Inna kakar maigida tazo zaman wanka wanda tsofaffi ke zuwa idan anyi sabuwar haihuwa, gidan jikinsu ko kuma wani nasu. Kamar yadda aka saba sai ga inna ta dawo gida riƙe da leda a hannu. ta shiga, ta ajiye ledar sannan ta nufi kujerar da Abdallah ya zauna, ta danna hannunta a kan kujerar. Sannan ta taɓa wajen da matarsa ta zauna, ta taɓe baki, sannan tace:
"Halima, kinga abinda nake faɗa miki kullum ko? Da kince mutanen-nan su zauna a ƙasa. Wallahi, ba kiga yadda kujerar-nan tabi ta faɗa ba, gaba ɗaya ta lotse! Ji nayi har katakon cikinta yana fidda wani sauti, musamman wajen da Sojojo ya zauna. Duk da haka, an kawo kaya masu tsadan gaske." Ta faɗa tana cigaba da taɓe baki, sannan ta zauna a ƙasa ta fara fito da kayan jarirai kala kala daga cikin ledar, kayan masu kyau da tsada har da kuma atamfofi.
"Kai! kai! kai! Tabdijam!! Ashe dai Sojojo yana da kuÉ—i. To, Allah ya amfana." Sadiya har lokacin bata ce komai ba saboda wani lokacin abinda Inna take yana É—aure mata kai. Ta gaji da wannan zaman wankan da tazo yi gida gaba É—aya.
"Yo, kiyi magana mana kika ƙyale, duk ɗaya ne. Amma kiga wannan kayan da suka kawo miki kamar bashi suka dakko. Kinga matarsa ma tsohon ciki gareta, dole idan ta haihu kema ki rama mata." A dai-dai nan Imran ya shigo da sallama, cikin haushin abinda yake ji.
"Imran, kaga abinda_Sojojo_ya_kawo_maka. Wallahi, kai da karambani_kake. inba karambanin_akuya ba mai ya kaita leƙa ɗakin_kura! Ina kai, ina wannan mutum. Yanzu, ace ka rasa aboki sai wannan ƙaton abu kamar himin kaya! Ina abokinka Abida? Tun ranar daya kawo mu, shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Amma wannan Sojojon da kuka haɗa alaƙa.
Imran bai ce komai ba, ya shige bedroom, saboda haushin Inna da Sadiya suna damunsa.
"Kaga aniyarka Imran! Wato ƴaƴan naka kake yiwa baƙinciki saboda an kawo musu kaya. So kake ya bayar da kuɗi, ka ɗauka kayi wuf dasu, ko? Har yau babu sadaki babu dalilinsa. Ka ɗauki ƴar mutane ka mata juna biyu, ta haifa maka ƴaƴa har biyu, amma har yau babu ragunan suna! Ga lokaci na wucewa. Sai dai ka kawo wani ɗan nama a ƙaramin leda wai name jego ne. Yo, wane irin me jego ita da za'a kawowa raguna masu ƙarfi? Mun_gaji da gafara_Sa ba_muga_ƙaho_ba!"
Babu wanda yace komai. Imran ya shige É—aki ya kwanta, yana ta jiyo muryar Inna, yana kuma tunanin abinda ya kamata.
"Oh ni Ashrofa! Sai kace an aiki bawa garinsu! Tunda tace zata je gidan ƙawarta amma har yanzu bata dawo ba."
"Me zata miki idan ta dawo?"
"Haba Halima, har na rasa abinda zata min. Yunwa nake ji."
"To, ki zubo abinci mana."
"A'a, ni ba shinkafa zanci ba. Inaso ta dawo ta dafa mini indo momi (tana nufin indomie). Taliya ta yara akwai daÉ—i wallahi." Sadiya ta kalleta kawai bata ce komai ba.
DARE
Tunda ya kwanta, Imran yake juyi a katifa, yana ji kamar ya fitar da Inna daga gidan ya kulle ƙofar. Gaba ɗaya yau ba ya jin jikinsa dai-dai. Yana zaune da tagumi, yana jin mararsa tana murɗawa. Ya daɗe a haka har ya tashi ya leƙa bedroom ɗin. Fitilar a kashe, amma ɗakin bai yi duhu sosai ba saboda hasken farin wata da ya shigo ta gefen labule. Babu abinda kake ji sai ƙarar numfashi a ɗakin, Inna ce ke shirga munshari.
Wannan yasa ya É—anyi lalume har ya isa wajen gadon. Tsaye yake yana ta tunanin yadda zai gane matarsa. Yanzu kowacce na iya É—aukan bargon É—aya ta rufa, kuma suna iya canjin wurin kwanciya.
Yar zaman wanka part 2
Ya hau gadon saida ya zauna a tsakiyarsu, yana ƙoƙarin gane matarsa domin ya tashe ta bashi magani. Kunne ya kai kusa da bargon domin ya tantance ina Sadiya. Amma kowacce ta rufa ne har kanta. Ya mika hannunsa kusa da bargon ya buɗe hannun wanda ke cikin bargon, ashe Inna ce! Wani juyi da tayi ya tsorata Imran, ya ɗauka zata tashi ne, Idan kuwa ta ganshi a tsakiyarsu, tabbas za'a samu matsala. Da sauri ya zame yana ƙoƙarin fita daga ɗakin.
Ya dawo falo cike da haushi da wani mugun takaici. cikinsa har yanzu yana ciwo, sannan ya kunna fitilar falon ya fita zuwa kicin.
