Yarima Ashman complete part 1

"Yarima Ashman" is a fascinating tale set in the 14th century in a kingdom ruled by the powerful Sarki Mulgaru. Known for his conquests and vast empire, Sarki Mulgaru's reign is marked by constant warfare and reliance on sorcery. Despite his many wives and concubines, he lacks an heir, which deeply troubles him.

One day, a mysterious man named Nafurabu arrives, claiming to have a remedy for the king's problem. After much effort and various attempts, Nafurabu's potion succeeds, and one of the king's concubines, Safara'u, becomes pregnant. She gives birth to a handsome and strong boy named Yarima Ashman.

Yarima Ashman grows up to be a beloved and skilled warrior, admired for his bravery and compassion. He learns the art of sword fighting and leadership, preparing himself to inherit his father's throne. His fame spreads across the land, and many princesses wish to marry him. The people of Zagarisa and surrounding regions look up to him, hoping he will become their future king.

Overall, "Yarima Ashman" is an intriguing story about power, legacy, and the making of a great leader. The characters are well-developed, and the plot is engaging, making it a highly enjoyable read.

A can ƙasashen yamma a cikin ƙarni na goma sha huɗu anyi wani gawurtaccen sarki mai suna Sarki Mulgaru wanda yake zuba sha'anin mulkinsa a babban garin Zagarisa, shi dai wannan sarkin yana da masaurata faffaɗa domin kuwa masarautarsa ta haɗa dauloli ne da yawa waɗanda ya ciyo saboda yaƙe yaƙen daya riƙa yi yana samun nasarori. A lokacin wannan sarki, zamani ne na yaƙe yaƙe haka kuma wannan ƙarni na goma sha huɗu lokaci ne da ake tsafi sosai, a saboda haka daular wannan sarkin ta haɗa matsafa da yawa waɗanda ake neman sa'a a wurin su ta fitar yaƙi ko kuma sha'anin mulki da sauran su. Wannan mashahurin Sarki wato Sarki Mulgaru yana da mataye na aure da bayi bila adadin waɗanda shi kansa bai san yawansu ba.

Sarki Mulgaru ya tara dauloli a ƙarƙashin mulkinsa ga dukiya sai dai babu magajin duka wannan abubuwan daya tara, ba a ko taɓa yin ɓari a tsakanin matansa ba, wannan abun yana damun sarkin nan kwarai da aniya. Sarki Mulgaru ya nemi magunguna kala-kala, haka kuma anyi mai duba anyi bugun ƙasar amma duk ba akai gaci ba. A duk lokacin daya ji labarin wani mai bada magani sai ya aika komai nisan wurin azo masa dashi, haka suma masu bada magani suna yawan kawo ziyara zuwa masarautar sarki mulgaru domin gwada sa'ar su ko za'a dace. Haka dai shekaru suka miƙa sarki mulgaru kasancewarsa mayaƙi, sai ya cigaba da fita fagen fama yana ciwo ƙasashen kan iyaka yana shigowa dasu masarautarsa.

Ana nan wata rana sai wani koɗaɗɗen mutum yazo garin bakhmut wani gari dake ƙarƙashin mulkin sarki Mulgaru. Sarkin bakhmut mai suna Sarki Barazasu na hannun daman Sarki Mulgaru ne. Wannan koɗaɗɗen mutumin yana tafiya ne a cikin tsummokara kuma daga shi sai ƴar ƙaramar jakarsa ta fata irin ta magori wacce masu magani suke yawo da ita. Wannan koɗaɗɗen mutumin yana yawo wuri wuri yana kiran wanene zai kaini gaban sarki mulgaru na bashi maganin haihuwa?. Haka wannan baƙo yake fitowa kullum daga fitowar rana zuwa faɗuwarta sannan ya koma bayan gari ya kwana, idan kuma gari ya waye rana ta fito haka zai sake fitowa ya cigaba da wannan zagayen nasa ba tare da gajiyawa ba. Kullum wannan mai bada maganin sai ya wuce ta fadar sarkin garin. Bayan kamar mako biyu  da fara fitowar wannan baƙon wata rana da safe ya fito ya fara zagayen daya saba yi sai yazo wucewa ta fadar garin, ko da sarki ya jiyo shi sai yasa aka tashi wani bafade yaje ya shigo dashi.

