Littafin hausa novel complete part 1
"Hello.. Hello.. Wai baka jina ne, ka fito ga mutuniyar can yanzun nan aka sauke ta daga cikin wata dalleliyar mota.
" What!?..
"Au shikenan tsaya kallon ruwa kwaɗo yayi ma ƙafa. Ni dai na faɗa maka za ayi ba kai.
Wata irin dira yayi daga kan gadon sannan ya jawo wata doguwar jallabiyarsa ya zura a jikinsa sannan ya fice daga cikin É—akin a É—ari.
Jamal, kenan yaro ɗan kwalisa, ɗan kwalliya da burga amma yanzu kusan shekara ɗaya kenan da ƴan motsi yana masifar son wata matashiyar yarinya budurwa da tazo gidan yarta amma ya kasa yi mata magana. Jamal son zuhra yake tamkar rai amma wai abun ban haushi ya fito yayi mata magana ya kasa. Mai karatu in taƙaice maka labari dai ita kanta zuhra ta san Jamal ya gama faɗawa tarkon sonta ko kuma kogin begenta. A cikin shekara ɗaya, lokaci ne mai tsawo wanda idan wani abu yana faruwa zai yi wuya ace mutum bai ankare ba in dai har abun ya shafe shi. Kamar yadda aka bayyana, zuhra dai asalin bafulatanar gombe ce wacce aure ya kawo yayarta Aisha garin kano cikin unguwar kundila.
Asalin Labarin...
A lokacin da zuhra ta samu fagen shiga karatu wato admission kenan a jami'ar Bayero sai ya zamana bata da wani masauki face gidan yayarta Aisha.
Tun daga ranar da Jamal ya kyalla ido ya hango zuhra a lokacin sun fito kenan da safe yayarta Aisha zata sauke ta a makaranta a lokacin ma registration take yi, to fa tun a sannan Jamal ya fara neman bayanai a kanta ta hanyar kiran wani abokinsa kuma ɗan layinsu mai suna Babangida wanda yake kwana ya kuma tashi da sanin yawan ƴanmatan da suke unguwar, saboda haka Babangida wanda aka fi sani da bangis ya san kowace yarinya a kundila, walau haifaffiyar kundilar ko wacce tazo, haka kuma ya san bazawara ya kuma san budurwa bugu da ƙari duk yarinyar daya gani ya san daga gidan data fito saboda tsabar sakawa mata na mujiya da yayi.
A lokacin da jamal ya fara ganin zuhra ya san babu makawa bangis ya san da wanzuwarta a wannan unguwar shi yasa ya kira shi ya kuma faɗa masa gidan daya ga baƙuwar yarinyar, a take kuwa a wannan wayar bangis ya shaida masa sunanta ya kuma gaya masa cewa karatu tazo yi a jami'ar Bayero. Tun daga wannan ranar jamal ya maida wurin gidansu zuhra tamkar mai yin ɗawafi saboda kai komon da yake yi a wurin. Da sassafe zai zo ya tsaya don kawai ganin fitar ta, haka kuma daya dawo daga duk inda yake to fa anan ƙofar gidansu zuhra zai ci birki, a taƙaice dai anan layin su zuhra ya tare gaɓa daya. Da yake yau da gobe bata barin komai tuni zuhra tayi ƙawaye da kuma abokai duk a cikin unguwar kundila. Haka kuma duk cikin matasan dake unguwar da kuma ƴanmatan cikinsu kusan kowa yasan irin mahaukacin son da jamal yake yiwa zuhra sai dai kuma abin mamakin shine kasa tunkarar ta da yayi.
Littafin hausa novel complete part 2
Tun abokansa suna tsokanarsa har suka gaji sai dai jifa-jifa idan zance ya taso ko kuma idan an haɗu a majalisa ana hira sai a riƙa masa tsiya.
