Tayi min kankanta complete hausa novel

Tayi min kankanta complete hausa novel and review 

Tayi min kankanta complete hausa novel

Tayi Min Kankanta, written by Nabila Ahmad, is a novel that looks at love, arranged marriages, and the challenges of living in modern times while following Hausa traditions. Nabila Ahmad dedicated this story to her online readers.

The story follows Lailah Hassan, a young woman whose family arranges her marriage to Kamal, a wealthy man. Neither of them knew about the arrangement before it happened. Lailah, who already had feelings for Kamal, must now navigate life as his wife, even though Kamal was not initially interested in the marriage. The novel explores how their relationship grows over time.

Key Characters:

- Lailah Hassan: The main character, dealing with her arranged marriage and her feelings for Kamal.

- Kamal: Lailah’s husband, who starts off not wanting the marriage but eventually grows to love her.

- Zahra: Lailah’s sister, who supports her through the changes in her life.

- Aliyu: A man who loves Lailah, but she does not feel the same way about him.

- Engr. Hassan: Lailah’s father, who represents the older generation and their beliefs in arranged marriages.

The story focuses on how arranged marriages work in Hausa culture and how love can grow between two people even if they didn’t choose to marry each other. It also shows the pressure that families can put on individuals when making big decisions like marriage.

The novel is written in Hausa and is available for free online, with a hard copy for those who prefer to read offline.

Final Thoughts:

"Tayi Min Kankanta" is a great read for anyone who enjoys stories about love, family, and traditions. It’s a touching story about how Lailah and Kamal learn to build a life together, even though they didn’t choose each other at first. Nabila Ahmad has created a relatable and heartfelt story that many will enjoy.

English Excerpt:

"She was an 18-year-old girl, fair-skinned with striking features — sharp nose and a small mouth. She walked with grace and calmness, even though signs of hunger were evident. Despite this, she remained composed, showing dignity and energy. This was Lailah, a well-mannered girl admired by everyone in her neighborhood. She was of medium height, well-built, and had a figure any man would dream of. Unfortunately, despite her beauty, she had no boyfriend, unlike her peers."

The story follows Lailah, a beautiful and intelligent young woman, as she navigates life and encounters arranged marriage prospects. The narrative explores her growth and the people around her, including her father, who prioritizes her education over everything else, and Aliyu, a young man secretly in love with her. Through Lailah’s journey, the novel highlights societal expectations, personal aspirations, and the clash between modernity and tradition in relationships.

Tayi min kankanta complete hausa novel (part 1)

The first part of the gives background of the story, how Lailah living in her area with her family and her daily activities.

A koda yaushe burin wannan gida namu na tsamiyanovels shine jindadin maziyarta. A yau mun kirkirar muku sabon hausa novel complete mai suna tayi min kankanta. Wannan labari namu dauke yake da soyayya, juriya, da kuma ilimummukan rayuwa a koda yaushe muna fatan mu samar maka da abinda zaka ji dadinsa. Asha karatun tayi min kankanta complete hausa novel lafiya!!.

Yarinya ce yar shekara goma sha takwas fara jajir da ita, me kyakkyawan tsinin hanci gamida dan Æ™aramin baki. Tafiya take cikin hankali gamida nutsuwa duk da cewa alamu sun cewa yunwa take ji, amma hakan baisa ta fita a hayyyacinta ba. Domin kota ina ka dubeta cike take da kamala da kuma kuzari. Lailah kenan yarinyar kirki wacce kowa a unguwa ke yabo. Budurwa ce mai matsakaicin tsayi sannan gata da diri wanda kowane namiji zai so ya samu irinta. Gaba da bayanta ta gama haduwa, sai dai kash! duk da wannan kyau nata ko irin saurayin nan da yan-mata ke danyi ita bata dashi. 

Dalilin kuwa ba wani abu bane illa mahaifinta wadda ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da yarinyarsa tayi karatun boko dana zamani. Sau da yawa samari a makaranta na nuna mata tsantsan so da kauna amma ko kallo wani lokacin basu isheta ba, ba wai domin raini ba, domin itama tana son namiji tamkar kowace mace. Sai dai bata bukatar ta fara soyayya har hakan ya shafar mata karatun. 

Lailah Hassan kenan wacce itace jarumar wannan labari na tayi min kankanta complete hausa novel, haka ta cigaba da tafiya ta tunkari kofar gidansu. Gida ne shima matsakaici me kyau na masu rufin asiri sosai, domin yasha siminti samfurin kalar zamani, yanada karamar haraba gamida sit-room guda biyu ta waje. Sannan kuma nada Æ™aramin gate wanda mahaifinta ke ajiye mota ta ciki. 

