Tafita zakka hausa novel part 1

"Tafita Zakka" is an engaging story about a mischievous girl named Shafa'atu, set in the household of Ustaz Alaramma Isyaku Marafa, a respected Islamic scholar. Ustaz Isyaku is known for his large family, with four wives and forty-two children. The family is deeply rooted in religious teachings and education, but Shafa'atu stands out due to her troublesome nature.

From a young age, Shafa'atu is known for her pranks and disobedience. She often pretends to be ill to avoid attending Islamic school, only to join her peers in play later. Her mother, Anti Habiba, tries to discipline her, but Shafa'atu's defiant nature makes it challenging. Despite her behavior, she is the apple of her father's eye, and he hopes she will eventually settle down.

Shafa'atu's antics extend beyond the home, causing trouble in the neighborhood. Her reputation for fighting and throwing stones at others becomes well-known. Her family, particularly her older brothers, often have to pay for the damages she causes.

The story takes a turn when Shafa'atu reaches the age of fourteen and starts showing interest in boys. Her father, worried about her future, arranges her marriage to Murtala, hoping this will help her mature and settle down.

"Tafita Zakka" provides a humorous yet thought-provoking look at family dynamics, discipline, and the challenges of raising a strong-willed child. It highlights the efforts of a family to instill values and guide their children, even when faced with difficult personalities.

Ɗan adam mai wuyar gane hali..

Wannan wata magana ce ta malam bahaushe wacce take nuna ko bayyana tsantsar sifa da kuma halayya ta ɗan mutum. Halitta ta ɗan adam wata halitta ce mai ban mamaki, domin kuwa zamu ga uwa wato mahaifiya ta haifo ɗa ko ƴa cikin duniyar nan, kamarsu tamkar an tsaga kara, idan abin da aka haifar baiyo kama da uwar ba sai ya ɗauko sifar uba, wannan kama kenan ta sifa. Ita kuwa kamanceceniya a halayya aba ce wacce idan abin da aka haifa ya girma ya kai minzali za'a fi fahimtar ta. To kamar haka ne yake kasancewa da ko wane ɗan adam. Wani mahaifin ko mahaifiyar mutane ne da basu da magana sosai amma sai su haifo ɗa ko ƴa masu surutu kamar aku. Wasu mahaifan sukan zamo masu zafin rai amma abin mamaki sai su samu ɗa ko ƴa mai ɗan karen haƙuri..

*****

Gidan Ustaz Alaramma Isyaku Marafa, gida ne na malamai tun iyayensu da kakanni. Haka kuma matayensa ma da yake aure guda huɗu reras dukansu malamai ne daga uwargidan sa ta farkon su wato iya Zainabu ko kuma magajiya, har zuwa kan amarya wato anti Habiba. Ragowar matan sa Malama lami da Malama suwaiba cikon ta biyu da ta uku dukansu babu wacce bata bada karatu a duk ranar asabar da lahadi a nan makarantar dake masallacin gidan. Kasancewar masallacin gidan Ustaz Isyaku Marafa masallaci ne na Juma'a hakan ya baiwa makarantar masallacin damar yin fice a cikin makaranta tsararrakin ta dake cikin garin Marafa. Yara daga ko ina a faɗin garin na Marafa akan kawo su domin kwasar madarar ilimi a wurin malaman wannan fitacciyar makarantar.

Tafita zakka
Tafita zakka 1

Kamar yadda iyalan alaramma Isyaku suke malamai na gaske gida na tarbiyya to haka fa manyan yaran gidan suke wato manyan su maza da mata yayin da ƙananun cikinsu kuma ake fara ɗaura su akan wannan tafarki da zarar yaro ko yarinya sun kai shekara huɗu. Alaramma Isyaku Marafa mutum ne mai iyali da yawa domin kuwa a tsakanin matan sa huɗu na aure yana da ƴaƴa arba'in da biyu. Uwargidan sa na da ƴaƴa goma sha ɗaya, mai biye mata tana da ƴaƴa goma sha ɗaya ita ma, matarsa ta uku tana da ƴaƴa goma sha biyu sai amaryarsa cikon ta huɗu su tana da ƴaƴa takwas idan aka haɗa jimillar ƴaƴan wannan mashahurin malamin yana da ƴaƴa ɗai-ɗai har arba'in da biyu.

