Bibiyata akeyi novel

"Bibiyata Akeyi" is a suspenseful story set in Ahmadu Bello University, Zaria. The protagonist, Jamila Hashim, is a student who finds herself being followed by a mysterious black Honda Accord. The story begins with Jamila rushing to avoid a heavy downpour after a long lecture. She takes shelter but soon decides to brave the rain to get home, only to realize she is being followed by the same car that has been trailing her for weeks.

Despite her fear, Jamila manages to get a ride home, but the car continues to follow her, heightening her anxiety. She confides in her brother, Jamilu, who contacts a police friend for help. They decide to capture the car's license plate number to report the stalking.

The next day, Jamila and Jamilu spot the car again. Jamilu attempts to record the license plate, causing the car to speed away. After this encounter, the car stops following Jamila, allowing her to regain her peace of mind.

Bibiyata akeyi shiga ta farko

Ahmadu Bello University Zaria

Tuesday, July 13,  2010.

07:30PM

Sauri take ta zubawa iyakar iyawar ta, burinta bai wuce kada wannan baƙin hadarin daya jima a haɗe tun ƙarfe huɗun yamma ya sauko a kanta ba. Tun ƙarfe shida ya kamata ace sun fito daga lakcar da sukayi a wannan yammacin amma da yake lakcaran yana da matuƙar naci awa biyun nan basa isar sa sai ya ƙara, shi dai Dr. Labaran indai zai yi lakca to sai ya wuce lokacin daya kamata ya fita, wannan har ma ya zama kamar wata ƙa'idarsa, yanzu gashi kafin ta samu ta fita bakin gate ma ba ƙaramin aiki bane, uwa uba kuma aje ga batun zuwanta gida. Jamila Hashim na cikin wannan zantuttukan nata na zuci ne taji alamun yayyafi da ƙarfinsa ya fara sakkowa ai tuni ta koma gefe da gudu ta shiga cikin wata rumfa da aka tanada saboda ɗalibai irinta. Rumfar irin waɗannan rumfunan ne da ake tanada domin ɗalibai masu jiran motar ɗalibai ta makaranta ce, dama lokacin da take tafiya ta kusa ƙarasawa bus stop ne, shi yasa ta ƙarasa da gudu cikin wannan rumfar domin ta fake.

Bibiyata akeyi
Bibiyata akeyi pic 1


Jamila Hashim na shiga wannan rumfar kamar dama ita yake jira ai kawai sai wannan yayyafin ya tsuge kamar da bakin kwarya. Kasancewar ruwa ne irin na daminar da tayi nisa hakan yasa ruwan kawai zuba yake babu alamun tsagaitawarsa. Jamila dai tana cikin wannan ƴar rumfar wacce fakewarta a ciki da kuma masu tafiya a cikin wannan ruwan kusan basu da wani bambanci illa iyaka dai kawai kanta ne bai jiƙe ba amma kusan abayar dake jikinta gaba ɗaya ta gama jiƙewa saboda iskar ruwa da take kaɗo shi zuwa gareta kuma dama rumfar iya rufinta na sama ne amma gefe da gefen ta duk a buɗe suke.

Ganin cewar wannan ruwan bashi da alamar tsayawa yasa jamila fara tunanin tafiya cikin ruwan domin ta fita daga gate ta samu ta tare ɗan sawu ta wuce gida. Haka kuwa aka yi, fitowa tayi ta riƙa takawa a hankali kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki, sai dai kuma bata wani jima da fara tafiyar nan ba kawai taji mota a bayanta kamar dai yadda aka saba binta a ƴan satuttukan da suka gabata. A hankali ta juya bayanta domin tabbatarwa kanta zargin da take yi, tana ganin wannan baƙar Honda accord ɗin ai kawai sai Jamila ta ɗiba a guje yayin da ita kuma motar ta cigaba da tafiya a hankali.

Bibiyata akeyi shiga ta 2 

A makaranta mai girma da yawan É—alibai kamar Ahmadu Bello, zai yi wuya a samu rashin gilmawar mutane a kowane irin lokaci ne, komai dare haka kuma koda hutu ake lokacin da babu É—alibai indai kazo gidan Ahmadu to kuwa zaka samu jama'a walau É—alibai, walau masu zama suna rayuwa a cikin makaranta da dai sauran duk wanda yake da alhakin raÉ“ar wannan wuri, to kamar haka ne a lokacin da Jamila ta Æ™arasa bakin wanna gate É—in, akwai É—aiÉ—aikun mutane a wurin. Tsayawa tayi ta kintsa kanta sannan ta koma gefen titi domin jiran É—an sawu. Na farkon daya fara tsayawa Jamila tace masa; 

"Babban dodo..

