Aymana Hausa Romantic Novel

Aymana Hausa Romantic Novel

Our today posted book Aymana hausa romantic novel is an emotional and engaging story that explores themes of love, sacrifice, and the unpredictability of life. The story weaves a powerful tale of a mother's undying love and her heart-wrenching sacrifice during childbirth, leading to a hidden secret that lingers for decades.


The novel is rich with cultural details and deep emotions, showcasing family bonds, trust, and forgiveness in the face of life’s trials. The characters are well-developed, especially Ammy, whose strength and compassion form the core of the story.


What makes Aymana hausa romantic novel stand out is its ability to connect readers to real-life struggles while delivering an unexpected twist that leaves a lasting impact. It’s a perfect read for those who enjoy family-centered stories with a touch of romance and suspense.

English Version

Aymana hausa romantic novel part 1

Twenty-six years ago, at the time of Sadeeq and Mustapha's birth.

One day, on the day I went into labor in Bauchi town, I suffered intense pain, but there was neither delivery nor any sign of it, as if the baby was refusing to come out. Because of this, I was taken to the hospital's maternity ward.

At the same time I was brought in, there were other pregnant women who had also been taken to the labor room. I can say that I gave birth almost alongside one of the women there. Just one look at her and it was clear she wasn’t from a poor family, judging by the quality of her clothing.

By God’s will, I gave birth to twins, both boys. The other woman gave birth to a single baby boy.

That woman kept looking at my twins lying beside me, tears streaming down her face, though I didn’t understand why. I saw her pacing restlessly. This caught my attention, and I glanced around the room to find that all the nurses were focused on another woman in labor, whose condition appeared pitiable.

At that moment, no one around us had been told I had given birth. The woman approached me and then informed me that one of my twins had passed away and returned to his Creator.

I was deeply distressed because the love between a mother and her child is immense.

Aymana hausa romantic novel
Aymana hausa romantic novel 1

The woman spoke to me, saying, “Dear sister, my newborn’s life is in great danger. That’s why I’m begging you, for the sake of God, to save his life before something terrible happens. One look at you, and I felt you are trustworthy. My heart accepted you. I am begging you, please, let us exchange our children—give me your baby who has passed away, and I will give you my son.”

I looked at her closely because she was crying bitterly and pleading. My heart broke for her, and compassion overtook me. As if under a spell, I didn’t argue. Instead, I took my dead child, prayed for him, and quickly handed him to her. We agreed she wouldn’t mistreat my baby’s body, and I vowed to care for her child until he turned thirty, as she requested.

Before leaving, she told me to name the boy Abubakar Sadeeq. Just as she was about to say more about herself, we saw a nurse approaching us. The nurse, smiling, took the baby from the woman and said, “Let me take him to your mother outside. She’s been disturbing everyone, demanding her grandchild by the window.”

The woman broke into tears, saying, “My child has now gone to my sister.” The grief on her face was clear. She held my hand, then left the room, repeatedly looking back at her crying child.

I took the baby, Abubakar Sadeeq, and embraced him, feeling pity and love for him in that moment.

Aymana hausa romantic novel part 2 

Returning Home

After a short while, I was discharged from the hospital and returned home. When I told Abba what had happened, he scolded me harshly for making such a decision without consulting anyone. Eventually, he accepted the situation, and we agreed to keep it a secret between us.

The surprising part was that Abubakar Sadeeq refused to breastfeed, unlike his twin. Whenever we tried to force him, he would cry uncontrollably. So, we decided to give him goat’s milk, and by God’s grace, he drank it with ease.

On the naming day, we named the twins Mustapha and Abubakar Sadeeq.

The Hidden Secret

“This is the brief story of the secret we’ve kept hidden for so long, believing there was still time to share it,” Ammy said, bursting into fresh tears as if everything had just happened now.

Sadeeq, who was lying close to Ammy, began to tremble violently as though having a seizure. Ammy embraced him tightly, fresh tears streaming as she pitied the situation he was now in.

Aymana hausa romantic novel
Aymana hausa romantic novel 2

Everyone in the room was in awe of God’s mysteries, realizing that life truly has no guarantees.

