Auren kwangila part 1
"Auren Kwangila" follows the story of Sadiya, a young woman struggling to find a job after a series of unfortunate events, including a devastating flood that destroyed her home and claimed the life of her fiancé, Sirajo. Sadiya and her mother, Malama Uwani, are forced to move to Kano and live in a rented house. However, they face eviction as the landlords decide to sell the property.
Desperate for work, Sadiya applies to numerous companies, including Muntari and Sons Limited. The owner, Alhaji Muntari, takes an interest in her plight and proposes a contractual marriage. His terminally ill mother wishes to see him married again before she dies, and Alhaji Muntari needs Sadiya to fulfill this wish. He promises to provide for her and her mother without expecting a conventional marital relationship.
Initially hesitant, Sadiya eventually agrees due to their dire financial situation. The marriage goes smoothly, with Alhaji Muntari honoring his promises and Sadiya maintaining her integrity. Over time, Alhaji Muntari proposes to make their marriage permanent, which Sadiya accepts, leading to a genuine and lasting union. His mother, Hajiya Amina, lives to see her son happily married.
"Auren Kwangila" is a compelling story about resilience, unexpected alliances, and the possibility of finding love and stability in the most unlikely circumstances. It highlights themes of duty, compassion, and the importance of keeping promises.
Kai!.. Wannan wace irin rayuwa ce? Sadiya ta nisa cikin gajiyawa. Idan har bata yi É“atan lissafi ba, yau sati na biyar kenan tana fafutukar neman aikin yi. Ta rasa tudun dafawa, haka kuma ta rasa inuwar da zata shiga ta fake tun sa'ilin da aka kafe musu notis É—in barin gidan da suke ciki suke rayuwa ita da mahaifiyar ta, a sakamakon masu gidan wato magada ko kuma yaran da suka gaji gidan a wurin mahaifin su, sun yanke hukuncin sai da gidan tun bayan da aka raba musu gadonsu.
Wannan gidan kuwa a cikinsa ne Sadiya da mahaifiyar ta Malama Uwani tsohuwar ungozoma suke rayuwa tun sa'ilin da suka dawo garin kano da zama, yau shekaru biyar kenan da dawowar tasu garin kanon dabo sakamakon iftila'i ko annobar ambaliyar ruwa data riske su acan garinsu na Babaldu dake jihar Jigawa. Da yawa daga cikin Æ´an uwan su Sadiya sun rasa rayukansu ne a wannan ambaliyar ruwa da aka yi, haka kuma Æ´an tsirarun cikinsu da suka tsira da rayukan nasu, wannan annobar tayi silar karayar arzikin su, waÉ—anda a cikinsu ne har dasu Sadiya da mahaifiyar ta.
Kasancewar su asalin fulani, mahaifin Sadiya ya mutu ya bar musu shanu masu yawa wanda bayan mutuwar sa ne ƴan uwansa suka hau kan wannan dukiyar tasa ta shanun suka yi wadaƙa ganin cewa bashi da wasu magada tsayayyu. Sadiya ce kaɗai ƴarsa, sai kuma mahaifiyar ta wato uwani ungozoma. Bayan anyi rabon gado ne, a wancan lokacin uwani da ƴarta Sadiya suka yanke hukuncin sayar da ƴan shanun da suka samu a rabon gadon suka sayi gidan zama ragowar kuɗaɗen kuma suka riƙa juya su a ɗan kasuwanci. A haka suke rayuwa har kawo lokacin da Sadiya ta kammala karatunta na diploma.
Sadiya bata jima da kammala wannan karatun nata ba, tsayayyen saurayin ta wato sirajo wanda suke zaune duk a gari É—aya, ya sake bijiro da maganar auren su, kuma dama can akwai maganar auren saboda duka manya daga kowanne É“angare sun san da wannan maganar ta aure tsakanin sirajo da Sadiya. Bayan an sake zama ne an kuma tsayar da maganar auren su a watan maulidi na sabuwar shekara sai kuma kwatsam wata rana suka tashi cikin dare da wannan mummunan iftila'in na ambaliyar ruwan data tafi da gidajen su ta kuma yi silar rayukan mutane da yawa ciki kuwa har da sirajo wato manemin Sadiya wanda aka tsayar da maganar auren su a watan maulidin gobe.
Auren kwangila part 2
Mutuwar Sirajo ta gigita Sadiya ainun, sai dai kuma da yake duk mai rai mamaci ne, haka Sadiya tayi jimaminta ta gama har ta samu ta wartsake daga wannan rashin na masoyin ranta. Da yake wannan ambaliyar tazo musu da ta'adi mai yawa na dukiyarsu, hakan ne yasa da yawa daga cikin ƴan garinsu suka riƙa barin gida suna yin ƙaura zuwa wasu garuruwan domin neman sana'a da kuma canjin rayuwa, ciki kuwa harda Sadiya da mahaifiyarta. Wannan shine silar dawowar su garin Kano inda suka yada zango a unguwar tishama bayan sun samu gidan haya, anan ne kuma suka zauna har suka shekara biyar kafin notis ɗin tashin su daga gidan ya same su, hakan ne ya sake jefa rayuwar su cikin walagigi, hakan ne kuma yasa Sadiya ɗaura aniyar neman aikin yi da kwalinta na diploma..
End of flash-back..
Duk wasu kamfaninka dake kan hadejia road babu wanda bata kai ziyara ba da sunan neman aiki tare da kwalin diplomar ta sai dai kuma kamar yadda ta riƙa gani acan kamfaninka dake unguwar sharaɗa, babu alamar zata samu sa'a.
