Love and romantic hausa novel

Love and romantic hausa novel

Love and romantic hausa novel

Amazing new story about love and romantic hausa novel by Aliyu Maigari is a captivating tale that beautifully explores young love, personal growth, and the journey of relationships. The story of love and romantic hausa novel follows the life of Aliyu Jamil, a young man who falls deeply in love with Zainab, a girl of striking beauty and kindness. The love and romantic hausa novel captures the innocence and intensity of their romance, from their days in school to the eventual development of a lifelong bond.

Maigari's novel stands out for its portrayal of genuine emotions, cultural values, and the simplicity of love in a Hausa setting. The characters are relatable, and the story resonates with readers who enjoy heartfelt romance with a blend of cultural richness. This love and romantic hausa novel is an engaging read for those who appreciate traditional love stories told with warmth and sincerity.


Love and romantic hausa novel part 1

Wannan shine bangare na farko na labari mai taken love and romantic hausa novel wanda muka kawo domin ɗebe muku kewa, kodayaushe burinmu faranta muku zuciya da kyawawan labarai da hikayoyi iri daban daban.

Lokacin da ina makaranta na kasance ina matukar son wata yarinya mai suna Zainab. Zainab ta kasance kyakkyawar yarinya mai kyan gaske, domin fara ce gata doguwa, Allah ya albarkaci Zainab da hanci mai tsini sak irin na labarawa sannan gata da dogon gashi. 

Kullum idan nazo makaranta bana iya kallon Zainab saboda ina matukar jin kunyarta, kai wani lokacin har karkarwa nake idan muka hada idanu. Tana yimin kwarjini sosai, gata da dara daran idanu tamkar madara domin farare ne tas.

Aliyu Jamil sunana kuma yau zan baku labarina nida Zainab Ahmad wacce a yanzu ta kasance matata wacce nake matukar so da kauna, sannan na sawa wannan labari nawa na soyayya love and romantic hausa novel domin tsagwaron soyayya ce a cikinsa. Na kasance dogo sannan kuma baki irin wanda ake cewa black beauty wato wankan tarwada, inada yar doguwar fuska da kananan idanu masu kyau kuma inada baiwar gashi a kaina domin idan nayi aski gashi baya ɗaukar lokaci yake fitowa. Shekarata ashirin da daya domin na soma girma kuma na mallaki hankalin kaina, idan ka kalli fuskata gemu da saje sun soma fitowa wanda suka ƙara yimin kyau sosai a fuskata.

Love and romantic hausa novel
Love and romantic hausa novel part 1

Kamar yadda muka saba nida abokina Fahad kullum ƙarfe takwas muke kama hanyar zuwa makaranta, wani lokacin muna tafiya a ƙasa wata ran kuma akan babur dinsa, yau mun shiga school da wuri inda muka tsaya a bakin kofar ajinmu muna hira. Fahad yace 'Aliyu ga gama assigment dinka na malamin English' cikin firgici nace! assigment kuma? yaushe ya bayar? Fahad yayi sannan yace 'kana nufin baka san malam Adam ya bayar da assigment ba, lallai yau zaka daku kenan' habawa! cikin hanzari nace dan Allah bani naka nayi sharp sharp na kwafa, cikin wasa Fahad yace 'ah haba! amma kanamin wasa ko? to gaskiya bazan bayar ba, nan muka soma guje-guje ni da Fahad muna dariya ina rokonshi ya bani na kwafa.

Muna cikin haka saiga Zainab ta shigo cikin ajin, nan da nan naji na nutsu na samu waje na zauna. Fahad fa ya gane meyasa na tsaya kawai sai ya nufi inda Zainab ke zaune. Cewa yayi 'Zainab good morning? tayi masa murmushi sannan tace Fahad how are you? nan suka soma hira, shine har yake gaya mata wai Aliyu ne baiyi assigment ba. Cewa kai subhanallahi! garin yaya baiyi ba, manta yayi? ni kuma na hana shi ya kwafi nawa.

Sai Zainab ta ɗago kai ta kalleni ina zaune acan desk dinmu. Sai naga ta buɗe jakar makarantarta ta dauko littafi ta taho inda nake, da zuwa tace min ina kwana? na amsa lafiya kamar ina tsoronta, ta bani littafinta tace ta kwafa assigment. Cikin farinciki na soma kwafar assigment dinta gashi ta iya rubutu. Bayan na gama ina kyarma na mayar mata da littafin, a ranar nan haka na wuni ina farinciki ban taɓa jin murna irin ta ranar ba.

Naji wata sabuwar soyayyar Zainab ta ƙara kama zuciyata, inaji kamar zan iya yin komai saboda ita, kullum idan nazo makaranta sai dai nayi mata murmushi kawai amma bana iya yi mata magana saboda kunya. Itama sai dai tayi min murmushi duk da ita wani lokacin tana kiran sunana. 