"Kai da matarka amma sai kake tsoron tashinta kamar wani barawo" ya faɗa a zuciyarsa. Ya ɗakko jar kanwa, ya jiƙa yasha domin rage ciwon cikin. Haka ya dawo ya kwanta, yana jin ɓacin rai. Ya so ya shirya wani abu cikin daren, amma rashin kuzari da nutsuwa ya hana shi. Haka ya kwanta yana cewa, "Wata rana za'a haɗu."
WASHE GARI
Kamar kowace rana, yau-ma haka Inna ta shirya ruwan wanka. Cikin ikon Allah, ta gama wanke Hassan amma bai farka ba, sai data shirya su tsaf kamar yadda ta saba.
DA YAMMA
Suna zaune a falo, Ashrof, Sadiya, da kuma Inna. Imran ya fita baya nan. Ana yi musu sallama, Ashrof ta amsa, data leƙa sai taga Abid ne.
"Ya Abid, ina wuni?"
"Lafiya ƙalau, Ashrof. Mama, ina Hajiya Inna?"
"Mama tana gida, Inna kuma tana ciki. Ina nemanta kake?"
"Kamar kuwa kin sani, saboda ita nazo. Kice tana nan ana shan zaman."
"Eh," cewar Ashrof tana dariya.
Tare suka shigo da Abid, Inna na ganinshi ta fara murna tana cewa, "Lale da Abid, sannu da zuwa."
Shima dariya yayi, ya zauna yana gaishe da Inna. Suka gaisa da Sadiya. Ya tambayi kwanan yaran, aka bashi amsa da lafiya ƙalau.
"Wallahi abubuwa_ne suka É—ansha kai_na, ban samu_dawowa_ba. Na ga yaran ba."
"To wane gani kuma kai da muka dawo da kai daga asibiti dasu," cewar Sadiya tana murmushi.
"Haba Sadiya, ke meyasa kike haka ne? Ai idan ance za'a ga mutum ba wai gani na ido ake nufi ba. Baki ga Æ´an siyasa ba ko masu kuÉ—i? Idan Æ´an maula suka je wurinsu, sai suce zan ganka zuwa gobe. To, ai suna nufin zasu sallami mutum da wani abu." Inna ce ta tsoma baki tana kallon Sadiya. "Sadiya_ba kiga_irin_maganganun_Abid ba."
Yar zaman wanka last
Sadiya tayi yatsine da fuska, tana yiwa Inna kallon irin, "Meyasa haka?" Ashrof kuwa kunya ce ta rufeshi gaba É—aya.
"Kai, rabu da ita Inna, ai gaskiya kika faɗa," cewar Abid yana dariya. "Dama irin ganin da nazo musu kenan," ya ƙara da dariya.
Ya miƙa mata manyan ledoji guda biyu. "Ga wannan_kiyi_amfani_dashi_Inna, nakine, wannan_kuma_na_jarirai."
"Ayyiriri! Taɓɗi! Yau ake yinta," cewar Inna tana ta murna tana ɗaukar atamfa.
"La, ba komai Inna. In ba a kyautata wa tsofaffi ba, wa za'a yi wa?"
"Kai dai kasan haka amma Imrana yaron nan baya fahimta."
Shi Abid ya cigaba da dariya yana cewa, "Inna, ni dai naga na ƙaunaceki sosai."
Inna kuwa ta cigaba da zancen abubuwan da suka faru a cikin gidansu da Imran, tana cewa, "Wallahi fa, ranar daka kawo mu daga asibiti, sai dana kwana a ƙarƙashin gado."
"Subhanallahi! A ƙarƙashin gado fa kika kwana Inna?" Ya tambaya cikin mamaki.
"Haka fa! Sanyin_garin_nan yasa_na_kwana a ƙasan_gado. Ba wai saboda rashin wuri ba, kawai sanyin garin ne ya sanya haka." Ta ƙara faɗa tana gutsirar goro.
Abid ya yi dariya sosai, ya ce, "Lallai sanyi bai kyauta ba. Amma dai gaskiya abin dariya ne."
"Sanyi fa, kai kaɗai ba zaka gane ba. Bugu da ƙari kuma Hassan ya dawo da wata baiwa a jikinsa. Haka kawai yaro ya koma tamkar miciji!"
"Miciji kuma Inna?" Abid ya tambaya cikin mamaki dayin dariya.
"Eh_mana, ai_washe_gari bayan_haihuwarsa ya_canza_ya_koma_miciji_da_kan_mutum. Amma saboda rashin imanin Imrana, haka ya garƙame ni da miciji a ɗaki. Nayi ta neman ɗauki amma ban samu ba har na gaji. Sai da na rinƙa karanta addu'a."
Dariya kawai Abid yake yi da jin labarin. Yasan dai akwai abinda ya shige tsakanin Inna da Imran, domin duk abinda ke faruwa ba ƙaramin ƙarairayi bane.
"To, Abid, ga wannan," cewar Inna tana ƙara ɗanɗanar goronta da Abid ya kawo mata.
"Lallai kuwa, Inna, babu kamarki. Amma ki ƙara hakuri da halayen Imran, duk da cewa ina ganin akwai wata matsala tsakaninku," Abid ya ce da murmushi.
Inna tayi dariya kadan, tace, "Ai ba abinda Imrana zai yi ya shige min, ni dai ina so kawai naga yana da kyakkyawan hali."
Suka cigaba da hira, suna dariya da tattaunawa kan abubuwan da suka faru a gidan.
Ita dai Sadiya tunda inna tazo zaman wanka tabi ta isheta, kuma ita ba abin tace ta bar mata gida ba, haka Imran da Sadiya suka cigaba da hakuri har inna ta gama zaman wankan jarirai ta koma gida.