Tana tsaye ne a bakin get É—in wani kamfani mai suna Muntari and Sons limited. Babban kamfani ne daya shahara wurin sarrafa buhu.
A lissafinta na yau wannan kamfanin shine kamfani na goma sha takwas data kaiwa ziyara domin neman aikin yi.
*****
Kallo ɗaya za'a yiwa Alhaji Muntari wanda ke zaune a cikin katafaren ofis ɗinsa a fahimci irin nisan da yayi a duniyar tunani. Alhaji Muntari dai shine mamallakin wannan mashahurin kamfanin na buhunhuna wato Muntari and Sons limited. Tun daga lokacin da yaga zuwan sadiya kamfaninsa ta cikin na'urar cctv da kuma abinda yake tafe da ita watau neman gurbin aiki ko wane iri ne, da kuma bayanin da sakatare yayi mata na cewar a yanzu haka basa buƙatar sabbin ma'aikata, babu wani abu da bai ji ba dangane da wannan tattaunawar tasu. Haka kuma ya fahimci irin matsanancin halin da ita yarinyar take ciki.
Katse wannan tunanin nasa yayi fahimtar cewa babu inda zai kaishi sannan ya jawo wayar tarho ya danna kira, sakatarensa Idi na É—aga kiran, sai Alhaji ya umarce shi lallai a nemo wannan yarinyar da tazo neman aiki. Hakan ne yasa Idi sawa a fita a nemo masa ita tunda yana tunanin ba tayi nisa ba. Cikin sa'a kuwa sai gashi yaron da aka tasa ya nemo Sadiya sun shigo ofis É—in sakatare tare daga nan Idi ya shaidawa maigida cewar an nemo yarinyar, Alhaji Muntari bai É“ata lokaci ba yace a shigo da ita.
Auren kwangila part 3
Haka Sadiya ta shiga katafaren ofis É—in Alhaji sai raba idanu take. Bayan ya umarceta ta zauna daga nan yayi mata bayanin duk abinda ke tafe da ita, Sadiya ta nisa tace haka ne. Sai Alhaji yace wa Sadiya to me zai hana mu haÉ—u su magancewa juna matsalolin mu. Jin haka ne yasa Sadiya ta kalli Alhaji haÉ—e da watso masa tata tambayar;
Kai kuwa wace matsala ce da kai wacce zan iya maka maganin ta ? Ta tambaye shi cike da mamaki.
Murmushi Alhaji Muntari yayi sannan yace mata;
Mahaifiyata bata da lafiya, likitoci sun tabbatar min ba zata tashi daga cutar da takeyi ba, sun ma ƙayyade cewar ba zata haura wata uku nan gaba ba. Burin mahaifiyata shine taga na sake yin aure kafin ta rasu. Ki yarda muyi aure wata uku wato auren kwangila, bayan mahaifiyata ta rasu sai na sahale miki. Ni kuma nayi alƙawarin zan wadata ki da komai haka kuma babu abinda zai shiga tsakinin mu dake har sai idan ke kike buƙatar hakan. Nasan za kiyi mamakin mai yasa zan miki maganar aure a haɗuwar mu ta farko ba, to ni kaina ban san me yasa hankalina ya kwanta dake tun sa'ilin da kika shigo ba har kuka yi magana da sakatare na. Wannan shine dalilin da yasa nace a kirawo ki kenan.
Ko da Sadiya taji maganganun Alhaji sai tace za taje tayi tunani tukunna.
A haka suka rabu. Bayan taje gida ta samu Uwani mahaifiyarta da magana, sai dai kuma bata samu goyon bayanta ba kasancewar lamari na aure ba abin wasa bane. Haka dai suka ci gaba da saƙa da warwara har dai ya zamto baifi saura ƴan kwanaki ya rage musu su tashi daga wannan gidan hayar ba. Sai fa a sannan ne Uwani ta amince Sadiya ta bayyanawa Alhaji Muntari amincewarta.
Daga samun amincewar Sadiya zuwa bikinsu da Alhaji gaba É—aya abun baifi sati É—aya ba, da yake Alhaji kuÉ—i ba matsalarsa bane. Mahaifiyarsa kuwa, hajiya Amina tafi kowa farin cikin ganin É—anta ya sake wani auren tun bayan shekaru shida da rasuwar matarsa.
*****
Kamar yadda kowane aure yake cike da ƙalu bale to hakan ce ta kasance da auren kwangila wanda Alhaji Muntari yayi tare da amaryarsa Sadiya. Koda yake daga ɓangaren ma'auratan babu matsala, saboda ta ɓangaren alhaji, Sadiya ta same shi mai cika alƙawarin, saboda ya ɗauke musu duk wani nauyi ita da mahaifiyarta haka kuma babu wani abu da yake shiga tsakaninsu ta fuskar auratayya. Ita ma Sadiya tunda suka yi wannan auren, Alhaji Muntari yakan yi ajiyar kuɗaɗe masu yawan gaske a ɗakinta amma haka zai dawo ya ɗebi kuɗaɗensa ba tare dako sule ya ɓata ba. Irin wannan riƙon amanar da kuma kauda kai daga abin hannunsa daya ga Sadiya nayi ne, wata rana ya same ta da maganar shi kam lallai idan so samu ne, to me zai hana auren su ya tashi daga auren kwangila ya koma auren mutu ka raba takalmin kaza. Nan da nan Sadiya tayi na'am, Alhaji kuwa yafi ta farin ciki ganin ya samu mace mai riƙon gaskiya da amana.
Mahaifiyar Alhaji kuwa, Hajiya Amina bata mutu ba har sai da taga tilon ɗanta ya nutsu cikin aure kamar yadda take buri... Faƙat!