Littattafan hausa novels masu dadi
Allah mai girma da daukaka ya albarkaci garuruwan Hausawa da fasihan marubutan littafai daban-daban maza da mata. Wasu marubuta sunyi rubutunsu ne akan littafai na labaran ban dariya wasu kuma sunyi ne akan littattafan hausa novel masu dadi wanda ke ƙara basira wa masoya dama inganta al'adun Hausawa. Haka kuma ubangiji ya albarkaci ƙasar ta Hausa da masu karanta littafan Hausa Novels har complete din su.Nayi mu'amala da mutane da dama wanda na fuskanci suna matukar neman Hausa Novels Complete domin ɗebe kewa dama samun nishadin rayuwa. Wannan ne dalilin da yasa na garzaya babbar ma'ajiyar Littattafai musamman romantic Hausa novels wacce muka fi sani a turance da digital Books store wato Arewa Books sannan nayi muku tsarabar jerin sababbi dama tsofaffin littafan Hausa wanda nake tunanin da izinin ubangiji zasu amfane ku ta hanyoyi masu yawa, idan da bukata zaku iya ziyartar store din kai tsaye domin kashe ƙwarƙwatar idanunku.
Ga jerin littattafan hausa novel complete masu dadi na 2023 - 2024 - dama na 2025 munyi wannan zaɓe daga kowane Category, kuma zaku iya bin wannan Link domin karantawa kai tsaye idan kuma yaƙi aiki sai a daddana a uwa Google Domin samun abinda ake buƙata _www.arewabooks.com_ sannan kuma ayi sani cewa kowane littafi dake kan wannan shafin yanar gizo na arewa yanada marubucinsa haka zalika kowane marubuci yana da cikakkiyar dama akan ya siyar da littafinsa ko kuma ya baiwa makaranta kyauta domin ayi sani cewa shafin tsamiya novels bashi zai baka damar cimma burinka na karanta cikakken littafin ba, amma wata wannan gida namu ya rubuta shi kyauta, domin dubawa sai ka danna alamar rariya dake sama sannan ka rubuta sunan littafin ka bincika idan ka dace kaga shikenan.
Sannan ayi sani cewa kowane littafi a shafin intanet na ArewaBooks yana kamawa daga abinda marubucinsa ya bada dama, cikin sauƙi sai ka saka yan kudadenka domin karanta wanda kake so.
Wasu daga cikin littattafan hausa novel complete masu dadi gamida Zafi amma in da kuÉ—inka.
(1). Babu So
rubutaccen labari ne daga babban marubuciya Bilyn Abdul wanda ya kunshi soyayya da shakuwa tsakanin masoya.
(2). Tsintacciya
Daga Nimcy Luv, wanda yan magana ke cewa tsintacciyar mage bata mage, amma a halin gaskiya da nazarin rayuwa wannan batu akwai gyara cikinsa.
(3). Idon Naira
Marubuciya: Mamuh Gee. Wannan yana É—aya daga cikin littattafan hausa novel masu dadi, domin littafi ne da yayi duba akan rayuwar mutane masu ₦aira ko nace masu kuÉ—i.
(4). Kufan Wuta
Safiya Huguma ta zazzage tsagwaron basirarta domin antayo muku wannan novel, abinda ke tsakaninka dashi abokina ko ƙawata shine ziyartan shafin na arewabooks
(5). Zain Abeed
Nimcy Luv ta ciri tuta domin wannan shine littafinta na biyu a cikin wannan jeri namu, wannan littafi ta rubutashi akan gundarin rayuwar Zain Abeed
(6). Gurbin Ido
Itama Safiya Huguma ba'a barta baya ba, domin dama marubuciya ce mai É—umbin mabiya, wacce ta saba zubo zafafan romantic hausa novels.
(7). Noor ƙalbi
Hajiyar marubuciya Mamuh Gee, itace marubuciyar wanga littafi wannan ke nufin Hasken zuciya a fassarar Hausa, ko bamu faÉ—a ba wannan littafi tayi shine akan soyayya.
(8). Daudar Gora
Wannan littafi na Billyn Abdul yana É—aya daga cikin Littattafai wanda ake matukar nemansu a kafafen Sada zumunta dama gaba ilahirin yanar gizo. Domin mu kanmu a wannan gida mun bayar da wani yanki na wannan littafi, sai ka bincika domin nishadantar da kanka.
(9) Gobe Da Nisa
Marubuciya: PhartyBB wannan labari na gobe da nisa yana É—aya daga cikin littattafan hausa novel complete masu dadi wanda nima da kaina na neme shi domin ka gwangwaje basirar wannan marubuciya.
(10). Sanadin Labarina
Novel daga Hafsat Rano, wannan shima labari ne wanda yaja hankali makaranta daga kowane É“angare na gida Najeriya.
(11). Wake Daya
Yan magana suka ce wake É—aya baya É“ata miya, amma dangane da nazarin rayuwa tofa wake É—aya kan iya É“ata miya, sai dai idan hali bai kai ba. marubuciyar wannan littafi itace Mom Islam.
