever-love-that-village-girl. She doesn’t even have class, let alone grace."
Hafiz shook his head. "Hmm, take it easy, my friend. You might come back asking for advice one day."
Saif closed his eyes, exhaling deeply as if he had just run a race. After a moment, he said, "I’m leaving now. Let me greet Mom and head out."
Hafiz stood up quickly, laughing. "So you’re mad just because I told you the truth? May God calm your heart."
They both went to greet Mom. She was sitting and watching them. "Oh, welcome back, America’s finest! When did you return?"
Saif smiled. "Good morning, Mom. All is well."
After a brief conversation, they bid her farewell and left. Hafiz walked him to the parking space.
As Saif got into his car, Hafiz said, "Say hi to your bride for me. I’ll come to greet her soon. And send my regards to Mom too."
Saif-rolled-his-eyes, started his car, and-drove off.
On Ruky’s side, she entered the house to find Aunt sitting in the parlor with a stern face. Aunt looked at her angrily and said, "Ruky, who died that you’re bringing someone to greet me? Why can’t you be composed and responsible? Remember, you’re now an adult, and such behavior doesn’t suit you, especially as a woman."
Mijin yarinya hausa novel last
Ruky glanced at her from head to toe, clicked her tongue, and said, "Come on, Aunt. Just because someone greeted you, you’re raising your voice? Whoever will be yours had better be ready." With that, she went upstairs with the clothes Saif had given her.
Aunt watched her with frustration, shaking her head. "May God guide you, Ruky. May He send someone who can handle you." She stood up and went to the kitchen, still shaking her head.
Ruky entered her room, threw her clothes on the bed, and sat down, thinking. How would she win over Saif? She was determined to marry him, for in her heart, she had already tasted his sweetness.
She remembered her friend, Sumy, and quickly picked up her phone, scrolling for her number. She called, and after two rings, Sumy answered, "Hello, dear! How are you doing?"
Ruky smiled. "I’m fine, dear. Are you home? I’m coming over. We need to talk."
Sumy chuckled. "Really? Okay, I’m waiting, dear."
Ruky ended the call, grabbed her car keys, and left the house. Aunt, still in the kitchen, heard her leave and shook her head. "I need-to-do something-about-this-girl. I must-find a solution."
On Fatima’s side, they finished tidying up their parlor. Everywhere was sparkling clean. They swept, mopped, lit incense, and sprayed air freshener, filling the room with a pleasant aroma.
Fatima looked around and said, "This place looks beautiful. It smells amazing too."
Sona smiled. "This is how it should always be. From now on, if you’re told to clean, this is how you’ll do it."
Fatima smiled and nodded in agreement. After locking up, they went to their room. Sona took a bath, performed ablution, and began her prayers.
Fatima, on the other hand, only performed ablution before joining her in prayer. When they finished, Sona dressed up and looked at Fatima.
"Go take your bath," she said.
Fatima grumbled but went to the bathroom. After bathing, Sona styled her hair, making it shiny and beautiful. Fatima was thrilled, admiring her new look.
Sona continued to praise her. "This hair looks amazing."
She handed Fatima some clothes Mom had given her the day before – blue jeans and a pink T-shirt. Wearing them, Fatima looked stunning, almost unrecognizable. Despite her youth, she had height and glowing skin that made anything she wore look good.
Sona took her phone and snapped several beautiful pictures of Fatima.
When they went back to the parlor, Mom, who was scrolling on her phone, looked up and was stunned. "Wow, my daughter! You look so beautiful!"
Fatima shyly lowered her head, smiling. "Thank you, Mom. May God bless and increase you."
Mom smiled and returned to her phone. Fatima and Sona sat, chatting.
Just then, Saif entered the parlor, greeting them. They all responded. When he looked up, his eyes met Fatima’s. He closed his eyes briefly, amazed at how beautiful she looked, unable to hide his surprise.
Hausa Version
Mijin yarinya hausa novel part 1
"Wata-yar-kauye-ce ta-dameni, wallahi-sai-ta gane-kurenta. Zata san da wa take magana," ya fadi yana sauke wata iska mai zafi daga bakinsa.
Hafiz, wanda yake zaune yana kallonsa, ya ce, "Ka kwantar da hankalinka, my man! Yanzu dai a ina ka hadu da wannan yarinyar har ta baka rashin kunya? Kuma wane irin rashin kunya ne haka da ya sa ka rikice?"