Love and romantic hausa novel part 2

A cigaba da nishaɗantuwa da wannan ƙasaitaccen labari na love and romantic hausa novel, kuma kada a manta cewa ana bangare na kusa dana karshe akan abinda muka kawo.

Ranar wata Lahadi ba makaranta, mamana ta aike ni na siyo mata kayan miya a kasuwa, haka na ɗauki babur din yayanmu da nufin in tafi dashi, amma ina dubawa sai naga yayi faci, haka na ajiye shi sannan na soma tafiya a kasa. Ina shiga kasuwa na nufi inda ake siyar da kayan miya, na siya tunatar da albasa ina bawa mai kayan miya kudinsa, sai naji ance "Aliyu! ina juyawa sai naga Zainab ce, cikin hanzari nace na'am Zainab kece? tayi murmushi, sannan tace kazo cefane ne? nace wallahi Mama ce ta aikoni.

Itama tazo siyayya ne kasuwa, nan haka naji wata sabuwar kunya ta rufeni domin ko magana da kyar nake yi, tace zata je siyan takalmi ne kuma saita hango ni, nayi dariya, nace muje na rakaki to. Muka kama hanyar shagon siyar da takalmi dama lokacin da wasu yan kudadena bayan ta gama zaben wanda take so, ta tambayi mai kaya yace dubu biyu da ɗari takwas, tace kai!! gaskiya yafi karfina, zata ajiye kenan nace mai kaya sakamin wannan a leda, haka ko ya saka na cewa Zainab mu tafi.

Ta kalleni Aliyu dan Allah ka basshi nace karki damu Zainab wallahi kinfi haka a wajena. Nan Zainab ta karbi takalmin muka wuce, ta tafi gida nima haka. Bayan Zainab ta shiga gida, ta wuce dakinta, inda ta ajiye sabon takalminta, fuskarta cike da annuri domin ta samu irin takalmin da take so, a hankali taji ta soma jin soyayyata a zuciyarta, har ta soma tunanina, gaskiya Aliyu yanada kirki haka tace a zuciyarta. 

Love and romantic hausa novel
Love and romantic hausa novel part 2 

Washe garin ranar Monday na shiga makaranta, bayan anyi break muna zaune ni da Fahad a wata inuwar bishiya. Saiga Zainab tayi sallama muka amsa, ta gaishe damu. Ta kalleni tace Aliyu kai nake nema tun ɗazu, nace Ni? tace eh mana. Ta tashi Fahad yana kallona yana dariya. Na tashi na bita muka tafi aji, wai karatu zan koya mata, nan dai nayi mata abinda zan iya na tafi. 

Tun daga wannan rana naga Zainab ta canja, domin kullum saita neme ni, ni kuma bata san kullum ƙara sonta nake ba. Wata rana bayan na dawo daga masallaci da dare na shiga dakina na kwanta sai kawai bacci ya sace Ni, nan na ganni a wata sabuwar duniya, cike da wasu furanni masu kyau, a bakin wata ƙorama naga Zainab a zaune tana shan iska, cikin farinciki naje wajenta muka zauna tare muna hira, cike da soyayya muke hira Ni da Zainab. 

A haka na farka daga wannan bacci mai daɗi, nine ban koma bacci ba, sai bayan sallar asuba, dana koma bacci sai karfe goma na safe sannan na tashi, a lokacin har anyi break din makaranta mamana nayi tsammanin na tafi makaranta sai ta ganni na fito daga dakina, tace dama Aliyu baka tafi makaranta ba? Nayi hanzari na shirya sannan nayi karin kumallo. 

Love and romantic hausa novel last 

Masu iya magana suka ce aiki ga mai ƙare ka domin love and romantic hausa novel namu anan yazo karshe da fatan an samu nishadi dama ilmantarwa daga cikinsa.

Na shiga aji, na zauna sai na soma dube dube ko zan hango Zainab amma ban ganta ba, na tambayi Fahad yau kaga Zainab. Eh tazo makaranta yau inji Fahad. Kawai na tashi na fita waje ina dube-dube a filin makaranta can na hangota a wata inuwa da sauri na tafi wajenta, da zuwana nayi sallama, ta juyo cike da soyayya ta kalleni, Aliyu kai ne? muka yiwa juna dariya sannan na soma bayani, Wallahi Zainab zuciyata tana jin soyayya mai karfi a tattare dake ina sonki Zainab. 

Zainab ta dafa kirji cikin farinciki tace da gaske? nace wallahi da gaske nake. Haba! nan fa aka soma soyayya mara misaltuwa tsakanina da Zainab. Wannan shine masomin love and romantic hausa novel nawa, bayan wasu lokuta mun saba da juna. 

A haka muka cigaba da love and romantic kauna har muka gama makaranta, kuma muka dora makarantar gaba da sikandire bayan mun gama na samu aiki mai kyau itama Zainab. Haka wannan labarin love and romantic hausa novel ya koma zuwa aure, domin yanzu haka muna zaune nida Zainab a matsayin matata kuma muna zaune lafiya.

Previous Post Next Post