Mijin kwaila novel part 1
"Mijin Kwaila" is a captivating story about family dynamics, arranged marriages, and the clash of personalities. The plot revolves around Sagir Haruna, known as Daddy, and his unexpected marriage to his cousin Bilkisu, orchestrated by their domineering grandmother, Baba Hajara.Sagir, a reserved and introverted young man, is forced into this marriage despite his strong aversion to the idea. Bilkisu, on the other hand, is a lively and talkative girl who has had a crush on Daddy since childhood. The forced union between the introverted Sagir and the extroverted Bilkisu creates a humorous and challenging scenario.As the story unfolds, Sagir struggles to accept his new reality of living with a much younger and boisterous wife. The narrative explores themes of obedience, family pressure, and the adjustments required in an arranged marriage."Mijin Kwaila" offers a blend of humor and drama, providing insight into the complexities of arranged marriages and the diverse personalities within a family. The story is engaging and thought-provoking, making it an enjoyable read.
Mafarin labarin mijin kwaila
Sanin kowane mahaluƙi ne daya tashi a cikin dangin Alhaji Sagiru Kacako, wato mai aman naira, laƙabin da abokan kasuwancinsa suka laƙaba masa kenan, matarsa Hajara ita take juya gidan, abun da tace shi ake yi, yadda ta dama haka za'a sha kuma yadda take so ko kuma yadda tace to fa haka za'a aiwatar, babu wanda ya isa ya sauka daga kan layinta ko kuma ya bijirewa umarnin ta koda kuwa ba hakan aka so ba kama daga kan babban ɗanta Alhaji Haruna, ko ƙannensa Alhaji Kabiru da kuma autansu Alhaji Buba. Tun zamanin mijinta na da rai wato mahaifinsu har kawo yanzu daya jima da barin wannan duniyar. Wannan auran da aka ɗaura tsakanin babban ɗan gidan Alhaji Haruna wato Sagir Haruna Sagir (Daddy) da kuma Bilkisu Kabir Sagir waɗanda suka kasance ƴaƴan wa da ƙani cousins kenan a turance, duk yana cikin umarnin baba Hajara ne ga ƴaƴanta Haruna da sagiru waɗanda babu yadda suka iya da ita duk kuwa da sanin irin halin ɗan nasu sagiru naƙin son aure kuma musamman ma yarinyar da aka aura masa saboda sam babu jituwa tsakaninsa da ita ko kaɗan.
Sagir dai wato Daddy kamar yadda ake ɓoye masa suna saboda cin sunan maigidan da yayi wato Alhaji sagiru kacako, matashin saurayi ɗan shekara ashirin da shida kamar yadda bayani yazo tun daya taso a gidansu mutum ne shi mai nesanta kansa da sauran mutane, shi ɗin irin mutanen nan ne da ake kira da introvert a turance, sam baya son hayaniya ko kaɗan haka kuma baya shiri sam da duk wani mutum mai hayaniya. Wannan ne babban dalilin daya sa baya jituwa da kakar tasa baba Hajara wacce mai ta kasance mai kwarereto da karaɗin gaske, haka kuma jikar tata ma take wato Bilkisu, yarinyar da baba Hajara ta shiga ta fita ta saka mahaifinsa lallai tilas ya aura masa ita bayan ta tara kowa da kowa na iyalinta ta gargaɗi kunnensu akan kar a sanar da babban jikan nata wato Daddy.
Bilkisu a nata ɓangaren yarinya ce mai rawar kan gaske, yarinya ce mai tsananin surutu da cakwaikwaiya kuma da yake bata iya ɓoye komai da yazo ranta, tun tana ƴar shekara tara take gayawa mutane irin son da takewa cousin ɗinta Daddy, a lokacin da Daddy yaji haka kuwa hankalinsa ya kai ƙololuwa wurin tashi musamman da yaga rigimammiyar tsohuwa kamar yadda yake faɗawa baba Hajara, tayi na'am da jin wannan zancen. Da farko duk mutane a cikin dangi sun ɗauki maganar Bilkisu ne a matsayin wasa musamman ma da yake yarinya ce ƙarama.
Mijin kwaila novel part 2
Bayan shekara huɗu..
