Surbajo hausa novel
"Surbajo" is a captivating Hausa novel that delves into the complexities of relationships, responsibilities, and societal expectations. The story revolves around Al'ameen, a dedicated soldier, and his wife, Aisha, whose differing attitudes towards life and responsibilities create a compelling narrative.
Plot Summary
The novel begins with Al'ameen preparing to leave for work early in the morning, only to find his wife, Aisha, still asleep despite his earlier warnings. The chaotic state of their home reflects Aisha's lack of interest in household duties. Al'ameen, frustrated but resigned, leaves money for Aisha before heading to the airport for his trip to Port Harcourt.
Aisha's disdain for household chores and her reliance on Al'ameen's financial support are evident throughout the story. She spends her days socializing with friends and neglecting her responsibilities. The narrative takes a turn when Al'ameen encounters a young girl named Aisha, who is in distress after losing money meant for food. Al'ameen's compassionate nature leads him to help her, showcasing his contrasting character to his wife's.
Themes
1. Responsibility and Duty: The novel highlights the importance of responsibility and duty, both in personal relationships and societal roles.
2. Compassion and Kindness: Al'ameen's actions towards the young girl emphasize the value of compassion and helping those in need.
3. Societal Expectations: The story explores the expectations placed on individuals within a marriage and the impact of neglecting these roles.
Character Analysis
Al'ameen: A dedicated and compassionate soldier who values duty and responsibility. His interactions with both his wife and the young girl highlight his caring nature.
Aisha (Wife): A character who struggles with her responsibilities and prefers a carefree lifestyle. Her actions create tension in her relationship with Al'ameen.
Aisha (Young Girl): Represents innocence and vulnerability. Her encounter with Al'ameen showcases his kindness and willingness to help others.
Writing Style
The novel is written in a straightforward and engaging manner, making it accessible to a wide audience. The use of dialogues effectively brings out the characters' personalities and emotions, while the descriptions of daily life add authenticity to the story.
Conclusion
"Surbajo" is a thought-provoking novel that offers readers an insightful look into the dynamics of relationships and the importance of fulfilling one's responsibilities. Through its relatable characters and engaging narrative, the story emphasizes the value of compassion, duty, and societal expectations. It’s a valuable read for anyone interested in exploring the complexities of human interactions and the impact of personal choices on relationships.
Surbajo hausa novel part 1
Sauri yake ya ƙarasa gidan saboda yaga bakwai na safe tayi. Tunda ya fita sallar asuba bai dawo ba yana masallaci sai yanzu tafiya yake yana addu'a cikin zuciyarsa Allah dai yasa Aisha taga dama ta tashi daga wannan mugun baccin nata na ƙaddara.
Tun daga shiga falo ya fahimci cewa adduarshi bata karɓu ba, duba da ganin yadda falon yake a hargitse tamkar filin wasan dambe.
Duk_da_dai_dama_falon_ya_saba zama _a cikin_wannan_yanayin, jikinshi a sanyaye ya haura sama ya nufi dakinta ai kuwa kamar yadda yayi hasashe tana kwance akan gado tana sharar baccinta.
Nan ya bita da kallo ranshi yana É“aci saboda tun jiya ya shaida mata yau zai koma bakin aiki kuma jirgin karfe takwas zai hau zuwa Port Harcout amma gashi ko tashi daga bacci ba tayi ba, idan da sabo ya saba da halinta, kawai juyawa yayi ya koma É—akinsa domin ya shiga wanka sabida yasan idan yace zai shiga toilet dinta yace zai yi wanka sai ya kusa amai saboda zarnin da toilet din ya keyi. Haka wannan littafi na surbajo ya cigaba.
Cikin abinda ba zai haura rabin awa ba har ya gama shiryawa cikin kakinsa na sojoji, kakin yayi kyau sosai saboda dama kyakkyawa ne shi. Jaka ya dauko sannan ya dauko mukullin motarsa, É—akinta ya nufa har yanzu tana baccinta, nan ya tasheta daga baccin ta buÉ—e idanu ta ganshi a tsaye cikin shiri, wani tsaki tayi sannan tace amma wallahi al'ameen kai dan rainin hankali ne, yanzu ace fisabilillahi ina bacci zaka zo ka tashe ni.
