Dr. Ahmad complete hausa novel
Review for the story
The story of Dr. Ahmad Al-Huda Huda is a captivating tale of an extraordinary individual whose intellectual prowess was evident from a very young age. Born in Potiskum, Yobe State, Dr. Ahmad demonstrated remarkable abilities early in his childhood, such as counting and reading complex materials with ease. His photographic memory and rapid learning pace set him apart from his peers, making him a standout student throughout his educational journey.
Despite his young age, Dr. Ahmad's academic brilliance was recognized by his teachers, who witnessed his ability to grasp and retain vast amounts of information effortlessly. This exceptional talent earned him a place in higher learning institutions at a remarkably young age, where he continued to excel, eventually leading him to study medicine in London.
One of the most notable highlights of his career was his successful surgery on conjoined twins, a feat that garnered international recognition. His ability to navigate the complexities of such a delicate procedure at just twenty-five years old showcases his extraordinary skill and dedication to the medical field.
In summary, Dr. Ahmad Al-Huda Huda's story is a testament to the incredible potential of human intelligence and perseverance. His achievements in the field of medicine, especially given his young age, are truly inspiring and highlight the impact that exceptional talent and hard work can have on the world.
Part 1
A cikin ire iren abubuwan da idanun duk wani ma'aboci karatu ko ma'abociyar karatu zasu iya karanto musu, akwai abubuwan da suke ƙunshe da darasi, tsantsar hikima, abin ban tausayi ko abin ban haushi da takaici haka kuma akwai abubuwa na al'ajabi da tsantsar mamaki. Ya ku masu karatu idan kuna tare dani a wannan labari da zan kawo muku na ɗan baiwa "Dr. Ahmad Al-Huda Huda" a cikinsa zaku ji irin baiwa da fasaha irin ta wannan ɗan tahaliƙi wanda baiwar karatunsa da irin ɗimbin ilimin daya tara a ƴan ƙananun shekarunsa abin zai zo muku tamkar al'amara. Da farko dai an haifi Dr. Ahmad a cikin garin Potiskum dake can jihar yobe, tun yana yaro ɗan shekara biyu ya iya ƙidaya wato ƙirge daga kalmar ɗaya zuwa ɗari, haka kuma tun a waɗannan shekarun nasa Ahmad Al-Huda Huda ya iya karatun 1,2,3,4..
A shekarun nan nasa biyu da ɗan motsi a duniya mahaifinsa ganin irin baiwar da yaron nasa yake da ita sai ya sanya shi a makaranta inda wayonsa da hazaƙarsa yasa ya yiwa yara ƴan ajin sa zarra, a saboda haka yayi musu fintinkau. Tsantsar iliminsa da fasaharsa sun fito fili ne ɓaro ɓaro a lokacin daya shiga firamare domin shi Al-Huda Huda kwata kwata baya buƙatar sai uncle ko aunty sunyi darasi a aji sannan zai gane ya fahimta, a'a sam ba haka abin yake ba, shi Ahmadu da an bashi littafi ko wane iri ne to ruwa ta sha, abu mai wuyar shi ne idanunsa su kalli rubutu, da hakan ta faru to sauran zance kuma ya zama tarihi.
A taƙaice dai shi Dr Ahmad irin mutanen nan ne da bature yake kira da "People with a photographic memory" wato mutanen da idan idanunsu suka kalli shafin littafi ko dai wani rubutu a takarda a maimakon su karanta su gane, ko kuma su haddace kamar dai yadda sauran mutane suke, a'a su sai dai idanunsu su ɗauki hoton taswirar shafin nan ya zamto duk wani abu dake jikin wannan shafin to kwakwalwarsu ta riƙe har abada. Yaku masu karatu haka Dr. Ahmad yake a wurin karatu. Wasu daga cikin malaman da suka koyar a makarantun da Dr. Ahmad ya halarta sun tabbatar da wannan maganar, kamar irin su Malam Sanusi wanda ya ɗauki su Dr. Ahmad Al-Huda Huda a babbar makarantar sakandire aji ɗaya wato ss1 kenan, a lokacin da wasu manema labarai suke zantawa dashi kamar haka;
Dr. Ahmad novel part 2
"A shekarun baya ba zan taɓa mantawa ba lokacin ina malamin sakandire ta maza a can Bunyadi, akwai wani lokaci da aka haɗa wata gasa wato quiz kenan, tsakanin babbar makarantar sakandire ta maza, bunyadi da kuma babbar makarantar sakandire ta mata bunyadi.
