Abadan Hausa Novel

Abadan hausa novel 

Abadan hausa novel is an emotionally charged story that beautifully captures the complexities of love, jealousy, and reconciliation in relationships. The narrative revolves around Maryam and Abdallah, whose relationship is tested by misunderstandings and emotional turmoil.

The Abadan hausa novel strength lies in its vivid descriptions and intense dialogues, which bring the characters' emotions to life. Maryam's vulnerability and Abdallah's realization of their deep connection evoke both sympathy and admiration. The writer masterfully portrays the push and pull of love, weaving in cultural nuances that resonate with the Hausa-speaking audience.

The Abadan novel's pacing is engaging, with moments of tension balanced by heartfelt resolutions. Themes like loyalty, communication, and self-discovery are explored, making it a relatable and impactful read.

However, some parts of the narrative could benefit from tighter editing to enhance clarity and flow. Despite this, Abadan stands out as a captivating tale of enduring love and emotional growth.

This novel is a must-read for fans of romantic dramas that delve deep into the human heart.

Abadan hausa novel part 1

Tace cikin wata irin murya mai kauri cike da tashin hankali.

''jeka- jeka nace, ka tafi tunda ka fadamin abinda kake so, lallai saƙonka ya isa inda ya kamata ya isa, ''tayi maganar cikin ɓacin rai da canzawar kalar ƙwayoyin idanuwanta.

Ya sake matso ta yana cewa ''to kema me nayi don Allah maryam, ina cewa ke kika bayar da damar da zan ƙaro wannan auren-ko. Tunda na baki zaɓi na ganin koda ƙaramin canji kafin dawowata sai dai gashi har naje na dawo amma banga wani canji ba, haka yana nufin abdallah jeka auri Ero ko?''

Idanuwanta cikin nashi tana kallonshi kuka take neman yi sai dai ta kasa.

''Dama kana sonta abdallah na dade da fahimtar hakan, to menene don ka aureta, shin hakan na nufin ƙarewar numfashin maryam da tsayawar rayuwarta a duniya?''ya fuskanci ta fara ficewa daga hayyyacinta, saboda haka sai ya miƙe yana saɓa babbar rigarsa da nufin ficewa tareda faɗin ''Allah ya kyauta, Allah ya baki hakuri kinji, sai mun dawo''

Abadan hausa novel
Abadan hausa novel 1

tsintarta_kawai_yayi a gabansa_tana tura kofar_gamida jingina_jikinta_da_kofar, hawayen_da_bata_so_su_fita_sune_suka_fara zubowa_kan_kuncinta.

Nan fa ta jingina kanta da bango kana ta saki wani sabon kuka, muryarta a shaƙe cikin rashin sanin meke fitowa daga cikin bakinta tace. ''idan kana son tafiya ka tafi, amma babu inda zaka je abdallah har sai ka tsaga ƙirjina ka cire zuciyata sannan ka tafi da ita, wannan wane irin sone? wannan wane irin horo ne, nagaji nagaji abdallah da irin wannan horo, meyasa kake yiwa zuciyata irin wannan hukunci, meyasa ka kasa gane cewa zuciyar maryam cike take da so da ƙaunarka, shin kasan irin matsayinka a cikinta kuwa?''

Abdallah kasa tsayuwa yayi har saida ya ƙarasa inda take tsaye sannan yasa hannayen shi duka biyun ya dafe kofar shima ya yiwa maryam rumfa, numfashinsa na fita da sauri-sauri, wani_irin samfurin_farinciki wanda_bai_yi_tsammani_akwai_irinsa a_cikin wannan_duniya_ba, shine_ya_mamaye_ilahirin jini_da_tsoka_harma_da_zuciyarsa_yace.

Abadan hausa novel part 2 

''abdallah ya dade da sanin cewa ya dasa gagarumin ƙauna cikin zuciyar maryamunsa, irin kaunar da ko masoya mutuwa suka yi bata barin zuciya, abu ɗaya abdallah yake da muradin yaji daga bakin ɗiya mace ƙwaya ɗaya tal a duniya shine NIMA_INA_SONKA ABDALLAH_KWATANKWACIN_YADDA_KAKE SONA K......*

NIMA_INA_SONKA_ABDALLAH_FIYE DA YADDA_KAKE_SONA, FIYE_DA_YADDA_KAKE TSAMMANI_KO_HASASHE_CIKIN ZUCIYARKA, haka ta faɗa cike da tare numfashinsa ba tareda ya kammala fadar abinda ke bakinsa ba, kasa daurewa yayi saida yaji duminta a jikinsa, saida yaji hucin numfashinsu na haɗuwa waje guda, gaba-daya ta narke a ƙirjin nasa tana sake cusa kanta. tsayuwa ce ta gagaresu, hakan yasa ya jata gefan gado suka zauna.

