Tame gari section 1
A short review for the novel
"Tame Gari" is an engaging story featuring Dije, Hafsi, and their friends. Dije, nicknamed "tame gari," is upset with Hafsi for spilling flour and calling her names. Despite her anger, Dije helps Hafsi avoid punishment at home by grinding more flour for her, showing empathy.
The story takes a humorous turn when two wealthy young men, Habeeb and Nasir, arrive in town. Dije, misunderstanding their intentions, throws a stone that injures Habeeb. The men, thinking she's a supernatural being, panic. Eventually, Dije forgives them after they apologize, emphasizing respect.
"Tame Gari" blends humor and cultural insights, teaching valuable lessons about empathy, forgiveness, and understanding others. The characters are well-developed, and the story is entertaining and thought-provoking.
Wallahi Allah ba zan haƙura ba sai an biyani nikana, kin isama na rantse da Allah kuma in kika je kika fadawa innata wallahi sai nayi maganinki cewar dije dake kara tattake garin tuwon wanda ke zube a kasa, kuma an barar da garin duk ranar da kika ƙara kirana Dijangala tame gari tuwon gidanku ma zanje na zubar ba garin ba.
Su Shatu dake gefe guda suna kallon wannan al'amari ba damar suyi magana domin suna tsoron dije (tame gari) dan haka ba suyi magana ba, ko suce yi hakuri amma basu faɗa ba, ita kuwa hafsi sai rizgar kukanta take yi saboda tasan yau idan taje gida sai an dake ta, domin delu sai ta mata duka kuma sai ta sata nemo wani garin ai kuwa tana tuna hakan sai ta ƙara bare baki ta cigaba da kuka. Dije ce ta kalleta sannan tace wai ke me nayi miki da kike ta faman wannan kukan dan ma kinci sa'a ban faffasa miki ƙwaryar niƙan ba.
Shatu ce ta matso kusa da ita sannan tace kin san dai delu dukanta zata yi wallahi idan taje gida kinsan halinta dai ba imani ta cika ba.
shiru dije tayi tana tunani na ɗan wani lokaci sannan kuma tace to kinga ke kika janyowa kanki tunda kika tsokane ni amma yi hakuri kinji tashi muje nasan yadda zamu yi amma fa sai kin bani hakuri saboda tsokanar da kika min tame gari. Da sauri hafsi ta cewa Dije yi hakuri dan Allah, to shikenan ya sunana.
Hafsi tace "Anti dije"
wani sabon farinciki ne ya mamaye zuciyarta domin tana masifar son irin sunan nan na 'yan birni wato Anti dije saboda haka da sauri ta cewa hafsi tashi muje gidan mu na baki wata dawar ki kara kaiwa niƙa.
Cikin sauri hafsi ta mike saboda tasan ko yanzu takai nikan gida sai taci duka dan ta daɗe, da sauri suka nufi gidansu dije koda suka ƙarasa dije bata ɓoyewa mahaifiyarta saudi komai ba ai kuwa ta basu wata dawa suka kai nika, har gida suka raka hafsi ai kuwa delu tayi ta jaraba, sai dai su Dije sun samu rabon zagi amma bata daki hafsi ba.
//////////
Wata mota ce kirar Honda_Accord (LC) ta shigo garin Gawo kasancewar hanyar bata da kyau ga kuma da alama wanda ke cikin wannan motar ya sha wahalar tafiya, mutane biyu ne a ciki, samari kyawawa domin daka gansu kaga yan hutu waɗanda kuɗi suka zauna, tuki yake yi tamkar wanda aka yiwa dole kafin ya ya kalli dayan yace masa cikin kasalalliyar murya Habeeb wallahi nagaji da yawa na matsu mu ƙarasa cikin garin_nan mu yada zango kan gadon tsohon_nan.
Tame gari section 2
Habeeb yayi murmushi sannan yace kai ma kenan balle kuma ni dana sha tafiya gashi yauma saboda inason ganin dattijon nan me ran karfen yasa na biyoka.
Hmm kai dai bari ai tsohon nan inaga rokon Allah yake yi mana shiyasa bama daukar lokaci mai tsayi ba tareda mun ganshi ba, ko daddy ma fa kullum maganarsa baba malam kusan koda yaushe yana kan hanya, to Allah yaja da rai, Ameen ya Allah.
kam bala'i ta fada yayinda taga motar na kokarin wucewa alamarma cewa na ciki bai san me ya aikata ba, giginyar dake hannunta ta saita glass ɗin motar ta jefa ai kuwa cikin sa'a ta daki glass din gefen driver sannan ta hada da bakin Habeeb wanda ya gama magana yanzu.
wani uban birki ya taka tareda kiran sunan Allah saboda ganin abinda ya faru kamar a mafarki, dubansa ya kai wajen da habeeb yake, nan da nan bakinsa ya wani kumbura yadda kasan bakin jaɓa nan kuma jini ya soma zuba, kamar yayi dariya amma ba dama dole ya ambaci subhanallahi ya soma ƙoƙarin bude motar ya fito domin ya zagaya bangaren habeeb saboda har yanzu bai san ta inda abin ya faru ba.