"A bisa al'ada Ahmad Al-Huda Huda yana daga cikin waɗanda aka zaɓa daga makarantar maza saboda dama yafi kowa kwazo a makarantar, to a wannan lokacin fa yana ss1 ne. Sai na kirawo shi aji na bashi littafin fiziya (physics) na zaɓo wasu maddodi watau subjects nace ya karanta su sosai ya fahimta idan ya gama zan masa wasu tambayoyi a matsayin gwaji saboda gasar da za'a kara da makarantar mata.
"Bana mantawa awa ɗaya na bashi yayi wannan karatun amma abin ban mamaki kawai sai naga yaron nan ya dawo bayan mintuna kamar goma yake cemin malam na gama. Da yake na saba jin irin abubuwan mamakinsa a bakin malamai da sauran ɗalibai ƴan uwansa kawai sai na karɓi littafin na shiga zubo masa tambayoyi amma abin al'ajabi yaron nan babu tambayar da bai amsa ba kamar yadda aka rubuta a shafukan littafinnan, wannan ni ganau ne ba jiyau ba..
Wannan ɗaya kenan daga cikin irin labarun da suke fitowa daga bakunan Malaman Dr. Ahmad. Sannan kuma makaranta su sani cewa shi fa Dr. Ahmad yana da shekaru tara a duniya ya shiga ƙaramar sakandire aji ɗaya wacce ya samu gamawa da ƙarancin shekaru goma sha huɗu, a wannan matakin ne Dr. Ahmad ya fara jan hankalin jama'a tsakanin arewa da kudancin ƙasa sakamakon lashe jarabawar share fagen shiga jami'a da yayi wato jarabawar nan ta JAMB. A cikin maki ko daraja 400 Dr. Ahmad sai daya ciyo 398 biyu kawai ya samu naƙasu, tunda ake wannan jarabawar ba'a taɓa samun wanda yayi mata kaca-kaca kamar haka ba, kuma fa wai yana da shekaru sha huɗu ne kacal a duniya. Wannan ƙoƙari nasa ne ya sa gwamnatin tarayya ta ɗau nauyin fitar dashi can ƙasar ingila a babban birnin landan inda yaje domin karantar likitanci.
Dr. Ahmad novel last part
A shekaru ashirin cif da haihuwarsa Dr. Ahmad Al-Huda Huda ya zama likitan kwakwalwa yana kuma da shekaru ashirin da uku ya fara buɗe kan mutum domin yin tiyata wato abin nufi dai, da wannan ƙarancin shekarun ya zama "CNS SURGEON".
A wani babban al'amari daya faru da Dr. Ahmad lokacin daya yiwa wasu ƴan tagwayen turawa aiki to fa anan ne duniya ta sallamawa wanna ɗan baiwar likitan. Su dai waɗannan ƴan tagwayen an haifesu ne kansu a haɗe da juna, iyayensu ƴan asalin ƙasar jamus ne. A binciken da suka riƙa yi ne akan likitoci game da matsala irin ta yaransu har suka je birnin landan inda Dr. Ahmad yake aiki. Kafin haɗuwarsu da dakta sun zaga ƙasashe masu yawa har dai suka dawo wurinsa, koda yake da farko basu amince su kai wannan ƴan tagwayen ga dakta ba, duba da ƙarancin shekarunsa.
A lokacin da Dr. ya amince zai yi aikin sai ya nemi da a bashi ƴaƴan ya tafi dasu gida domin ya riƙa nazartar yadda yaran suke kafin yayi musu aikin tiyata. Wata rana Dr. yana zaune yana karatu yaran suna zaune a gabansa suna wasa, sai Dr ya lura yarinya ɗaya tayi bacci yayin da ɗaya yarinyar take zaune tana wasa da ƴar tsana. Hakan yasa Dr fahimtar cewa yaran biyu duk da kansu haɗe yake da juna amma kowacce da tata kwakwalwar. Haka Dr. ya saka ranar yi musu tiyata bayan ya samu ɗan lokaci yayi nazari. A taƙaice Dr Ahmad sai da ya zamo zakaran gwajin dafi, domin shine ya zamo likita mafi ƙarancin shekaru, ɗan shekara ashirin da biyar daya taɓa tiyata ya raba kan yara biyu waɗanda aka haifo kansu a haɗe.
Wannan shine É—an gajeren tarihin É—an baiwa Al-Huda Huda rumbun ilimi wato Dr. Ahmad..