Da zuwanta ta shige gida, tayi sallama, mamanta ta amsa. Suka yiwa juna murmushi, welcome home my daughter, thank you ma ta yiwa mamanta martani. Ta wuce dakinsu ta kimtsa sannan ta fito, ga abincin ki, ta amsa sannan tayi godiya ta koma dakinsu. Mama ina Zahra? yanzu na aike ta siyan kayan miya cewar maman. Jarumar tayi min kankanta complete hausa novel ta saka ki daki domin cin abincinta.

Salama alaikum: sallamar Zahra kenan kanwar Lailah ta shigo da bakar leda a hannu, da alama kayan da aka aiketa siyane ciki. Mama wallahi wai babu attaruhu sai an kawo mata zuwa anjima zata turo miki. Amma Zahra me nace miki? inji mama. Zahra tayi shiru; uhm cewa kika yi idan babu attaruhu ko tattasai kada na siyo, amma Mama an samu tattasai ai. Hararanta Mama tayi sannan ajiye min kije kitchen ki dauki abinci. 

Fuska cike da tsoro ta nufi kitchen, kafin ta karasa, taji kiran Lailai, Zahra! Zahra! ai fasa shiga tayi kitchen domin dama so take ta samu inda zata huce. Gani! ta fada cikin muryan raini, wai ke kullum sai na gaya miki ki daina doramin takalmin makaranta akan jaka. Akwai Alkur'ani a ciki fa, toni na sani ne anti, ni bamma san akwai Alkur'ani a ciki ba. Bazan kara ba, Zahra bata jin magana domin ba dan maganar Alkur'ani aka yi ba, to da yanzu ta soma yi mata rashin kunya. Zahra na matukar son yar uwarta Lailah sai dai kuma yar tsama wacce ba'a rasa ba.

Zahra na matukar ji da Lailah sakamakon ita ke share mata hawaye amma duk da haka wani lokacin ta raina ta. Wannan ba wani sabon abu bane tsakanin yaya da mai binta. Haka Lailah tace kizo muci abinci, a'a mama ta zuba nawa daban cewar Zahra. Shikenan yar mama aci lafiya. Bayan jarumar tayi min kankanta complete hausa novel ta gama cin abinci ta fito tayi wanka sannan suka shirya domin wucewa zuwa islamiyya.

Bayan sun gama kimtsawa suka kama hanyar makaranta. Tunda suka fito samarin layi suka saka musu ido, sake take da dogon hijabin islamiyya wanda ya rufe ko ina a jikinta, amma ba kwalliya a fuskan sabida hukumar makaranta ta hana, duk da dama ita ba ma'abociyar yawan yin kwalliya bace. Amma da yin kwalliyarta da rashin kwalliyar duk daya domin kyawunta dole ya sule ka, kai idan bata yi kwalliya bama tafi kyau. 

Wasu samari dake gefe, Sulaiman ya kalli Aliyu, mutumina ga mutuniyar fa, juyowa Aliyu yayi yace wacece? Lailah mana, ah haba! gasu nan zasu wuce. Nan Aliyu ya kurawa Lailah ido tamkar zai hadiyeta. Su dai tafiyarsu kawai suke bama su kula da kowa ba. Jarumar tayi min kankanta complete hausa novel tareda da ƙanwarta basu tsaya ko ina ba sai islamiyya.

Aliyu yaro ne nutsattse, kuma mai hankali wanda a yanzu haka ya haura shekara ashirin da daya, amma duk duniya ba wacce yake so irin Lailah wannan soyayya dake zuciyar Aliyu dadaddiya ce tun tana yarinya yake sonta, sai dai saboda shakka bai taba koda kusantarta da wannan batu ba. Kullum haka yake fama da sonta amma zurfin ciki kawai yake.

Bayan an tashi daga makaranta kamar yacce aka saba, jarumar tayi min kankanta novel da Zahra suka kamo hanyar gida. Suna cikin tafiyar ne sai Lailah ta hadu da wasu kawayenta suka tsaya hira ita kuwa Zahra data gaji tayi tafiyarta gida. Haka ta baro Lailah, Lailah data duba bata ga Zahra be, nan take tasan tayi tafiyarta. Lailah ta kama hanyar komawa gida, sai taji anyi mata sallama daga baya.