tsaye take ta wani riƙe ƙugu da hannu ɗaya, dayan hannunta kuma wata giginyar ce wacce tafi ta farko girma, kwalliyar dake fuskarta kawai ya gani yaji gabansa na faɗuwa saboda wallahi babu tantama wannan aljana ce.
wa 'innahu sulaimanu wa 'innahu bismillahir rahmanir raheem ya fara karantawa cike da tsoro saboda shi a tunaninsa dai babu tantama wannan aljana ce duba da yanayinta gata fara sai kace zabiya ga kuma wani uban bakin kwalli wanda ta shafa a leɓen nan, ga jagira ta hade da kwallin da taja hawayen masoyi.
jikinsa ne ya hau tsuma yan karkarwa inda ita kuma dije nan take ta fahimci me yake nufi ai kuwa harara ta cigaba da wurga masa, tana ta jujjuya idanu inda shi kuma hakan ke kara ɗimauta shi cikin karkarwa ya ƙarasa inda Habeeb yake, sannan ya sunkuyar da kansa kasa sabida nauyin da yayi masa sakamakon giginyar data bugi kansa ga haƙorinsa guda daya ya fita, haka zalika ga bakin ya kumbura yayi wani tsayi tamkar shantu cikin rawar jiki.
Nasir ya ƙarasa wajen da yake ya bude ƙofar motar yana karanta duk addu'ar da tazo bakinsa, dago kansa yayi ya kalleshi jin yana ta kwarara addu'a, nan fa ya fahimci cewa lallai gamo suka yi da wani abun tsoro saboda ya hango aljanar, da giginyarta ta Aljanu a hannu tana ta faman juya idanu, duk da yana jin jiri amma hakan bai hanashi ruɗewa ba. Haba shima ya soma ƙoƙarin fitowa daga cikin motar nan fa suka ƙanƙame juna shi da Nasir wanda har ya fara ƙwalla, saboda tsoro musamman duba da yanayin wajen babu komai sai bishiyoyi wanda bai san ko na menene ba amma dai yasan akwai bishiyar kuka kuma yasan anan gidan aljanu yake.
Tame gari last section
Cikin wata irin ƙatuwar murya da malƙwaya harshe dije tace ku bil'adama daga ina kuke?
haba wani fitsari ne ya kufcewa Naseer a wando shi kuwa habeeb ji yayi tamkar ya suma ko bakwa jine ina muku tambaya?
Cikin wata rawar murya Nasir yace yi....yi..ha.k..uri.daga Abuja daga Abuja wallahi muka zo shine kuma aka ce dan kun zo daga birni ku takamin 'ya'yana da mota suna tsaka da yin wasansu wato saboda kun rainamu ko.
ah ah wlh ba...ba haka bane bamu sani ba wallahi ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba dan girman Allah kiyi hakuri kiyi mana afuwa wallahi bamu sani ba, to naji zan hakura amma da sharaɗin sai dai ku bar abin hawanku anan wajen ku tafi zaku je da ƙafarku ko kuma ni na kai ku da kaina.
ah ah wallahi mun_gode Habeeb da Nasir suka fada a tare, zamu ƙarasa tafiyar da kafar mu ina ke ina wahala damu.
haHaha hahaha
ta dinga dariya sannan tana yiwa kanta kirari tana cewa sai ni dije uwar aljanu, ku wuce amma ku sani bazan rabu daku ba saboda yadda kuka raunatamin 'ya'yana yanzu haka suna bangon duniya na gabas wajen me magani saboda haka kuma sai naje naga yadda jikinsu yake kafin nasan wane hukunci zanyi muku.
Ƙuuu cikin nasir yayi wani ƙara dan girman Allah dan girman Annabi kiyi hakuri, wallahi bamu san suna wajen bane, ina mu ina aikata irin wannan rashin hankali. To naji ku tashi ku tafi washe gari ku zo ku dauke motar amma ba yau ba, to toh mun yadda wallahi.
Sam Habeeb ya kasa tafiya da ƙafarsa yayinda Naseer ya kamashi da kyar ya saba a kafaɗarsa ya kama hanya ba ko waiwaye har da gudu bako waiwaye.
Tun da dije taga haka nan fa ta zube a wajen tana ta dariya har da hawaye a wannan yanayin su Shatu ƙawayenta suka ƙaraso suka sameta nan suka shiga tambayarta, ita kuwa taƙi fada musu abinda ya faru, ba damar su matsa mata ta danƙari mutum dan ƙarfi ne da ita, sai da tayi dariya ta isheta kafin daga bisani ta mike tace mu tafi, Hafsi ce tayi ƙoƙarin tambayarta ina gyadar da kika samo?
Ban sani ba, haka ta faɗa tana faman harararta ai kuwa tayi gum suka cigaba da tafiya duk lokacin data tuno yadda bakin Habeeb ya kumbura da kuma yadda taga dayan saurayin yayi fitsari a wando sai ta kuma kyalkyalewa da dariya su dai su hafsi nasu kallo amma ba damar su tambaya.