Kurkukun kaddara novel part 1

"Kurkukun Kaddara" is a touching story set in Jalingo, Taraba State, Nigeria. The protagonist, Kalla Adamu, is a 35-year-old accountant who struggles with insomnia and the burden of caring for his ailing mother. His wife, Gloria, died during childbirth two years ago, leaving him heartbroken and overwhelmed.

Kalla's mother, who suffers from dementia, has been a pillar of strength throughout his life, enduring hardships and working tirelessly to support his education. Her illness and the loss of his wife have taken a toll on Kalla, affecting his performance at work and leading to warnings from his employer.

Despite his friends' advice to remarry for support, Kalla fears bringing someone into his life who might not care for his mother as Gloria did. His previous attempt at remarriage ended quickly when his new wife couldn't handle the situation. Kalla remains determined to find a way out of his predicament, hoping for a better future while dealing with his current struggles.

"Kurkukun Kaddara" is a poignant tale of love, loss, and the challenges of balancing personal and familial responsibilities. The story highlights the deep bond between Kalla and his mother and his unwavering commitment to her well-being.

Ruwa ne mai yawan gaske ake ta zubawa a cikin garin Jalingo, babban birnin jahar Taraba wadda ke arewacin Æ™asar Najeriya. Garin yayi baÆ™i Æ™irin sakamakon wutar lantarki da aka É—auke saboda ruwan da ake ta tsulawa tun misalin Æ™arfe tara da rabi na dare gashi kuma har yanzu Æ™arfe biyun dare ruwan sai zuba yake kamar da bakin kwarya. A wannan ruwan da ake ta dokawa É—aukacin al'ummar garin Jalingo bacci suke yi duk da dai ba za'a rasa É—aiÉ—aikun mutanen da ba suyi baccin ba, a daidai wannan lokacin Æ™ila saboda wani uzurin daya hana su yin baccin ko kuma dai wani dalilin daban. 

A cikin ire iren mutanen da za'a iya sawa a lissafin mutanen da idanunsu suke a farke waÉ—anda ba suyi bacci ba a wannan lokacin akwai Kalla Adamu É—an asalin jihar Taraba. Kalla, wanda ya kasance É—an shekara talatin da biyar, akawu ne (accountant) a fidelity bank reshen jihar garin su, haka kuma ya jima yana fama da lalurar rashin bacci ko kuma muce lalurar rashin isasshen bacci tun sa'ilin daya fara jiyyar tsohuwar mahaifiyarsa tare kuma da rasa matarsa Gloria da yayi wacce ta gamu da ajalinta a wurin naÆ™uda. 

Shekaru biyu sun shuÉ—e tun lokacin da matar tasa ta mutu, amma alhinin rashinta har zuwa yau yana É—awainiya da Kalla Adamu, haka kuma a duk lokacin daya kalli mahaifiyarsa akan gadon jiyyarta Æ™irjin sa yakan Æ™ara nauyi musamman da yake mahaifiyar Kalla mace ce mai karsashi domin kwata kwata bata da lalaci ko son jiki a wancan lokacin da take da lafiya kuma musamman ma kafin girma ya kamata. Kalla baya manta irin É—awainiyar da mahaifiyarsa tayi dashi duk domin ya tsaya da Æ™afafunsa a wannan rayuwar mai cike da Æ™alubale. 

Mahaifiyar Kalla mace ce wacce tayi rayuwa mai tsaho cikin ƙunci, wahala da ɓacin rai kala-kala. Tun daga lokacin da ta auri mahaifinsa babu irin kyara, takura, da ƙasƙancin da bata gani ba a wurin dangin mijinta wanda ya mutu wata biyar kacal bayan auren su. Hakan ne yasa dangin mijinta suka laƙaba mata kalmar maiya suka kuma haƙiƙance ita ta cinye kurwar ɗan uwansu, wanda da wannan hujjar tasu ce sukai amfani da ita su kai mata korar kare daga gidan su, dama a ɗaki ɗaya suke, ɗakin mijinta tun bayan aurensu. Haka dole babu yadda ta iya ta koma gidansu inda anan ta haifi Kalla tayi jegonsa.
 