A ɓangaren zuhra kuwa, wata yarinya mai suna nuratu wacce take ƙawace ga ƙanwar jamal mai suna Hafsat ita ta fara faɗawa zuhra cewa yayan ƙawarta yana sonta amma a wancan lokacin dariya kawai ta ɗanyi sannan ta shiriritar da zancen. Bata sake jin labarinsa ba kuma sai a bakin bangis wato Babangida matashin da jamal ya fara yiwa magana akanta. Da yake shi bangis bayan irin sa idon da yake wa matan layi to dukansu yana shiri dasu, komai miskilancin mace sai bangis yasan yadda yayi suka saba koda gaisuwa ce kawai zata haɗa su.
Bangis shine mutum na biyu daya tabbatarwa zuhra cewa akwai wani wanda yake bala'in sonta amma kuma wai ya kasa yi mata magana, da farko lokacin da nuratu ta faɗa mata, iya gaskiyarta tayi tunanin zolaya ce amma da bangis ya faɗa mata ta yadda. Duk da cewar jamal bai taɓa tunkararta ba, amma zuhra tana sane da irin kai komo da jeka ka dawo ɗin da jamal yake a ƙofar gidansu, amma ita abin da yake bata dariya wai ya kasa mata magana, ita dai zuhra ta ayyana a ranta cewar a iya ganin da take masa sam bashi da wata makusa saurayi ne normal kuma koda bata san yana sonta ba, koda bata taɓa ganinsa ba, da ace zasu haɗu a wani wuri yayi mata magana, to baya cikin irin mazan da za taki bawa fuska.
Irin zaryar da jamal yake a layin su zuhra domin kawai ya riƙa ganin sahibar tasa, wasu lokutan a maimakon shi ya ganta, ita take ganinsa. Wasu lokutan idan jamal ya tsaya da matasan layin suna hira ko musun kwallon ƙafa sai hankalinsa ya ɗauke daga fitowa ko kuma shigar zuhra gida, a irin waɗannan lokutan sai dai kawai tayi dariya ko ta girgiza kai ta wuce, idan kuma jawad yana cikin samari ana hira daya ankara da zuhra sai ya saukar da kansa ƙasa ko ya waske. Irin wannan abin yana bawa zuhra dariya sosai haka kuma irin wannan kunyar tata da jamal yake ji sai ya shiga ranta sosai ba tare da ta ankara da hakan ba.
Littafin hausa novel complete last
A taƙaice dai ita kanta zuhra idan tayi kwana biyu bata ga jamal ba bata jin daɗi.
A kwana a tashi haka matasan nan suke soyayya daga nesa duk lokacin da suka haÉ—a idanu sai su aikawa juna murmushin soyayya, da jamal yaga haka ya fuskanci tabbas zai iya samun shiga a wurin masoyiyar tasa sai ya saka ranar da zai je wurin ta a karo na farko. To a wannan ranar ne aka yi masa waya cewar ga zuhra can wani gaye ya sauke ta daga cikin wata dalleliyar mota hakan ne yasa ya fito a sukwane daga cikin gidansu, koda jamal ya isa layin su zuhra sai aka ce masa ai ta shige gida mai motar kuma ya tafi.
Haka jamal ya tashi hankalinsa har dare sannan ya shirya yayi wa gidan su zuhra tsinke, yana zuwa bakin gate sai yasa waya ya kirata, tana É—auka bayan yayi sallama ta amsa sai ya gabatar da kansa ta hanyar faÉ—ar sunansa. Murmushi zuhra tayi wanda sai da jawad yaji sautinsa ta cikin wayar nan har da wani lumshe idonsa
"Sai yau kenan kaga ya dace kazo?
Zare ido yayi jin zazzaƙar muryar zuhra data jefo masa tambayar nan.
Yana nan yana jiranta haka ta fito suka sake gaisawa. Tun daga wannan ranar masoyan biyu suka É—inke daga nan sai tarihi.