Littattafan hausa novel complete part 1
Labarin Ikram
Sunana Ikram Junaid asalin ƴar garin Kaduna. Na taso a gidan mahaifina cikin yara huɗu duka mata nice ƴar autarsu. Na taso cikin tsananin gata da jin daɗi saboda mahaifina mutum ne mai kuɗin gaske gashi kuma kasancewata ƴar autar gidanmu komai nake so sai na samu idan kuma a wasu lokutan aka ƙi yi mun, haka zan sa kukan taɓara wanda mahaifina sam baya son wannan kukan nawa ko kuma ganin zubar hawayena. Mahaifiyata Hajiya Mariya, wato mommy tana yawan yiwa mahaifina ƙorafin irin sangartanin da yake yi, amma mahaifin nawa Alhaji Junaid sam baya saurarenta, a cewarsa idan bai yiwa uwarsa abin da take so ba wa zai yiwa. Dama haka mahaifina yake cemin "uwata" saboda sunan mahaifiyarsa da naci, asalin sunana Aisha shine ake ɓoyemin da Ikram.
Gaskiyar magana babu yabon kai ni kyakkyawar mace ce, a cikin mata ina cikin rukunin farko a fagen kyawun fuska da diri na halitta. Mazaje tun kamin na kawo minzalin girma suke kawo min farmaƙin soyayyarsu amma ban taɓa kula dasu ba har na gama babbar makarantar sakandire wato ss3. Yanzu haka ina fagen shiga Jami'a a inda takardar ɗaukata a matsayin ɗaliba ta fito a wata makarantar jami'a ta kuɗi mai suna Baze University dake birnin tarayya Abuja. Ƴan uwana wato yayyena guda biyu yaya Samira da yaya Maimuna sunyi aure shekara ɗaya data wuce yanzu haka daga ni sai yaya jidda wacce kullum cikin faɗa muke, muyi faɗa mu shirya kasancewar mu sakonnin juna. Muna yawan gaddama da ita akan ba zan taɓa ganin wani saurayi namiji da zai burgeni wai har naji ina sonsa ba, yayin da ita kuma take ƙaryatani har ma tana cewa irin mu masu cika baki mun fi kowa faɗawa soyayya da zurfi.
A duk lokacin da mukai irin wannan musun da ita sai dai na ji ta kawai, amma ban taɓa hasasowa kaina wai yau gashi ina soyayya da wani namiji ba. Haka kuma musamman yaya jidda tana yawan tuna min cewa yanzu ne zan shiga jami'a kuma tana mai tabbatar min ba zan gama shekara ɗaya cur ba tare da saurayi ba.
Littattafan hausa novel complete part 2
A lokacin data fara faɗa min haka har rigima muka yi. Wai a cewarta iya ƙoƙarin da zan iya yi shine in gama semester ɗaya banyi saurayi ba. Kamar yadda na faɗa a sama cewar na sami gurbin karatu a jami'ar kuɗi ta Baze University inda zan karanci Law, babban burinta bai wuce na ganni na zama cikakkiyar barrister ba, wacce zata tsaya tsayin daka wurin kwato haƙƙin waɗanda aka zalinta.
A yau ashirin da huɗu ga watan september ta kasance rana ta farko a rayuwata ta jami'a, kuma bisa ga al'ada kamar yadda yawancin jami'o'i suke yi a ranar farko, ana gabatar da orientation na ɗalibai wato bi ma'ana shi dai wannan orientation ana yinsa ne domin gabatar da sabbin ɗalibai a department daban-daban na jami'ar kuma haka ce ta kasance a faculty of law wato faculty ɗin mu. Bayan an gama wannan orientation ɗin sai kuma aka sanar da ɗalibai na law cewa ƴan final year wato ƴan shekarar ƙarshe na law suna yin court simulation a cikin wani hall da ake kira da B-29. Shi dai wannan court simulation ɗin wani shiri ne da ake yi wanda za'a zauna kamar zaman kotun gaske da baristoci da kuma alƙali, haka kuma akwai mai ƙara wanda ya shigar da ƙara, haka kuma akwai wanda ake zargin yayi laifi.
Ni ikhram junaid ina cikin waɗanda suka je kallon wannan simulation ɗin, a lokacin da aka fara gabatar da shirin sai prosecutor ya tashi ya karanto case ɗin da za'a yi ya kuma bai wa baristoci damar su gabatar da kansu. Tun daga lokacin da wani ɗan final year law ya miƙe tsaye yayi gyaran murya sannan ya fara magana a nutse yana mai gabatar da kansa a matsayin mai kare wanda ake zargi, tun lokacin hankalina yayi kansa. Ni dai tun da nake ban taɓa ganin namiji mai charisma irin Adnan Sufyan ba, gashi ɗan gayu suit ɗin da ya saka ma kaɗai abar a yabawa ce, domin kuwa suit ce ta georgio armani wannan fitaccen designern kamfanin na ƙasar italiya.
Littattafan hausa novel complete last part
Irin yadda Adnan yake zuba yaran nasara tamkar a cikinsu ya tashi ga kuma uwa uba kyawun sura da yake dashi, ban yi aune ba duk sai naji na raina kaina. Haka dai aka gama wannan court simulation ɗin ba tare dana tsinci komai a cikinsa ba. Bayan an fito daga hall ɗin nan sai muka tafi cafteria ni da wata sabuwar ɗaliba wacce muka saba a wannan ranar ta farko mai suna Rumana. Muna zaune muna hutawa a cikin cafeteria ɗin saboda gajiyar registration kawai sai ga Adnan sufyan wannan ɗalibin na law wanda ya birgeni a court simulation. Da murmushinsa ya zauna a table ɗinmu ya gaishe damu haɗe da tambayar mu komu sabbin ɗalibai ne, muka ce masa eh da haka ya riƙa jan mu da hira har muka saba sosai.
Da farko mun fara ne a matsayin friends ni da Adnan wanda mutane da yawa suke ce min na rabu dashi player ne, a cewarsu mayaudari ne mai wasa da hankalin ƴanmata, wai dama duk shekara sai ya nemi dating sabuwar ɗaliba. Duk da nasan Adnan friend ɗina ne amma sam bana ƙaunar naga wata mace ta raɓe shi indai ba ƙanwarsa muhibba ba. Daga ni har Adnan mun san muna son junanmu to amma ni dai ta ɓangarena sai na barshi a matsayin friend ko don irin yadda yaya jidda take cewa dole nayi saurayi a shekarar farko ta Jami'a. Amma saboda yadda nake shiga damuwa saboda yawan ƙawayensa mata kuma ina ji ina gani babu yadda zanyi tunda nima ɗin kawarsa ce, amma nasan Adnan yana sona kamar yadda nake son sa. Da na gaji da wannan fake friendship ɗin wata rana muna zaune mu biyu kaɗai a cikin lecture hall muna karatu, kawai sai na kalli Adnan nace masa
"Let's make it official..
Ranar da muka fara dating officially a ranar ne yaya jidda ta gan mu a jabi lake. Babu wanda yaya jidda bata kira ba tun daga kan daddy, mommy da sister's ɗinmu sai da ta gayawa kowa nayi boy friend.. Soyayyar mu da Adnan soyayya ce mai cike da tsari, mutunta juna da tsafta haka kuma soyayya ce mai cike da riƙon amanar juna..