Yarima Ashman part 2 

Bayan an gurfanar da wannan koɗaɗɗen mutumin sai sarki ya sa aka tambayeshi sunan sa da kuma inda ya fito. Wannan koɗaɗɗen mutumin ya nisa yace;

"Sunana Nafurabu ɗan mai ganye kuma ni mutumin ƙasar sham ne, ina bi nahiya nahiya domin bada taimakon magani ne, kuma na samu labarin sarki mulgaru ne wurin waɗansu fatake da muka ci zango dasu a tsibirin gararuza. 

Koda sarki yaji haka sai ya jinjina kai saboda haƙiƙa yasan mutanen sham sun shahara akan sirrikan magunguna iri-iri saboda haka washe gari yasa wasu amintattun fadawansa suka haɗa dawaki tare da Nafurabu ɗan mai ganye aka yiwa masarautar sarki mulgaru tsinke. Da yake tsakanin birnin bakhmut zuwa babbar masarautar sarki mulgaru akwai nisan tafiya mai tsawo, wannan ayarin basu isa ba sai bayan kwana huɗu wacce ta haɗa da cin zango da hutawa idan dawaki sun gaji. Bayan sun sauka an basu masauki sun huta daga nan sai aka yi musu iso gaban sarki Mulgaru anan suka gabatar da kansu a matsayin ƴan aiken sarki Barazasu suka shaidawa sarkin cewa suna tare da mai magani daga ƙasar sham, haka suka gabatar masa da nafurabu. 

Bayan an gabatar da nafurabu sai ya matso gaba ya saka hannunsa cikin jakarsa ta fata ya ɗauko wani ƙullin magani ya miƙawa sarkin gida inda yayi bayanin cewa a shiga dashi gida duk iyalin sarki da saɗakan cikinsu a basu a ruwa su sha za'a samu shigar ciki. Ai kuwa Allah cikin ikonSa bayan wasu ƴan watanni sai ciki ya ɓulla a jikin wata baiwar sarki mai suna safara'u. Sarki Mulgaru yayi murna kwarai da gaske ya kawo dukiya mai yawa ya bawa nafurabu, aka haɗa masa sutura irin su raƙuma, dawaki, alkyabbu, zannuwa, kilisai, kyankyandi da sauran sha tara ta arziki ya tafi yana murna. Bayan wata tara wannan baiwar ta sarki ta haifo zankaɗeɗen yaro kyakkyawan gaske bayan sati ɗaya akayi gagarumin bikin suna yaro yaci suna YARIMA ASHMAN! 

Yarima Ashman last part 

Yarima Ashman tun yana yaro ƙarami ya kasance mai tsananin farin jinin gaske haka kuma tun yana ƙaramin yaro ya nuna sha'awar koyon faɗan takobi wanda ganin haka ne sarki murgalu yasa wasu amintattun mutum biyu cikin mayaƙansa suka fara koya masa faɗan takobi da cilli da mashi. Daga nan bayan yarima ya sake wayo ya kai misalin shekaru sha biyu aka fara koya masa sha'anin mulki da alƙalanci. Waɗannan ne dalilan da suka sa ya shahara a fagen fama da kuma ɓangaren sha'anin fada. Sunan yarima ya kewaye ƙasashen yamma a lokacin daya fara fita yaƙi saboda irin dakarun da yake bajewa a shiga ɗaya. Yarima Ashman sadauki ne na gaske mai tsananin ƙarfin dantse haka kuma mai tausayawa talakawansa a duk faɗin ƙasar zagarisa da garuruwan da suke kewaye da ita da mahaifinsa yake mulka. Saboda irin farin jininsa, gwarzantakarsa da kuma tsantsar kyawunsa yasa gimbiyoyi daga ko ina a faɗin ƙasashe suke begensa suna fatan ya auresu. Haka kuma wannan farin jini nasa bai gushe ba anan cikin zagarisa da kewayenta kowa na ƙasar fatansa ko fatansu idan mahaifinsa Sarki Mulgaru ya bada baya to ya zamana cewa yarima ashman shine sarkin gobe, kamar yadda kirarinsa ya game ko ina idan ya shiga sai dai aji ana faɗin;

"Gaka yarima ɗan sarki gaka sadauki, gaka fari kyakkyawa, gadon zinaren Zagarisa naka ne a gobe kowa yayi mubaya'a. 

Sarki Mulgaru kuwa mahaifin yarima ashman ya gama sakankancewa da al'amarin jajirtaccen jarumin sadaukin ɗansa wanda iya sunan sa idan aka ambata abokan gaba kan shiga taitaiyinsu...