Da yake tasu tazo ɗaya da baba Hajara haka kuma a duk hirarsu Bilkisu ta kan sako zancen Daddy, har wata rana baba Hajara tace;
"Ke kuwa mai gadon zinare mai zaki da wannan yaron mai girman kan tsiya, ki rabu dashi ni zan haɗaki da tsalelen saurayi san kowa kin wanda ya rasa.. Baba hajara ta ƙarasa maganar ta bayan ta ɗauko wani tsohon magoginta na goro ta fara goga wani daushe akai saboda babu haƙoran cin goron sai ta goga ta mayar dashi gari take iya ci.
Shassheƙar kukan bilki ne ya dawo da hankalin baba hajara kanta hakan yasa baba hajara sakin salati tana tafa hannayenta, faɗi take mai zan gani daga magana shine kika fara kuka don nace ki kyale wannan mutakabbirin yaron?
"To ba ke bace kike cewa wai na daina sonsa. Bilki ta faɗa tana share hawayenta haɗe da zumburo bakin shagwaɓa..
Kaɗa kai baba Hajara tayi tana faɗin eh lallai ba shakka yaran zamani, to bari harunan yazo ni zansa ya aura miki sagirun ko yana so ka baya so, kin dai ce kinji kin gani. Wannan maganar ta baba hajara ita ce mafarin ƙaddarar auren Sagir Haruna wato daddy da amaryarsa ƴar shekara goma sha uku.
Ai da gudu Bilkisu ta tashi tayi cikin gida tana dariya dama tazo ne taya kakar tata hira kamar yadda ta saba. A wannan ranar babu wanda Bilkisu bata bawa labarin auren ta da yaya daddy ba sai dai idan bata haɗu da mutum ba.
Bayan wata ɗaya kamar yadda baba Hajara ta tsara aka yi shagalin biki duk kuwa da cewar daddy yazo ganin gida sati biyu da suka wuce amma babu wanda ya fada masa saboda gudu bacin ran baba Hajara har ya koma Abuja. Sai ranar litinin wuraren karfe biyar na yamma a lokacin yana tare da wasu abokan aiki acan gwarinpa, sunje ganin wani site wanda za'a bige a canza masa fasalin sa, suna cikin tattaunawa da masu wurin daddy yaga kiran waya daga mahaifinsa, gefe ya koma ta ansa kiran anan mahaifinsa yake fada masa yazo ya same shi a gidan sa yana jiransa. Hakan ya bashi mamaki amma saboda babu lokacin tsayawa nazari sai ya tafi gida.
Mijin kwaila novel last part
Ashe acan ne zai tarar da babban abin mamaki da tashin hankali domin kuwa mahaifinsa ne Alhaji Haruna da kuma kwailar amaryarsa yar shekara goma sha uku da mahaifin nasa ya taso daga garin ya kawo masa ita ya kuma damka masa ita hannu da hannu don kada ma ya dauki maganar a matsayin wasa idan aka bar ta da mata su kawo ta. Bayan mahaifin nasa ya hada su yayi musu nasiha mai shiga ciki daga nan ya umarci Bilkisu data shiga ciki sannan ya yara hankalinsa wuri daya yayiwa dansa kashedi sosai ya gargade shi akan lallai ya kula da Bilkisu kada kuma ya sake ya sauki hukunci a hannunsa, kowane laifi tayi masa ga waya nan zai iya kira ya sanar dashi,, da haka yayi masa sallama ya bi jirgi ya koma garin Kano a wannan yammacin.
Tunda Sagir Haruna yake bai taba ganin abin mamaki da dimuwa irin kawo masa Bilkisu a matsayin mata ba.
"Duka duka nawa take, daddy ya fada a fili ba tare daya san ya magantu ba. Bilkisu da ta fito neman ruwan sha ashe taji shi sai kada baki tayi tace;
"Haba yaya daddy, shekaruna fa sha uku kuma wannan month ɗin mai shigowa zan shiga sha huɗu, 1st April !..
Yana daga zaune ya kafeta da idanunsa biyu, gumi sai karyo masa yake saboda shiga tashin hankalin yadda zai yi rayuwa da kwailar yarinya Bilkisu mai mugun surutu.
"Yaya akwai tashar" bollywood 4 u" kuwa nan gidan? Kasan fa ni sai da tashar bollywood 4 u nake iya rayuwa a wuri, kuma dama..
"Ke!..
Tana cikin sana'arta sai zuba take kamar kanya taji tsawar da daddy ya daka mata, babu shiri ta falla a guje ta koma ɗakin data fito.
Haka ne ya tabbatarwa daddy cewar lallai ba aure aka masa ba, an dai kawo masa yarinya ne yayi reno saboda haka zai ɗauki al'amarin a haka yadda yazo masa.