Bai yi mamaki ba domin ya saba jin abinda yafi haka ma daga bakinta, cewa yayi ni zan wuce ya bata amsa, ya cire Kudi ya ajiye mata kimanin Naira dubu É—ari uku (300,000) a kan durowar gefen gado, kallon wannan kudi tayi a wulakance, tace na menene wannan kuma na cefane ne kiyi amfani dashi kafin na dawo daga tafiya.
Surbajo novel part 2
idan na tafi wata uku zanyi, kan uban-nan!! Aisha ta faÉ—a yayinda take sakkowa daga kan gadon, tace wallahi al'ameen kayi kadan zaka yi wata uku ka É—auki Naira dubu 300k ka bani wallahi ba zai yiwu ba ta faÉ—a yayinda ta zubar da yawun daya taru a cikin bakinta a jikin bangon dakinta.
Al-ameen ba mutum ne mai son hayaniya ba, dan haka sai yace, nawa kike so? Naira dubu É—ari biyar 500k ta bashi amsa, bai musa mata ba ya dauko kuÉ—in ya kara mata sannan yace sai na dawo, kiyi min addu'a, a gayas ta bashi amsa tareda komawa gado ta kwanta.
Fita yayi waje, wani kurtun soja yazo da sauri ya amshi kayan dake hannunsa yasa a boot É—in mota sannan ya buÉ—e masa bayan motar ya shiga, shima ya zagaya kusurwar direba ya tayar da motar suka fita yayinda wasu motoci biyu na sojoji suka saka wannan mota a tsakiya, sai Airport suna zuwa kai tsaye ya shiga jirgi dama tuni an gama shirya komai, jirginsu ya É—aga zuwa Jihar Rivers, safe trip al'ameen.
Tunda al'ameen ya fita, Aisha ta cigaba da bacci bata tashi ba sai misalin ƙarfe tara, sannan ta mike ta shiga bayi ta ɗaura alwala sannan tayi sallar asuba. Bayan ta idar kitchen ta nufa madara ta kwaɓa a cikin kofi da Milo ta zuba ruwan sanyi ta juya da cokali yayi kauri kamar chakuleti, sannan ta dauko gorar ruwan faro ta dawo falo ta fara sha. Surbajo novel haka ya cigaba.
Duk duniya babu abinda Aisha ta tsana kamar tayi girki, sam bata son yin girki shine dalilin da yasa ma bata iya ba.
Zamanta keda wuya a falon taji ana ringing bell, cikin sauri taje bakin kofar ta leƙa domin ganin wanene, wani ihu tasa kafin ta bude kofar, tana budewa suka rungume juna ita da kawayen nata su biyu kai tsaye dakin al'ameen tayi musu masauki domin bata so su rainata idan sunje dakinta saboda datti da ƙazanta.
A falonsa suka zauna, nan suka shiga hira da wadda ta dace da wadda bata dace ba, suyi gulmar wannan baiwar Allah suyi ta waccan haka abin nasu. Can kuma sai ta fara basu labarin yadda suke zaman aure a gidansu da mijinta kamar yadda suka saba koda yaushe idan sun taru da ƙawayen, shewa ƙawayen suke kawai suna kara zuga A'isha, har suna fadin Eshat baby baki da dama.
Surbajo novel part 3
Dariya tayi sannan ta basu labarin yadda suka rabu yau da mijinta al'ameen, ɗaya daga cikin ƙawayen mai suna Ruky tace woho! mutuniyar kina wuta muna ƙara miki fetur, ina namu kashin tunda kin tatsa muma kinga sai ki sammana, ko yaya kika ce Zuly baby??
Wannan gaskiya ne ɗayar ƙawar mai suna Zuly ta bada amsa, Eshat sai ta fara magana haba sisters, har sai kun roƙe ni, ai kun wuce haka a wajena dan haka ku kwantar da hankali nifa wallahi kun fiye min al'ameen so dubu a wajena, domin Al'ameen dashi da banza duka daya na ɗauke su a gurina.
Kuma dama saboda nasan zan baku naku rabon ne yasa nace masa se ya ƙaramin kuɗi, saboda haka zan baku Naira dubu ɗari biyu 200k sai ku raba, Ihu suka yi suka rungume Aisha har da haɗa baki wajen fadin heyyy se madam tamu Allah dai ya biya Hajiya.