Ya dauki kusan dakika biyar kafin ya bude idanunsa, sannan ya lumshe daya cikin takaici, ya ce, "She is my wife."
Hafiz-ya-zaro-ido-cikin-mamaki, yace, "What? Ka san me kake fada kuwa? Matar k'afa kake nufi? Yaushe kayi aure ban sani ba?"
Saif ya jira tambayarsa kafin ya amsa, yana dan cije lebensa na kasa. "Yes. Dawowata daga America kenan, Dad ya kai ziyara kauye, kuma a nan aka hadani da ita."
Daga nan, ya ba Hafiz labarin yadda abin ya faru, har da abin da Fatima ta masa kafin ya bar gidan.
Hafiz ya kwashe da dariya, har yana rike cikinsa, ya ce, "Are you serious, man?"
Saif ya wurga masa wani kallo na banza, ya ce, "Oh, dariya ma nake baka? Toh ba d'uleba, yarinyar nan ta ce wai tana bukatar tausa. Ka ga ai baka yi mata ba!"
Mijin yarinya hausa novel 1
Tsaki Saif ya ja cikin takaici, ya ce, "Allah ya tsare ni daga taba yarinyar da bata kai shekara 15 ba. Me zanyi da ita? Wannan ai ko kwaila bata kai ba! Kuma ka tsaya kana ce na mata tausa? Lallai kai ma ba ka da lafiya."
Hafiz ya kara zaro ido cikin mamaki, ya ce, "Kana nufin bata kai shekara 15 ba, amma take wannan maganar? Wallahi wannan shi ake kira 'mijin yarinya'. Gaskiya, abokina, ka daure sosai ka kai zuciya nesa." Ya fada yana kokarin danne dariyarsa, ganin yadda fuskar Saif ta canza tamau.
Saif ya wurga masa wata uwar harara, ya ce, "Dole kayi dariya, ai ba kai aka yi wa haka ba. Wallahi idan na ga dama, sai na ce wa Mami ta aura maka dole, ka ji yadda nake ji. Kuma ka rufa min asiri kar Baby na ta ji wannan maganar."
Hafiz ya dara, ya ce, "Ka ji duka cikin soyayya ne, my man. Ni dai shawara ta gareka shine, ka daure, ka bi komai a hankali. Ka rage girman kan nan naka, ka yi biyayya ga iyayenka. Wata rana zaka yi alfahari da hakan."
Mijin yarinya hausa novel part 2
Saif ya dauke kai cikin takaici, ya ce, "Allah ya kiyaye ni daga son wannan yar kauye. Ai ba mata masu aji ba, balle wannan dak'ik'iyar kauye."
Hafiz ya girgiza kai, ya ce, "Hmmm! Abi a hankali, malam. Kar wata rana ka dawo kana neman taimako."
Saif ya lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya kamar wanda yayi wasan gudu. Bayan-wani-lokaci, yace, "Ni-zan-wuce. Bari na shiga gaida Mami, sannan na tafi."
Hafiz ya tashi da sauri, yana dariya, ya ce, "Toh fushe zakayi saboda na fada maka gaskiya? Toh Allah ya huci zuciyarka."
Daga nan, suka shiga dakin Mami suka gaisheta. Tana zaune tana kallonsu, ta ce, "Ah-ah, sannu da zuwa, mutanen America! Yaushe kuka dawo?"
Saif ya murmusa, ya ce, "Ina kwana, Mami? Lafiya kalau."
Bayan hira kadan, suka sallameta suka fita. Har parking space Hafiz ya rakashi.
Yana shiga mota, Hafiz ya ce, "Ka gaida min da Amarya, sai nazo gaisheta. Ka gaida Momy ma."
Saif ya tabe baki, ya ja motarsa ya fice daga gidan.
Bangaren Ruky kuwa, tana shiga cikin gida, ta sami Anty zaune a parlour fuska a daure. Anty ta kalleta cikin bacin rai, ta ce, "Ke Ruky, uban wa ya rasu da zaki kawo wani ya gaishe ni? Me ya hana ki nutsuwa da kamun kai? Kisani fa yanzu kin girma, kuma bai dace kina irin wadannan abubuwan ba, musamman a matsayin mace."