"Naira É—ari huÉ—u zaki bayar Æ´anmata.

Mai É—an sawu ya Æ™ayyade wa Jamila kuÉ—in da zata biya shi. 

Jamila bata ko nemi ragi ba ta shige saboda tsananin fargabar da take ciki. Daga Æ™ofar gate É—in samaru zuwa Æ™ofar gidansu ko kuma daga Æ™ofar gidansu dake Babban dodo zuwa samaru naira É—ari biyu da hamsin ne idan yayi wuta É—ari uku amma saboda halin É—imuwa haka ta shige É—an sawun nan. ÆŠan sawun da Jamila take ciki ya zo polo roundabout kenan yana Æ™oÆ™arin shiga ciki kawai sai Jamila ta sake ganin wannan motar a gefensu wacce suka shiga wannan shataletalen tare, tuni cikin Jamila ya É—uri ruwa, hankalinta ya kai Æ™ololuwar tashi wanda zuwa yanzu ta tabbatar bibiyarta ake yi, kuma ita wannan motar glass É—inta tinted ne sam ba'a ganin na cikin motar, haka kuma motar a nutse take tafiya. 

Bibiyata akeyi
Bibiyata akeyi pic 2


Wannan lamari yanzu kam ya girmi tsoro, yanzu abinda Jamila take ji game da wannan lamarin ba zata iya misalta shi ba, ita bata taÉ“a ganin tashin hankali irin wannan ba. Sati biyu da suka wuce kullum idan ta fito daga gida zata tafi makaranta to wannan motar kullum tana É—ayan gefen gidansu. Kuma da ta fito taje bakin titi sai wannan motar ta fara tafiya a hankali tana bin ta duk inda tayi, amma duk da haka Jamila bata yarda ita ake bi ba sai da shekaran jiya ita da Æ™awarta Hauwa suka je Amaru karÉ“o É—inkin anko, ganinta anan ne ya tabbatar mata da hasashenta na tabbas wanna motar ita take bi. To amma su wanene suke bin ta? Me suke so? ko kuma me suke nema da ita? babbar tambayar kuma ita ce su wanene ko su wanene a cikin motar? WaÉ—annan sune kwararan tambayoyi guda uku wanda take kwana take tashi dasu. 

Bibiyata akeyi shiga ta 3

A dalilin wannan bibiyar da Jamila ta tabbatar ana yi mata cikin sati biyu gaba ɗaya ta zabge ta fige sai kwala kwalan idanunta da yake manya ne. Duk wanda ya ganta an san a gigice take, haka kuma Baba Tabawa babu irin tambayar da bata yi mata ba akan ta faɗa mata damuwarta amma Jamila tayi ƙememe tace ba komai. Jamila Hashim a yanzu data tabbatar babu wata mafaka dole yasa ta yanke shawarar samun yaya Jamilu wanda yake yayanta ne kuma duka su biyun suna zaune na a ƙarƙashin kulawar kakarsu wato baba tabawa kasancewarsu marayu. Dalilin da yasa Jamila ta ɓoyewa baba tabawa matsalarta kuwa saboda ciwon hawan jinin kakar tasu ne.

Bayan Jamila ta Æ™arasa gida ta kimtsa tayi sallolinta ta kuma ci abinci bata kwanta barci ba har sai da yaya Jamilu ya dawo ta sanar dashi halin da ake ciki anan ya rufeta da faÉ—a kan meyasa ta É“oye har sai yanzu zata faÉ—i al'amari irin wannan. Daga nan bai É“ata lokaci ba yasa waya ya kira wani abokinsa É—an sanda mai suna tukur yayi masa bayanin komai. Tukur ne yace lallai suyi Æ™oÆ™ari su É—auko plate number ta wannan motar dake bibiyar Jamila idan yaso sai a chaje su da laifin stalking tunda dai bibiyarta ake yi har na tsawon sati biyu. 

Washe gari da lokacin tafiya makaranta yayi sai suka fito tare da Jamilu. Suna fitowa daga cikin gida sai Jamila tace masa; 

Bibiyata akeyi
Bibiyata akeyi last pic


"Yaya Jamilu ga motar can, wancan baÆ™ar mai baÆ™in glass. 

Jamilu da jin haka sai yayi wurin motar gadan gadan riƙe da wayarsa a hannu, tun daga nesa ya fara karanta lambar motar, da aka ankare cewa kwafar lambar akeyi ai kawai sai aka take motar a ɗari aka bar wurin dama motar a kunne take. Daga wannan ranar Jamila bata sake ganin motar nan ba, tun tana ɗari-ɗari har ta saki jikinta kamar da can.