Damata hausa romantic novel 

A short review for the story 

"Damata" is a captivating story that delves into the theme of opportunity and how it can drastically change one's life. The protagonist, Mubarak Bawa, narrates his journey from humble beginnings in Kano to a significant turning point in his life.

The story begins with Mubarak's early life in Kwanar Ɗiso, where he grows up with family and friends. After completing his secondary education, he joins the bustling Kantin Kwari market as a shop assistant. Despite the monotonous routine and meager earnings, Mubarak remains hopeful.

A pivotal moment occurs when an Igbo man (Inyamuri) asks Mubarak to help him find a rare piece of fabric for a burial ceremony. Mubarak's resourcefulness and market knowledge lead him to locate the fabric through a fellow shop assistant, Yahaya. The successful transaction with the Igbo man results in a substantial profit, allowing Mubarak to establish his own business.

The story highlights the importance of seizing opportunities and being resourceful. Mubarak's journey from a shop assistant to a business owner is a testament to the impact of determination and quick thinking.

"Damata" is an inspiring tale that encourages readers to recognize and embrace the opportunities that come their way. It underscores the idea that with the right attitude and perseverance, one can overcome challenges and achieve success.

             Part 1

Kowane ɗan adam a cikin wani lokaci na rayuwarsu wata damar takan zo musu, dama ce ta karatu, samun wani abin duniya, dama ce ta kai ziyarar sauke farali, dama ce tayin aure, dama ce ta samun kwangila ko kuwa dama ce ta samun aiki. To haka dai, ko da yaushe akwai damammaki masu ɗimbin yawa da sukan zo wa mutane ta fuskoki da yawa, haka kuma ta siffofin ko sigogi masu yawa. Kowane mutum dake taka wannan doron ƙasar akwai silar cin su da shan su. Haka kuma idan da rai da rabo, idan kuma babu rai to rabo ya ƙare. Sunana Mubarak Bawa wannan labarin da zan baka ya kai mai karatu ban taɓa baiwa kowa shi ba, sai fa yau dana ga ya dace na fito na faɗawa duniya ko akwai wani darasin da za'a iya tsinta a cikinsa.

A farkon al'amari ni Mubarak na kasance mutumin Kano anan cikin wata unguwa mai suna Kwanar Ɗiso dake ƙofar na'isa. Anan aka haife ni na taso duk rayuwa ta da gararambar yau da gobe anan nayi ta cikin ƴanuwa da abokai. Bayan na kammala ilimin sakandire sai mahaifina ya sanya wani yaya na ya kai ni kasuwar kantin kwari, da yake mu gidanmu bamu wani maida hankali a karatun boko ba. Yayan nawa daya kai ni kwari shima ɗin dai acan yake amma ba wurinsu ya kai ni ba, domin shima inda yake ba wai jarinsa bane, yana dai ƙarƙashin wani ne. Wani babban shago ya kaini inda ake siyan kayan sawa kamar su; shaddodi, yadiddika, lesuna kala-kala, atampopi, da materials akan sari. Wannan babban shagon suna siyar da kayayyaki na maza da mata.

A wannan shagon dai na kan fito kasuwa ne kamar misalin ƙarfe tara zuwa goma na safe, da ni da sauran wasu yaran shagon zamu fito da kaya ayi shara a kuma jejjera kayan duk safiya, duk kwastomomin da zasu zo mune zamu tarbe su mu kuma zagaya dasu muna nuna musu kaya, haka kuma muna yi musu bayanin farashin duk kayan da zasu tambaya. Haka kuma idan lokacin tashi yayi mu zamu mayar da kaya mu rufe shago kuma. Kuɗin sallamar mu a kullum naira ɗari biyar ne. A haka na rufa shekara kamar ɗaya, biyu ina aikin yaron shago a wannan babbar kasuwa ta kantin kwari. Daga baya aka yi mana ƙarin kuɗin sallama zuwa naira dubu.

Damata hausa novel part 2 

Bana taɓa mantawa a lokacin dana kai kimanin shekaru huɗu ina kasuwar nan, wata rana na fito a makare daga gida saboda wasu ƴan uzurirrika dasu ka sha kaina ban ƙaraso kasuwar nan ba sai wuraren sha ɗaya na safe. Bayan na shigo cikin kasuwar nan kafin na ƙarasa shagonmu kawai wani mutum inyamuri ya tsayar dani akan hanya. Sauri nake saboda makarar dana yi ban taɓa yin irin ta ba tun daga lokacin da yaya na ya kai ni wannan shagon, amma dai haka na jure na tsaya don nasan baƙo ne. Inyamurin nan yace dani cikin gurɓatacciyar hausarsa 

"Pls ki temekeni de weni abu ine nemenshi anen kesuwa ne. 