Tafita zakka novel part 2 

A cikin waɗannan ƴaƴa takwas na amarya anti habiba wacce Malam ya auro daga can damaturu a lokacin da yaje taron wa'azin ƙarshen shekara a shekarar miladiyya ta dubu biyu da biyar, babbar ƴarsa ta wurin amarya, yarinya mai suna shafa'atu an haife ta ne shekara ɗaya bayan Malam ya auro uwarta daga can damaturun. A shekarun haihuwa shafa'atu tana da shekaru goma sha takwas domin an haife tane a shekara ta dubu biyu da shida. Tun da shafa'atu ta taso ta fara takawa har tayi wayo a cikin gidansu  ta kuma fahimci ga fa yadda gidan nasu yake, sai ta fara ƙoƙarin farraƙewa wato ma'ana in dai yau za'a tashi da safiyar asabar ko lahadi waɗanda dama a waɗannan ranakun biyu ne ake shiga islamiyya tun da safe ƙarfe tara har biyar, tofa shafa'atu zata ƙirƙiro wata rashin lafiya da dole za'a barta cikin gida ba tare da taje makaranta ba sai dai kuma da zarar yamma tayi an taso daga makarantar kwatsam sai dai a tsinci shafa'atu a cikin yaran gidan ana wasan ƴanta da ita. 

Tafita zakka
Tafita zakka 2

Irin wannan ɗabi'artata ce tasa mahaifarta anti Habiba tsayawa akanta tsayin daka ko da tayi ƙaryar rashin lafiya tofa sai taje makaranta. Tun tana yarinya ƙanƙanuwa idan ana cikin wasa a tsakanin yara, kasancewar gidan malam gidane na mutane da yawa indai akaji yaro ko yarinya sun tsala ihu to babu amfanin duba meya faru domin kuwa shafa'atu ce ta mintsini wani kuma da tayi halin zata bar wurin ta ɓuya, ayi neman duniya baza a ganta ba. Saboda tsabar zafin hali, rashin iya magana da tsabar tsiwa irin ta shafa'atu, Malam da kansa yake zaunar da ita ya bata ruwan buta wai duk don a samu tayi sanyin hali amma abu yaci tura, gashi kuma abun ba'a ɓoye yake ba, a fili yake irin shaƙuwa da son da malam yake yiwa wannan ɗiya tasa shafa'atu. Duk yaro ko yarinyar dake gidan sukan yi sauka ne a shekaru goma ko sha ɗaya na haihuwa basa ɗara hakan amma ita kuwa shafa'atu gashi ta kai minzalin aure ko izu talatin bata haɗa ba. Ragowar darusa kuwa dama ba'a magana. 

A cikin unguwa kuwa tun tana ficiciyar ta ƴar shekara biyar zuwa goma babu irin jidalin da bata ɗaukowa kama daga faɗan da ake yi da ita wurin layin ɗiban ruwa ko kuma idan an taso daga makarantar boko. Shafa'atu idan akayi faɗa da ita kuma aka fi ƙarfinta a wannan karawar to ko shakka babu dutse take samu tabi mutum a baya har zuwa wurin data san babu nisa zuwa gidan su, mutum baiyi aune ba sai dai yaji tim! saukar dutse a kansa daga nan ita kuma ta ranta ana kare. Shafa'atu tasha fasawa yaran mutane kai wasunsu har ɗinki ake musu sai dai idan an kawo ƙara yayyenta ko shi Malam da kansa su biya kuɗin zuwa chemist.

Tafita zakka novel last part 

Inna Habiba mahaifiyarta tayi dukan tayi nasihar amma duk abinda zai shiga kunnen shafa'atu na dama to kuwa ficewa yake ta hagun. Wurin ayyukan gida irin su shara, wanke wanke da girki ba ƙaramin tashin hankali ake da shafa'atu ba kafin inna Habiba take tankwarata tayi, kuma a hakan ma tana aikin tana sakin habaici da ƙananan maganganu ga sauran ƴan matan da take aikin tare dasu. Mazajen gidansu babu irin jibgar da ba suyi wa shafa'atu ba akan ƙin dawowar ta gida da wuri idan an taso daga ta boko, bin ƙawaye zuwa wata unguwar ba tare data sanar a gida an bata izini ba ko kuma karatun littattafan soyayya. Duka waɗannan abubuwa sai dai labari a cikin gidan shehin malami Isyaku kafin samuwar shafa'atu kenan a cikin gidansa. Amma bayan samuwarta kuwa duk ire iren abubuwan da ada can sai dai labarin su a rediyo, to ra'ayal aini iyalan gidan suke ganin su a wurin shafa'atu.

Tafita zakka
Tafita zakka last 

Tun shafa'atu tana da shekaru sha huɗu ta fara yin samari wanda hakan ne ya tashi hankalin malam matuƙa, tana aji uku na ƙaramar sakandire wato jss3 yayi mata aure da saurayin ta Murtala yana mai fatan ta zauna lafiya ya huta da jidalin ta.