Ta juyowarta sai taga Aliyu, Lailah tasan Aliyu amma maganar soyayya bata da sani, ya kalleta cike da nutsuwa Lailah barka da dawowa. Ta amsa yauwa suka gaisa, tace masa "lafiya" cewa yayi " inason nayi magana dake ne" tace ok, ba matsala ina jinka. Aliyu bai boye komai ba, haka ya sanarwa Lailah cewar yana sonta. Nan take taji ta kamu da tausayin Aliyu, amma sai ta dubeshi tace "gaskiya kayi hakuri" bata ƙara cewa komai ba tayi gaba abinta.

Aliyu ya tsaya a kan hanya ƙiƙam tamkar wani gunki. Sai kuma ya kama hanyar shagonsa. Lailah tasan Aliyu farin sani amma bata taɓa tsammanin irin wannan batu daga gareshi ba. Itama tana yabawa dashi amma gaskiya bata taba jin tana sonsa ba, asalima ita ba wanda ta taɓa soyayya dashi. Sai dai a lokacin da tana karama anyi na wasa.

Tun daga wannan rana ta manta da wani maganar Aliyu, ta cigaba da rayuwarta yadda ta saba. Aliyu dai yana bakansa domin har yanzu yana tsananin sonta. 

Tayi min kankanta complete hausa novel (part 2)

Acan wata rayuwar kuma, wani dan attajirai ne mai suna Kamal, wanda shi a rayuwarsa bai san menene so ba, balle kuma kauna. Domin shi a rayuwarsa kwata -kwata ba zancen wata aba wai ita soyayya. Domin shi ba abinda ya sani illa karatu sai kuma neman kudi. Idan kaga baya makaranta tofa yana kasuwa, idan ko har baya kasuwa to ya tafi wani uzuri mai muhimmanci. Gaba É—aya ilahirin rayuwarsa mata basa gabansa domin shi tunaninsa mu'amala da mata bashi da amfani domin ba zaka taba cika burinka da rayuwa. Aliyu ya tara da kansa kuma iyaye sun tara masa kudi gida da waje. Su biyu a wajen mahaifansu shi da yar uwarsa Zainab ita kuwa tuni anyi mata aure. 

Hanzu haka wannan jarumi na tayi min kankanta novel wato Kamal ya cika shekaru talatin da biyu amma ko niyya kula yan-mata baya yi balle kuma yin aure. Mamansa tayi har ta gaji, Alhaji yace ta rabu dashi. Babban abun mamakin ma shine Kamal lafiyarsa kalau ba wani larura ta É—a namiji dake damunsa, kawai tsarinsa ne a haka. Idan an nuna masa wannan yace tayi min girma idan an nuna masa waccan yace tayi min kankanta haka yake fama. Kuma duk yana yin hakan ne domin a rabu dashi yayi rayuwar. 

Maganar tarbiyya kuwa ba'a nuna masa domin  baya yin abinda ya saba tarbiyya da al'adar malam bahaushe, yanmata da yawa suna son su shawo kan Kamal amma ina!!! Musamman yan uwansu mata, wato nephews dinsa amma ko tunkararsa basa iyawa. 

Kamar yacce Kamal ya saba fita da safe an wanke masa fitacciyar motarsa kirar GLE 43 AMG ya dau wanka kamar yacce ya saba ya fito domin gaishe da ummansa, suna hada idanu tayi masa dariya, kai babban mutum irin wannan wanka haka ko dai nayi sirika ne? Kamal murmushi yayi ya sosa keya sannan yace "Hajiya wallahi zanje kasuwa ne kayana sun sauka" ok, kayan da kace kayi order taga China. To Allah ya kiyaye hanya sai ka dawo, yace ameen. 

Yacce iyayen Kamal ke girmamashi yadda kasan wani ba É—ansu ba, hakan kuwa ya samo asali sabida biyayyarsa ga mahaifansa. Idan ka tarar dasu suna hira kuwa kace abokai ne. 

Alhaji wato mahaifin Kamal yau kwanansa biyu a Saudiyya, sai ga kiransa a wayar Hajiya, ta amsa bayan sun gaisa yake gaya mata yayi wani mafarki mai ban tsoro. Wallahi mafarki yayi ya mutu bai ga jikansa na gun Kamal ba, dan haka duk yacce za'ai ta nemowa Kamal matar aure ba tareda saninsa ba. Haka suka tattauna sosai ta fahimci abinda mijinta ke nufi. 

Nan fa Hajiya tace yau na sami abinda nake so, dama Alhaji ai kai ka hana daba tuni mun masa aure ba. 