Abadan hausa novel
Abadan hausa novel 2

A hankali kukan ya soma tsagaitawa, sai ta janye jikinta sannan ta dubeshi da kyawawan idanunta da a yau suka sauya kala.
''abdallah Mero fa?''yayinda ta tambayeshi tana ɗan jan majina a hankali, dariya ce taso ta ƙwace masa amma duk da haka saida murmushi cike da annuri ya wadaci fuskarsa, nan ta tsareshi da idanu sosai da alamu dai wani sabon kishi ne ya bude fagenshi cikin zuciyarta, saida ya lakuce mata hanci sannan yace ''gaki nan, ai kece MERO_NA kuma kece MAIRAMU haka nan kuma kece DIYANA duka''

kunya ta kamata, wai dama haka abdallah ya ƙware wajen buga Game ne?bata yi tsammani a fili tayi maganar ba sai da taji yace. ''yes abdallah kyakkyawan ɗan-wasa ne, sanna kuma me nasara ne, yau ma gashi nayi nasara, Now! the game is over today ''shigewa jikinsa ta ƙara yi yana mai boye kanta a ƙirjinsa, tareda wani kyakkyawan murmushi kwance kan fuskarta, hannunsa duka ya sanya ya ƙara riƙeta sosai yana magana cikin dariya-dariya.

Abadan hausa novel last part 

''ashe dama haka kike da mugun kishi mero?amma fa kin ɗan ji kunya kadan, kishi da 'yar-ƙauye? ya akai kika aminta da cewa zan iya duban wata mace ma balle a kai ga batun soyayya, macen ma kuma Mero, kin manta dasu Abida, Salma, Saddiqa, Zubaida_da sauransu, basu_isheni_koda_kallo_ba_sai mero.

Kuma fa hakane, amma ya akayi ta manta da hakan, kishi duk ya rufe mata idanu, ba shakka gaskiya taji kunya, haka dai ta sake duƙunƙunewa. ''ta bangare guda kin burgeni sosai kuma haka nan kin gama biyana ya fada yana kamo kunnenta so yake maganar ta koma ta sirri a tsakaninsu da meronsa.

''yadda kika nuna kina kishina, yasa na tabbatar da cewa ni ba ƙaramin dan gata bane''

Tayi far da idanu duk da baya ganinta, can ƙasa-ƙasa da murya tace ''amma wajen daurin auren waye zaku a ni'ima, kuma waye zai zauna a ɓangarena nane nada'' nan_ya_amsa "daurin_auren_Mero, kuma_fa Meron_ƙauye, kuma_acan_ni'ima_sannan bangarena_na_da anan_zata_tare_nata_ne''

Sai ta miƙe, hawayenta na ƙoƙarin dawowa
''abdallah ya zakamin haka, sai da ƙalbina ya gama kamuwa da ƙaunarka sannan kace zaka ƙara aure, ba zan iya ba ni ba zan iya sharing wata da kai ba, wallahi ina kishinka fiye da yadda kake tsammani ''ta fada tana girgiza kai tareda yunƙurin sauka daga kan gadon, wayyo wani sabon farinciki ya ƙara kamashi kamar yayi adungure saboda jindaɗi, tuni ya riƙota yana girgiza kai shima.

''Alhamdulilah Allah nagode maka daka bani mai kishina, nasan ba komai ne ya kawo hakan ba face tsatsar ƙauna, ki kwantar da hankalinki madam, Mero zata auri Labaran ne nata na can ƙauye, na ɗaukota ne ta zauna nan ne tareda mami domin ta dinga taya ta yan aikace-aikace da kula da gida, tun da mamin tace tana son zama damu amma kuma ta rantse gidanmu zamu tafi.

Abadan hausa novel
Abadan hausa novel last 

Ba zata zauna tareda mu ba gudun kar ta shiga haƙƙinmu, Labaran kuma na bashi aiki cikin kamfanonina na nan kano, kuma banyi ƙarya ba _A yau ni angon Mero nake amma Merota domin na tabbatar yau ba zaki tsallake_tarkona ba sai kin bude min da bakinki ƙaunar da kike binneta cikin zuciyarki bayan kuma akwai mamallakinta, shine dalilin da yasa nayi miki adon angwayen domin nima ango ne, haka zalika kuma yau ba zaki sake kwana a wajen mami ba sai cikin gidanmu, gidan dana soma ginashi tun daga ranar dana fara tozali dake a rayuwata, domin ke dama na ginashi shine dalilin da yasa a china na muku shigar sauri na zabi gadon amarcinmu saboda ni kadai nasan kalar wanda zai fi dacewa da wannan gidan, a lokacin mami tana ganin kamar na miki shishshigi amma bata san tanadi na yiwa kaina ba.
Previous Post Next Post