Aymana, on the other hand, couldn’t process her emotions as she watched Abubakar Sadeeq in his current state. She wanted to comfort him but couldn’t bring herself to do so out of shyness in front of her parents. Salifa let out a heavy sigh as she continued watching Sadeeq, who remained in Ammy’s embrace.

Everyone in the room felt deep sympathy for the family. Haydar and Musty helped Abubakar Sadeeq lie down on a three-seater couch in the sitting room, with his head resting on Ammy’s lap, as though trying to bury himself in her.

For a long while, no one spoke. Eventually, Abba broke the silence, saying sternly, “You may all leave now. But I swear, if this story leaks out of this house, there will be consequences. Do you all understand?”

They all nodded and replied, “Insha Allah.”

Just as they were about to leave, Anty knelt on the floor, grabbing Baba’s feet and crying regretfully over the harm she and Aymana had caused him.

Hausa Version

Aymana hausa romantic novel part 1

Shekaru ashirin da shida da suka wuce wanda lokacin yayi dai-dai da haihuwar sadeeq da kuma mustapha.

Wata rana, ranar dana tashi da nakudar haihuwa a cikin garin bauchi, nasha baƙar wahala sosai amma kuma shiru babu haihuwa babu alamarta kamar an shuka dusa, wannan dalilin yasa aka wuce dani asibiti zuwa ɗakin masu nakuda!

A dai-dai lokacin da aka shigo dani akwai wasu matan masu juna biyu da suma aka kawo su dakin naƙudar! wanda zan iya cewa kusan a tare muka haihu tareda wata daya daga cikin wannan matan dake cikin dakin haihuwar, kallo daya idan kayi mata zaka fuskanci cewa ba daga gidan ƙananan mutane wannan mace ta fito ba, saboda ko daga yanayin tufafin dake jikinta!

Ni Ubangiji yasa na haifi twins ne wato tagwaye a lokacin kuma duka maza! ita kuma sai ta haifi guda daya wanda ya kasance namiji ta haifa! 

so sai wannan mata ke kallon tagwayen nawa wanda suke kwance, yayinda idanunta ke zubar da hawaye wanda ban san na menene ba! gani nayi tana juye-juye! wanda hakan yasa na soma kallon cikin É—akin haihuwar da gaba-daya malaman asibiti (nurses) din dake cikin dakin hankalinsu ya koma kan wata baiwar Allah dake cikin É—akin abin dai akwai abin tausayi.

A wannan lokaci ba'a sanarwa kowa waÉ—anda muke tare dasu cewa mun sauka ba! matsowa tayi zuwa kusa dani inda a sannan ta ankarar dani cewa daya daga cikin tagwayen dana haifa ya koma ga ubangijinsa!

Sosai hankalina ya tashi saboda irin soyayyar dake tsakanin É—a da mahaifiya ba karamin abu bane!

"Yake wannan baiwar Allah rayuwar wannan jaririri sabon haihuwa nawa tana cikin gagarumin hadari! wanda wannan dalilin ne yasa nake so ki yiwa allah kiyi ceton rai kafin hankali ya kawo kanmu! kallo ɗaya dana yi maki naji zuciyata ta aminta da cewa kedin mai amana ce kuma naji na aminta dake hakan yasa nake rokonki dan allah ga jaririna muyi musanye da naki wanda ya koma ni kuma sai na karɓi naki!"

Aymana hausa romantic novel part 2

Duban matar nayi da kyau saboda yadda take ta faman kuka tana rokona abin yayi nisa! nan da nan naji zuciyata ta karaya kuma tausayinta ya kama ni! kamar wacce ake sarrafawa banyi wata jayayya ba se ma daukan jaririn nawa wanda ya koma nayi masa addu'oi cikin hanzari na mika mata shi sannan da yarjejeniyar cewa kada ta wulakanta mini gawar É—ana, haka nima ta bangarena nayi mata alkawari insha-allah zan kula mata da É—anta har lokacin da zai cika shekara talatin 30 kamar yadda ta nema.

Sannan sai na faÉ—a masa a inda zai samu mahaifiyarsa take! "kisa sanya masa suna ABUBUKAR SADEEQ" har ta bude baki da nufin zata sake fada min ita wacece sai muka hango wata malamar asibiti ta doso inda muke, wannan dalili yasa mu shan jinin-jikinmu muka tsaya muna kallonta!