Kwana uku da suka gabata Hajiya taje super market domin siyayya, anan taga abun mamaki wasu yaran mata ne su biyu kyawawa tareda mahaifinsu ta fahimci hakan ne saboda yaran na kama dashi, suka je shopping idan kaga yacce keda nutsuwa gamida tarbiyya kaso wallahi ka haifi irinsu, domin ko basu san mutum ba, yanzu zaka ga sun gaishe dashi cikin girmamawa.

Hajiya ta É—an sha wata karamar kwana tana duba kaya, kawai sai suka ci karo da Lailah, da haduwarsu Lailah tace mata ina kwana, Hajiya daÉ—in wannan abu ba kadan ba, domin tunda ta shigo cikin super market din babu wani mutum da yayi mata magana sai Lailah. Lokaci guda taji kaunar yarinyar cikin ranta. Ta amsa da lafiya yan-mata ya gida, saiga baban su Lailah shima suka gaisa, sannan kowa yayi nasa wajen.

Hajiya ta cigaba da zaben kayanta, sai ta jiyo muryar Zahra na cewa "Abba baka siyamin abayar ba" yace yanzu munyi siyayya da yawa ki bari sai wani lokaci. Zahra ta bata rai, kamar an cewa Hajiya tazo. Duk abinda yaran nan suke so su dauka zan biya kudin, yace sun gode wallahi. Cewa tayi nasan kafi Æ™arfin hakan amma dan ka bari nayi musu nima ai jikokina ne. 

Da kyar Mahaifin su Lailah ya yarda, amma Lailah bata dauki abu ko guda ba, sai Fatima uwar rigimar tayi min kankanta novel. Suka yi godiya. Itafa Hajiya sai taga kamar tasan fuskar mahaifin su Zahra. Take tambayarsa kana aiki a Urban development ne, cikin mamaki yace "eh" amma ya akai kika sani? 

Ni naga kamar na taba ganin fuskarka wani waje ne, nan take gaya masa an Alhajinta ya taba yin wata kwangila baya da wajen shekara biyu kenan shine ya nuna mata hotunan ayyukan ginin da suka yi. Anan ne naga hotonka shiyasa naga kamar na taba ganinka. 

Har ta karba lambar baban su Zahra wai akwai wani project da zata neme shi idan ya tashi. Amma a zancen gaskiya ta karba ne saboda Lailah. 

Bayan sun gama waya da Alhaji tace "yau ga rana tazo Allah ka cika min burina" yanzu babban burinta shine ta san duk hanyar da zata bi domin hada auren danta da Lailah. Wato tauraron tayi min kankanta complete hausa novel Kamal. Kiran wayar baban su Lailah tayi Engr. Hassan ta nemi su hadu a ofis dinta, ai ko bai yi gardama ba. 

Ba tareda wani shakka ba, ta gabatar da bukatarta gareshi. Engr. Hassan wayayyen mutum ne kuma yasan Alhaji, kuma ya shaida cewa Alhaji mutumin kirki ne, kuma ga arziki. Nan ya amince amma da sharadin dole yarsa zata cigaba da karatu koda a gidan mijinta ne sannan kuma sai idan tana son Kamal.

Tayi min kankanta complete hausa novel (last part)

Abu kamar wasa suka hada shiri, domin sun kara haduwa a super market ne tareda yaran, inda ya basu dama su raka Hajiya gidanta saboda yanzu ita abokiyar kasuwancin babansu ce. Lailah da Zahra sunyi murna sosai da shiga wannan katafaren gida, wanda za'a iya kira da aljannar duniya. sun yi yawo ko ina har dakin Kamal saida Hajiya ta basu dama suka shiga. A lokacin Lailah na shiga taci karo da wani hoton kyakkyawan saurayi lokaci guda taji zuciyarta ta buga da karfi. 

Har suka dawo tana tunanin wannan fuska data gani a hoto, daren ranar da kyar tayi bacci saboda tunanin wannan fuska. Bayan bacci ya dauketa nan fa tayi kyakkyawan mafarki wai gata nan ita da ya'yanta suna fadin Ummah! Ummah! wasa sosai cikin wani katafaren gida. Saiga wannan saurayi ya shigo sai ta farka daga barci. Zahra ce ke kwala mata kira wai ta tashi tayi Sallah.

Kamar ta hauta da duka amma ina, abubuwa da yawa suka tsayawa jarumar tayi min kankanta complete novel, ta rasa inda zata saka kanta. Shin wai shine mijina? tambayar data kasa bawa kanta amsa kenan.