(12). Ki Kula Ni
Sabon Hausa novel daga Nana Hafsat, wanda ya kasance labari ne na soyayya. Wanda ke ƙunshe da darasin rayuwa iri daban daban, kama daga yadda al'ummar Hausa ke mu'amalantar junansu ta hanyoyi da dama.
(13). A Rubuce Take
Kaddara kenan, shine ma'anar wannan labari na Safiya Huguma, wanda tayi dogon nazari da hangen nesa wajen yin aikinsa wanda ke tabbatar da amsa sunansa.
(14). Wata Zuciyar
ÆŠaya daga cikin fasihan marubuta Ibrahim Maliey, shima ba'a barshi a baya ba, domin ya gwangwaje mu da wanga romantic hausa novel mai dadi, kuma saka masa suna wata zuciyar.
(15). Ragamar Damisa
yana É—aya daga cikin littattafan hausa novel complete masu dadi a manhajar Arewa books, haka zalika kuma littafin ya samu karatu sama da sau dubu goma, marubuciyar wannan littafi itace Miss Anyway.
(16). Amaryar Daji
Sabon labarin Ummu Sultan wanda ke da laƙabin amaryar daji, shima ya karbi reviews da yawa daga mutanen da suka karanta shi, shiyasa ma muka saka shi cikin wanga jeri.
(17). Bakar Shuka
Hausa Usman Maijidda tayi nazari gamida tunani wajen antayo wannan labari, domin yana dauke da darasussukan rayuwa masu yawan gaske, wanda zaka karu dasu dama amfanar da al'umma baki ɗaya. Idan ka karanta wannan labari zaka gane me baƙar shuka ke nufi wanda idan baka taimaka wajen cire ta daga cikin al'umma ba, to fa zata shafi kowa da kowa har da kai.
(18). Sarki Sameer
Marubuciya Azeemah Dahiru, tayi rubutu kan wata katafaren masarautar Sarki Sameer, da yawa mun san yadda rigingimun masarautu ke kasancewa. Inda Itama Azeemah Dahiru tayi iya yinta domin magance wasu matsaloli a cikin wannan rubutu nata.
(19). Sakatariyata
Complete novel daga marubuciya Azeezat, wanda yanzu haka yana É—aya daga cikin littattafan hausa novel complete masu dadi, abin da kawai ya rage tsakaninka da wanga littafi, shine ka garzaya shafin arewabooks ko Wattpad asha karatu lafiya.
(20). Rafeeq
Hajjace antin marubuta ta doko sabo, haba ai sai ma ka karanta zaka wannan zance nawa, domin littafi ne wanda ta rubutashi akan rayuwar matashi Rafeeq.
Wadannan litattafan hausa novel complete masu daÉ—i guda 20 da muka kawo a sama sune wadanda suke tashe a manhajar ArewaBooks kuma kowannensu idan zaka karanta to siya ake da kudi wato ka biya ka kwashe.
Shahararrun Littattafai daga marubuta daban daban:
(1)Shamsuddeen
Marubuciya: Oummu Amna
(2)Kaddarata ce
Marubuciya: Yusuf Hussain
(3)The Dark Room
Marubuci: Khali Boy
(4)Matata Ce
Marubuciya: Miss Hajo
(5)Great Relationships
Marubuci: Isah Abdulsamad
Littattafan hausa novel complete masu dadi na Adventure guda biyar (5)
(1)Jaruman Duniya
Marubuci: Mansur Usman Sufi
(2)Mijin Tace
Marubuciya: Hafsat Sodangi
(3)Fataucin Bayi
Marubuci: Mansur Usman Sufi
(4)Takobin Daukaka
Marubuci: Mansur Usman Sufi
(5)Sarkin Sadaukai
Marubuci: Mansur Usman Sufi
Ƙirƙirarrun labarai (5) wanda za'a iya samu a arewabooks da Wattpad.
(1)Wata Kaddara
Marubuciya: Shamsiyya Manga
(2)Ciwon Zuciya
Marubuci: Abba Shehu
(3)Me Zanyi Da Ita?
Marubuciya: Nazifa
(4)Kukan Kurciya
Marubuciya: Miss Anyway
(5)Yel
Marubuciya: Xayyeeshert
Ayi sani cewa ba iya jerin littafan kenan ba. Akwai saura daga shafukan yanar gizo daban daban, domin ko a wannan gida na tsamiya novels akwai su da dama.
Littafan hausa novel complete masu dadi guda ashirin da doriya wanda muka lissafa a sama, gaba ɗaya zaku iya samun su a shafin na ArewaBooks wasu kuma a wannan gida namu na tsamiya novels, haka zalika kuma suna da manhajar waya wato application muma muna ƙoƙarin ɗora namu a koda yaushe za ku iya sauketa daga PlayStore ku karanta duk littafin da kuke so a natse.