Kurkukun kaddara hausa novel part 2 

Mahaifiyar tasa tayi sana'o'i kala-kala duk domin ta biya kuÉ—aÉ—en makarantarsa fara daga iliminsa na firamare har zuwa kammala karatun jami'ar sa. Mahaifiyar tasa tayi niÆ™a irin wanda akeyi akan dutse tun zamanin mulkin farar hula na farko har zuwa lokacin data haÉ—a kuÉ—i ta sayi injin markaÉ—e, bayan an sace injin markaÉ—en sai kuma ta koma yin lebura a wurin yin gini duk kuwa da kasancewar ta mace, da irin wannan leburancin na gini ta haÉ—a jarin yin fanke da Æ™osai safiya da maraice duk saboda ta É—au nauyi tilon É—anta Kalla Adamu. 

Cutar alzheimer wato dementia (cutar mantau) ita ce cutar da mahaifiyar tasa take fama da ita, kuma dama bisa ga al'adar ita wannan cutar mafi yawa tana kama mutane ne waÉ—anda suka fuskanci É“acin rai mai yawa har zuwa lokacin tsufan su. To yau dai ga mahaifiyar Kalla kwance babu abinda zata iya yi da kanta sai dai ayi mata. Yana daga cikin dalilan Kalla naÆ™in Æ™ara wani auren tun bayan mutuwar Gloria matarsa. Abin da yake gudu shine kar yaje ya auro wacce za tazo taÆ™i kula da mahaifiyar tasa. Yasan ba kowace mace bace zata iya juriya tayi É—awainiyar da Gloria matarsa tayi da mahaifiyar sa wacce lalurarta ke buÆ™atar tsantsar kulawa ta gaske. 

Irin wannan tunane tunanen ne su ka yiwa Kalla yawa har suka jaza masa lalurar insomnia watau rashin baccin da yake fama dashi. Ga matsakaicin ciwon kai da yake wuni ko kwana dashi kusan kullum babu dare babu rana sai dai idan ya É—an samu relief wato sassauci wanda shi É—in ma kusan jifa-jifa ne, amma idan ana sabo da ciwo to shi kam Kalla ya riga ya saba da tsananin ciwon kan nan nasa. Babbar barazanar da tasa lalurar take neman kawo masa itace query (gargaÉ—i) da ake bashi a wurin aikinsa na banki har sau biyu.

Saboda kura kurai da yakan tafka lokaci zuwa lokaci a cikin aikinsa na kan kantar banki (counter) akan bashi gargaÉ—i wanda a yanzu haka ya karÉ“i biyu kuma hukumar banki ta tabbatar masa da cewar idan aka sake samun sa da wani kuskuren to la budda babu makawa sallamarsa za'a yi, a cewarsu wai lamunin da aka yi masa ma ya samo asali ne saboda kwazonsa da jajircewarsa wacce aka sanshi da ita a da. 

Kurkukun kaddara hausa novel last part

Saboda irin waÉ—annan matsalolin ne abokansa ko nace aminansa biyu Ado da Jamilu ke yawan kawo masa maganar aure, suna yawan faÉ—a masa cewa aure shine kaÉ—ai hanyar da zai samu nutsuwarsa ta dawo ya kuma samu wasu nauyin dake kansa ya ragu, amma shi kuma Kallamu abinda yake gudu dai É—aya ne wato kar ya auro wata mace tazo ta shashantar da lamarin mahaifiyarsa. Amma saboda aminansa biyu da suka matsa masa lamba akan maganar auren, kuma da faÉ—in hausawa da suke cewa; sai an gwada akan san na kwarai, Kallamu ya taÉ“a auren wata yarinyar Æ´ar kudancin taraba wata shida da suka wuce amma fa tun a satin farko yarinyar tace ita fa ba zata iya ba, haka dai yana ji yana gani ya sawwaÆ™e mata. 

Kallamu ya riga ya ƙudurce babu shi babu yin wani auren matuƙar bai samu wacce zata maye gurbin Gloria ba wurin kula da mahaifiyarsa, a cewarsa mata da yawa zasu yi masa alƙawarin kula da ita amma duk a baki ne, idan ya auro su suka shigo gidan ba zasu taɓa yi ba, shi kam yayi imanin abinda zai faru kenan matuƙar yayi gangancin shigo da wata matar cikin rayuwarsa. Tare da haka kuma yayi imanin indai yana raye to watan wata rana zai samu ya kuɓuta daga wannan kurkukun da ƙaddara ta jefa shi ta kuma rufe shi a ciki.