Namiji baya kadan hausa novel 

"This novel" is a compelling Hausa novel that delves into family dynamics, respect, and the evolving relationship between siblings. Namiji baya kadan novel revolves around Mahmud and Khadija, who frequently find themselves at odds due to Mahmud's protective and sometimes intrusive nature.

Plot Summary

Mahmud is often seen intruding on Khadija's interactions with her suitors, much to her frustration. The novel captures a series of confrontations where Mahmud's overprotective behavior leads to conflicts between them. Their mother and aunt frequently intervene, highlighting the constant familial tension.

Throughout the story, Mahmud insists he’s no longer the boy Khadija once knew, but rather a man deserving respect. His actions, however, are driven by a genuine concern for Khadija, although she perceives it as an overreach. The narrative also explores Mahmud's personal growth and his struggle to balance his protective instincts with respecting Khadija's independence.

Themes

1. Family Dynamics: The novel portrays the complexities of sibling relationships and the protective instincts that often lead to misunderstandings.

2. Respect and Growth: It explores themes of respect, personal growth, and the transition from childhood to adulthood.

3. Conflict and Resolution: The story navigates through conflicts arising from overprotection and the subsequent efforts to resolve these differences.

Character Analysis

Mahmud: A central character whose protective nature sometimes comes off as intrusive. His journey is about gaining respect and understanding his boundaries.

Khadija: A strong-willed character who seeks independence and respect from her family, particularly her brother. Her interactions with Mahmud highlight her struggle for personal space.

Writing Style

The novel is written in a conversational style, making it accessible and engaging. It effectively uses dialogues to develop characters and advance the plot, providing a window into the cultural and familial settings of the story.

Namiji baya kadan novel part 1

Zaune suke a cikin falon suna hiran jindaɗi saboda yau gidan cikin nishadi ake, Mahmud wanda ya shigo yanzu cikin miskilanci ya zauna a gefen Maminshi tareda taɓe fuska yana wani huci, ya kalli Khadija dake gefe ɗauke da waya tana magana, kuma ga dukkan alamu da mutumin da ya kora yanzu ne suke magana.

Bayan ta katse kiran ta juyo ta tsurawa Mahmud idanu da alamun tuhuma, Shima Mahmud idon ya tsura mata tareda da wani hade fuska yace, "Wallahi ni har kunya ma kike bani kalli irin mutanen da suke zuwa suna yi mana layi a bakin kofar gida yadda kasan sun samu gidan mai. Duk gasu nan tarkacen banza.

Ita kuwa Khadija harara ta watsa masa cikin bacin rai sannan ta juya ta kalli Mami da Anty dake zaune tace. " Mami Dan_Allah ku_dinga yiwa_yaron_nan nasiha_ya fita daga_harkokina, wai ace duk mutumin da yazo_wajena sai_ya_dinga_korarsu ko_kuma ni_sa'arsa ce ni_wallahi_banason rainin hankali haka jiya ya yiwa Sulaiman rashin mutunci yau kuma ya kori Alhaji Bashir to me yake so dani"?.

Shima fuskar Mahmud ya haɗe yana cewa "Ke da_Allah kiyi ta tara tsofaffin mutane bayan ko sun aure ki ba iya zama zasu yi dake ba, koma sun aureki". Mami ce ta duba su cikin ƙosawa da irin hali nasu domin idan da sabo tofa sun saba, yanzu zaka jisu suna ta sa'insa anjima kuma ka jisu suna hira da ƙus-ƙus.

Wannan dalilin yasa ta miƙe tana cewa "toh kai Mahmud meyasa kake korar mata bakinta idan sun zo kai wane irin ɗan uwane wannan". Aunty Mami kuwa miƙewa tayi tana "ke Khadija ya akayi har yasan da zuwan bakin naki har yake korar nasu"?.

Hannu ta tura cikin nuna shi da yatsa tana cewa "Wallahi Aunty yaron_nan ya fiye sa'ido ne mutum kamar maye". Bata gama rufe baki ba ya taso a fusace ya tsaya a gabanta yana nuna ta da yatsa har jikinsa na rawa, ransa a ɓace muryarsa na rawa yace "Wallahi ina gaya_miki ki daina_ce min_yaro wallahi ki kiyayeni_Khadija waye_yaron sai kace_wata kanwar_uwata ki_dinga ce min_yaro" a fili ɓacin_ransa ke_bayyana.

Namiji baya kadan novel last part 

"Kwaraikuwa na gayama_yaro shekara nawa ne a tsakaninmu idan ka manta bari na tuna maka kasan ni nake muku wanka da shirya ku lokacin da kuke zuwa makarantar firamare ko"? Mahmud haɗe fuska yayi tareda matsowa kusa da ita cikin yin ƙasa ƙasa da murya tareda ɗan tsurawa Khadija idanu yana lumshe su yace "Khadija wallahi shi namiji baya kadan kuma ki daina cemin yaro, yayi tsaki wai nayi kaɗan? haba ni nasan nayi miki yawa ne ba wani kaɗan ba idan kuma kina shakku to nayi miki alƙawarin nan gaba zaki gane".

Dariya dai Khadijan ta ɗanyi cikin rashin gamsuwa da kalamansa tace "Wani ba Amma ba kai ba tukum domin kana sane cewa ni yayarka ce amma dan ka raina ni sai kake kirana Khadija kai tsaye wallahi sai na haɗaka da Abba zaka gane".

Murmushi Mahmud ya ɗanyi tareda cewa "ai idan nace miki Aunty saboda ke yayata wallahi naji kunya saboda na ɓata burin raina kuma zan janyowa muradina naƙasu". Nan dai Khadijan miƙewa tayi tana takawa a hankali tace "Na rantse kai Mahmud ka fiye son girman bala'i".

Shi dai idanu ya tsura mata tareda sauke wani ajiyar zuciya cikin wata iriyar murya yace "dazu a waje naga wata mai kama dake a bakin titi komai naku ɗaya kamar yan biyunki" juyowa tayi cikin yamutse fuska tace wata mai ƙiba ko"? Ido ya lumshe cikin daga gira yace "Ya aka yi kika gane haka take"?

Cewa_tayi "ai nasan da_anga wata_mai ƙiba sai ace muna_kama ni fa wallahi_banason ƙibar_nan". Shima Mahmud miƙewa yayi ya ɗan tako ya matso kusa da ita yace "ke wallahi mace mai ƙiba tayi a rayuwa ni bana son naga mace siririya saboda mai zanyi da mace ramammiya.

Cikin ranta dai cewa tayi Mahmud baya jin kunyata ma wannan maganganu haka. Yaron da magana ma tsada take yi masa ko yaushe bashi da abokin hira sai littatafanshi da kuma karatun Kur'ani. Shi kuwa cikin sanyin jiki yace 

"kina jin bacci ne"? Kai ta gyada mai alamar cewa a'a.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda cewa ki hau online akwai labarin da zan gaya miki" kar bar wayarta yayi ya buɗe mata data sannan yace "bari naji dakin mu na baki labarin"