Ajiyar zuciya mai nauyi muka sauke saboda ganin ta karbi jaririn dake hannun wannan mata fuskarta cike da murmushi sannan tace "bari na kaiwa mahaifiyarki dake waje domin gaba-daya ta damu mutane da surutu ina jinta ta bakin window wai ita a kawo mata jikanta!"

Nan wannan mata ta fashe da kuka sosai tace" yaron nawa ya koma yar uwa" sosai jimami ya bayyana fuskarta inda ta kamo hannunta suka fice daga cikin dakin haihuwar matar nata faman waiwaye tana kallon yaronta dake ta faman tsala kuka abin tausayi!

É—aukan wannan yaron nata nayi wato Abubakar sadeeq na rungume inajin tausayi tareda jin kaunarsa tana ratsani a wannnan yanayi! 

Aymana hausa romantic novel last 

Bayan wani ƙaramin lokaci aka sallameni daga asibiti muka dawo gida! a lokacin dana faɗawa abba, faɗa sosai yayi min saboda abinda na aikata ba tareda neman shawarar kowa ba! inda daga bisani kuma sai shima ya hakura muka rufe wannan sirri a tsakaninmu ba tareda kowa ya sani ba! abin mamakin dake faruwa kuma munyi-munyi da Abubakar sadeeq ya karɓi nono, kamar dayan amma fir yaki bude bakinsa ballema ya amsa! idan kuma_muka matsa_masa sai_yasha sai_ya fashe_da kuka_sosai! wanda wannan dalilin yasa muka yanke shawarar bashi nonon akuya kuma alhamdulillah cikin taimakon Allah sosai yake shan abinsa! ranar_suna data zagayo_muka raɗa_masu suna_wato MUSTAPHA_DA ABUBAKAR_SADEEQ!!

"Wannan shine takaitaccen labari gameda sirrin dake boye tsawon lokaci ba tareda mun bayyana ba saboda ina ganin kamar da sauran lokaci!"

ammy ta karashe wannan maganar tata tana mai sake fashewa da kuka sosai saboda gani take tamkar a yanzu ne komai yake faruwa!

Sadeeq kuwa dake jikin ammy wata irin rawa sosai da sosai jikinsa ya dauka kamar wanda keda ciwon farfadiya! rungumeshi ammy tayi tana jin wani sabon kukan na sake bijiro mata cike da tsantsar tausayin sadeeq na halin da zai shiga!

Kowa dake cikin wannan falon na jinjina lamari irin na ubangiji! lallai wannan duniya ba'a bakin komai take ba!

Aymana kuwa take ta nemi damuwarta ta rasa saboda ganin yanayin da Abubakar sadeeq ke ciki yanzun-nan amma kuma ba zata iya yi masa komai ba saboda kunyar yin hakan da take ji cikin mahaifanta! Salifa kuwa a lokacin da ammy ta karasa wannan bayani nata saida ta sauke nannauyan ajiyar zuciya mai karfin gaske tana mai cigaba da kallon sadeeq dake rungume a jikin ammy!

kowa dake wannan wurin sai da ya tausaya masu kwarai da gaske! Haydar da Musty ne suka taimakawa Abubakar sadeeq ya kwanta akan doguwar kujera ta 3 _seater wadda ke cikin palon kansa na kan cinyar ammy tamkar ya shige jikinta!

Aymana hausa romantic novel
Aymana hausa romantic novel last 

An ɗauki lokaci mai tsayin gaske babu wanda ya cewa wani ƙala har sai da hankulansu suka gama dawowa jukkunansu sannan Abba yace "zaku iya tafiya sannan kuma wallahi kar koda wasa kar muji kuma kar mu gani cewa wannan labarin ya fita wani wuri ina fatan kun fahimta??"

Duka suka gyada kai suka yi da fadin "insha allah" har zasu mike, sai anty ta durkushe a ƙasa ta kamo kafar baba dake zaune kan kujerar 2 seater tareda tana sakin kuka na nadama akan abubuwan data aikata masa shi da AYMANA.

Previous Post Next Post