Kwana biyu yarinya duk ta canja, mamanta tuntuni tasan komai nan ta saka ta a gaba. A hankali ta shawo kan diyarta ta fada mata gaskiya, Wallahi mama na fada soyayya da wani wanda ban san shi ba. Nan ta gaya mata duk abinda ya faru babansu yace su raka Hajiya gidanta. Maman wani murmushin farin ciki tayi domin burinsu zai cika. Ta lallabata da cewar ta dinga yawan addu'a saboda auren irin wannan ya'yan manyan sai dai ƙaddarar Allah.

Yarinya bata san hawa ba bata san sauka ba, ta dinga ganin mutane daban daban suna zuwa gidansu. Daga baya kuma taji wai anyi mata aure aka sha biki aka kai amarya gidanta. Duk abinda ake fuskanta a rufe bata san cikin ina aka kaita ba. Amma wani gida ne na gani na fada tamkar a ƙasar Qatar aka shiga da ita.

Ta bangaren ango shima ji yayi wai masa aure a bakin Alhaji da Hajiya domin Alhaji tun a satin farko ya dawo. Shi Kamal da safe kullum yake fita yayi tunanin ko irin wata kawar mamansa suke yan ayyukan bikin a gidansu. 

Haka Kamal jarumin tayi min kankanta complete hausa novel yaji wannan magana kamar aradu. 

Hajiya da Alhaji da Æ™anwarsa haka suka saka shi a gaba har gidansa, shi dai abin ne ya girmame masa shiyasa ko magana ya kasa kashi sun sashi a gaba dole ya taho. Har dakin amarya, bayan sun zo suka yi musu nasiha suka yi gaba. Kamal na matukar son mahaifansa dan dole ya zauna. 

Amarya da Ango ba wanda ya taba ganin wani, domin amarya Lailah kuka take, itama tabi iyayenta kawai kuma an kawo ta nan an ajiye. Kamal zaune yake a gefen gado ita kuma tana tsakiyar gado. Ya juya ya kalleta yaga da alama karamar yarinya ce, nan da nan kuwa ya kira wayar Hajiya tace lafiya wallahi Hajiya tayi min kankanta yarinyar nan, wallahi Hajiya zan nemo wacce nake so, wannan tayi min kankanta. Hajiya murmushi tayi sannan tayi wani dan karamin ta kashe wayar. 

Nan Kamal wayar Alhaji, wallahi baba tayi min kankanta, a bani dama. Alhaji cewa yayi kamal ka sani ba zan taba cutar da kai ba, shima ya kashe wayan. Kamal bashi da wani zabi yanzu  illa ya rungumi domin yasan cewa duk daren dadewa dole sai yayi aure. Yanzu kuma zance ya riga daya Æ™are.

Ashe lokacin da Kamal ke wannan waya tuni Lailah ta bude mayafinta, nan fa taci karo da wannan kyakkyawan saurayi wayyo daÉ—i, saboda tsabar farin ciki bata san lokacin data dinga murmushi ita kadai ba, ta kura masa idanu tana murmushi. Ai yana juyowa suka hada idanu, yaji kamar an soki zuciyarsa. 

Domin wata kyakkyawar yarinya ya gani cikakkiya kuma hadaddiya. Nan da nan yace mutum ko aljan, cewa tayi nice matarka cikin murmushi. Yace kece wacce Hajiyata suka kawo. Nice. Ba sai ji yayi yarinya ta rungume shi ba, tunda yake bai taba jin dadi irin na yanzu ba, laulausan hannunta ya sauka a bayansa duka cewa ya fita tsayi amma yasan ya samu cikakkiya, kuma mace mai diri. Kirjinta ya sauka akan nasa. Nan da nan yaji gaba daya yana karkarwa domin mace bata taÉ“a rike irin haka ba. Itama Lailah haka take amma tasan menene miji. 

Cikin yan dakiku gaba daya yaji ya motsa, ban san lokacin daya rungumeta, cikin wannan dare amarya da ango ya bude amarya duk da tasha wahala amma cikin soyayya suka yi baccinsu. Da safe Hajiya ta dawo abinda ta gani tayi farin ciki sosai wato har yayi bacci da matarsa. Shikenan suka cigaba da son juna kamar wanda suka kasance hanta da jini, koda yaushe suna Tare. Har yanzu idan Hajiya zata tsokani Kamal sai tace , wallahi Hajiya tayi min kankanta. Sai dai yayi dariya kurum.