Jin haka yasa nace da shi 

"Me kake nema a wannan kasuwar. 

Da Inyamurin yaji haka sai ya saka hannu cikin aljihun wandonsa na jeans ya ɗauko wata leda ya buɗe a gabana duk ina kallonsa. A cikin ledar ya ɗauko wani yankin yadi ruwan bula, wato kalar yankin yadi shuɗi ne wanda ya turu sosai. Sai Inyamurin nan ya ɗaga kai ya kalle ni sannan ya miƙa min ɗan yankin yadin nan ya sake cewa;

"Kinga wannan ne ina nema anen. 

Kaɗa kai nayi nace masa wannan ai tsohon yadi ne an daɗe da gama yayin sa, da wuya a same shi a kasuwar nan. 

Jin haka sai Inyamurin nan ya girgiza kansa yace;

"Na seni yenzu babu wannen keya sose, amma nesan in kin duba sose zaki semo min. Zan siye shi de yewa fa. 

Daga nan dai wannan Inyamurin cikin wannan gurɓatacciyar hausar tasa yayi min bayanin cewa wani tsohon kakansu ne ya mutu a can jihar enugu, saboda haka akwai bikin binne shi da zasu yi, wannan yankin yadin kuma daya bani na samo masa shine ankon kayan da zasu saka a bikin binniyar. A zuciyata ne "hmmm! Wata kwamacalar sai inyamuri kaji wai har akwai wani biki na binne mutumin daya mutu. Da yake a ƴan shekarun da nayi cikin kasuwar nan ta kwari idanu na sun buɗe babu laifi nasan mutane na kuma san takan harkoki, sai nasa wayata na kira wani yaron shagon daban mai suna Yahaya na tambaye shi idan yana kasuwar nan, sai yace eh. A maimakon na tafi namu shagon kawai sai na canza akalata nayi wa shagon su yahaya tsinke. Shagon su yahaya dai shago ne wanda suke ajiyar tsofaffin diloli na kaya. Yawanci idan aka rasa kaya a kasuwa wanda aka jima da dena kawo su, to a shagon su yahaya ake samun su. 

Damata hausa novel last part 

Haka muka rabu da Inyamurin nan bayan munyi musayar lambar waya. Naje shagon su yahaya na nuna masa ɗan yankin nan, bayan yahaya ya duba shi sai yayi magana da maigidansa wanda yace idan an tashi daga kasuwa zasu fito min da wannan yadin daga store. Bayan na jima da komawa gida bayan sallar isha'i sai ga wayar yahaya yana shaida min an samu yadin nan sak kalar da ake nema, ni kuma na kira inyamuri na shaida masa. Da gari ya waye inyamuri yazo kasuwa sai na tambaye shi har yadi nawa zai siya sai yace ai dila biyu zai siya, nayi mamaki kwarai jin yadda zai sayi yadin da yawa, daga nan sai na aje shi shagonmu saboda na san mugunta irin tamu ta ƴan kasuwa, idan wancan shagon suka fahimci irin ribar da zan samu da wannan inyamurin sai su daƙile ni. 

Haka na koma shagon su yahaya ni kaɗai aka yi cinikin dilar yadin nan guda biyu akan dubu arba'in, duk dila a dubu ashirin aka bar min ita saboda tsohon yadi ne. Ko dana dawo ga inyamurin nan yaga dilolin yadin nan sai yayi murna sosai ya tambayeni nawa zan sayar masa, dama na gama nawa lissafin, amma don kar nayi garaje sai ce masa nayi wannan yadin yana da wuyar samu sosai kuma yana da daraja sobada hak... 

"Ki seyer min duka 1.5 na haɗe miki har de kudin laden wahalerki.. 

Inyamurin nan ya faɗi ta hanyar katse min maganar da nake yi. 

Ji nayi abun tamkar a mafarki ko wata al'amara, amma sai nayi sauri na nutsu saboda fahimtar cewa inyamurin nan bai san yanzu wannan yadin bashi da wata daraja ba saboda yayinsa da aka dena. Kasuwanci na bugawa inyamurin nace kawai ya ban miliyan biyu babu komai ana tare, baiyi wata jayayya ba, ya karɓi lambar account ya danno min kuɗi na bashi kaya muka rabu. A cikin zunzurutun kuɗi naira miliyan biyu na cire dubu arba'in na kaiwa maigidan yahaya kuɗin kayansa. 

Wannan damar dana samu daga wurin inyamuri ai tuni na bar wannan shagon da nake aikin yaron shago na kama nawa shagon da jarina mai kauri.. Faƙat!