*Asalin wannan labari na SURBAJO novel*
Al'ameen jibrin sulaiman cikakken sunansa kenan matashi ne wanda ba zai haura shekaru 35 da haihuwa ba. Ɗa ne ga major general jibril sulaiman. Babansa asalinsa ɗan garin kano ne a wata anguwa da ake kira da lungun gabari, can ne asalin masomin su amma sanadiyyar aikin soja ya dawo kaduna da zama a Malali layin Sultan Road kuma ya kasance hamshaƙin mai kudi ne a jihar kaduna domin a jerin masu arziki na garin dole za'a saka dashi a lissafi.
Matar Major Jibril É—aya hajiya Binta, suna kiranta da Umma, suna da yara hudu. Kabeer shine na farko sai kuma Al'ameen, Munawwara da kuma autarsu Amal.
Gidan major jibrin gida ne gidan tarbiyya domin yayansu gaba_daya babu mai halin banza. Mahaifiyarsu na basu tarbiyya dai dai gwargwado, arzikin dukiya bai sa tayi watsi da tarbiyyar yaranta ba, tun bayan da mahaifinsu yayi ritaya ya koma fannin kasuwanci na kasa da kasa yana da kamfanoni masu yawa a fadin jahohin Nigeria, mutum ne mai tsoron Allah bashi da buri daya wuce a yaransa ya samu mai gadonsa a aikin soja kullum addu'arsa kenan.
Surbajo novel last
Allah ya taimake shi ya bashi Al'ameen, tunda ya fara mallakar hankalinsa yaji yana sha'awar zuwa aikin soja koda ya tuntubi babansa da batun ba karamin farin ciki yayi ba, ba ayi mako ba ya samo mishi aikin da yake akwai connection shi ko kabeer dama accounting ya karanta. Yana aiki a CBN matarsa daya da yaronshi É—aya wanda suke kiran shi da suna Waleed. Domin sunan mahaifinsu yaci, Munawwara yanzu tana jss 3 yayinda autarsu Amal ke aji huÉ—u na primary.
Tun da Al'ameen ya fara aikin soja gaba É—aya hankalinsa ya maida shi bangaren aikin nasa kullum burinsa baya wuce ya taimaki kasarsa, a kaduna ya fara aikin kafin a mayar dashi zuwa Abuja.
Kamar yadda ya saba kullum yau ma ya taso daga aiki da karfe sha É—aya na dare ta Badarawa ya biyo dan zai fi masa saukin isa gida da wuri, ya wuce bus Stop kaÉ—an dai dai Galadima road ta jikin katangar gidan baba boss, ya hangeta tana kuka ga wajen yayi shiru babu kowa. Har ya wuce sai yaji yana son sanin meya sameta take kuka kuma zaune a bakin titi.
Juyowa yayi ya dawo wajenta layin galadima road din, Nan ya shiga dai-dai gidan kallon kwallo sannan yayi Parking ya fito ya tako zuwa gurin da take, sallama ya mata a gigice ta ɗago kanta tana kallonsa, ƙara matsawa kusa yayi yace yan'mata meya faru kika zauna anan kike kuka?
Ganin uniform din sojoji ne a jikinshi ne yasa tace a ranta "bari na faɗa masa wata kila ya taimaka min cikin kuka tace wallahi mamana ce ta wuni yau tana wankau ta samu kuɗin da zamu ci abinci, tun safen ba mu ci abinci ba, shine yanzu ta turoni na siyo mana garin rogon da zamu sha. Yanzu ban san ya akayi ba kudin suka fadi, shine kaga ina kuka domin nasan yau saita kusa kashe ni ta fadi ƙasa tana sake rushewa da sabon kuka
To ya isa haka Al'ameen ya fadi yana kallonta ba laifi yarinyar tana da kyau dai dai gwargwado kuma ba zata wuce shekara 18 ba, yaya sunanki? ya tambayeta, sunana Aisha ta bashi amsa inane gidanku? nuna masa gidan tayi da yatsa domin ba nisa, tashi muje yace mata zaro mishi idanu tayi tace wallahi naje mata babu sakon nan, sai ta dake ni, dan Allah ka wuce ka ƙyaleni, ba zata dake ki ba ni zan biyata kudin amman karɓi wannan kije wancan shagon ki siyo muku shayi, nan ya bata dubu 2k godiya ta shiga yi masa kamar za tayi masa sujjada, ta gudu ta tsallaka sannan ta siyo kayan shayin, na siyo gaba tayi yana binta a baya har suka ƙarasa ƙofar gidan.