Ruky ta dube ta daga sama har kasa, ta tabe baki, sannan ta ce, "Haba Anty, saboda kawai mutum ya gaishe ki shine sai ki daga min murya? Ai shi fa wanda zai zama na ki ne, garama ki shirya." Bayan ta fadi haka, ta hau sama da kayan yakinta da Saif ya bata.
Mijin yarinya hausa novel 2
Anty ta bita da kallo cike da takaici, tana girgiza kai, ta ce, "Allah ya shirye ki, Ruky. Allah ya kawo wanda zai iya maganinki." Ta mike ta wuce kicin tana girgiza kai.
Ruky ta shiga dakinta, ta zube kayan hannunta a kan gado sannan ta zauna. Tunani ta fara yi – tayaya zata samu Saif a hannunta? Tabbas ta kuduri niyyar sai ta aure shi, domin a halin Saif, ta dandanawa kanta zumarsa.
Sai da ta tuna da wata kawarta, Sumy, da sauri ta dauki waya, ta fara laluben lambar ta. Ta kira, bayan ringi biyu Sumy ta dauka tana cewa, "Yar duniya, kina nan kuwa?"
Ruky ta murmusa, ta ce, "Ina nan wallahi. Yanzu dai, idan kina gida, gani nan zuwa, akwai magana."
Sumy ta murmusa, ta ce, "Da gaske? Toh ina jiranki, yar duniya."
Ruky ta kashe wayar, ta dauki makullin motarta, ta fice daga gidan. Anty dake kicin ta ji fitar ta, ta girgiza kai, tana cewa, "Gaskiya zan yi wani abu a kan yarinyar nan, dole na nemo mafita."
A bangaren Fatu kuwa, suka kammala gyara parlour nasu. Ko ina ya kasance tsaf, suka share, suka mopping, suka kunna turaren wuta, sannan suka feshe dakin da air freshener. Ko ina ya cika da k’amshi.
Mijin yarinya hausa novel last
Fatu ta kalli aikin, ta ce, "Gaskiya, ko ina yayi kyau. Sai k’amshi abin burgewa."
SONA-ta-murmusa, tace, "Ai wannan-ce ya-kamata. Daga yau idan aka ce ki gyara haka zakiyi."
Fatu-ta-murmusa, tareda-daga-kai-alamar amincewa. Bayan sun rufe bangaren, suka wuce dakinsu. SONA ta fara wanka tare da daukar alwala, sannan ta tada sallah.
Fatu kuwa, sai da ta yi alwala kawai sannan ta fara sallah. Bayan sun gama sallah, SONA ta shirya tana kallon Fatu.
Ta kalle ta, ta ce, "Tashi kije kiyi wanka."
Fatu ta mike tana kunkuni, ta wuce toilet. Bayan ta gama wanka, SONA ta gyara mata gashin kanta sosai, har ya fito yana kyalli. Fatu kuwa cike take da murna, don gashin ya burge ta.
SONA ta ci gaba da yabawa, tana cewa, "Gaskiya gashin nan yayi kyau sosai."
Ta dauko mata kayan da Momy ta bata jiya – wando jeans blue da T-shirt pink. Sanye kayan, Fatu ta yi kyau sosai, har ba za ka taba cewa ita ce ba. Fatu, duk da yarinta, gata da tsayi da kyan fata mai haske. Duk abin da ta sanya yana mata kyau.
SONA-ta-dauki-wayarta, ta-dauki-hotuna-masu kyau-na-Fatu.
Bayan sun fito parlour, Momy dake zaune tana lasar wayarta ta dago ta kallesu. Mamaki ya kamata, tana kallon Fatu, ta ce, "Wow, my daughter! Gaskiya kin yi kyau sosai."
Fatu ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi, ta ce, "Nagode sosai, Momy. Allah ya kara girma da arziki."
Mijin yarinya hausa novel last
Momy-ta murmusa, sannan ta-cigaba da kallon-wayarta. Fatu da SONA suka zauna suna hira.
A nan ne Saif ya shigo parlour da sallama. Duk suka amsa masa. Yana daga kai suka yi ido hudu da Fatu. Ya lumshe idanunsa cikin dan lokaci, ganin irin kyan da Fatu ta yi har ya kasa boye mamakinsa.