Kurkukun kaddara hausa novel
Our new posted novel Kurkukun Kaddara hausa novel by Umar ɗan kwarai delivers a suspenseful and emotionally charged narrative that grips readers from the first chapter. The story masterfully intertwines themes of fate, betrayal, and survival, presenting a high-stakes tale filled with tension and unexpected twists.
Kurkukun kaddara begins with a chilling late-night phone call that shakes the protagonist out of his slumber. He is a middle-aged man of 40, caught off-guard by a dire warning from his friend Aminina, whose life is hanging by a thread. From the moment Aminina's call is cut short by a gunshot, the protagonist is thrown into a whirlwind of danger that threatens not only his life but that of his young daughter, Angel.
Dankwarai skillfully captures the atmosphere of fear and urgency as the protagonist races to save his daughter. The descriptions are vivid, particularly in the moments when he witnesses Aminina's brutal murder via a video call, setting the stage for the harrowing events that follow. The writing is immersive, pulling the reader into the protagonist's inner turmoil as he struggles to protect his daughter from the same fate.
The suspense intensifies as the protagonist and Angel flee into the night, pursued by mysterious and dangerous men. The psychological weight of the father’s guilt is palpable, as he contemplates the ramifications of his actions as a journalist, which have led to this tragic series of events. The reader is drawn into his internal conflict, particularly when he is forced to make a heartbreaking decision about Angel’s fate during their escape.
In addition to the action-packed plot, the emotional core of the story lies in the father-daughter relationship. Angel’s innocence contrasts sharply with the violent reality they are thrust into, and her confusion and fear heighten the emotional stakes of the story. The protagonist's overwhelming sense of failure and desperation is deeply moving, especially when he is faced with the thought of sacrificing Angel to spare her from the hands of their pursuers.
Kurkukun Kaddara is not just a story about escaping physical danger but also a meditation on the consequences of one’s choices and the price of involvement in dangerous affairs. Dankwarai’s use of foreshadowing and suspense keeps the reader on edge, making them eager to know what will happen next.
Kurkukun kaddara hausa novel part 1
A yau da zafi muka dawo domin gabatar muku da sabon labari mai take kurkukun kaddara, dan haka muna cewa asha karatu lafiya.
Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana bada sauti tik-tik-tik. Dare ya tsala, lokaci kuma ya nuna ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Wayar da aka ajiye saman bed-side drawer, ƙirar Samsung Galaxy, ta soma ruri da ƙarfin gaske. A lokacin ya yi nisa a barci, kiran yana shigowa har sau uku amma ba ya farkawa. A kira na huɗu ne sautin ya daki kunnensa, a firgice ya farka yana ambaton sunan Allah. Jikinsa sanye da singlet da gajeran wando fari, ya kai shekaru 40 a duniya, launin fatarsa kuwa wankan tarwaɗa. Da ƙyar yake iya ware manyan idanuwansa a kan katafaren gadonsa kafin ya mayar da kallonsa kan agogon bangon. Tafin_hannunsa_ya_ kai ya_shafi fuskarsa, a sanyin_murya ya_ambaci sunanta: "Angel!"
Kafin_ya zame_hannunsa_daga_kan_fuskarsa, wani_kiran_ya_sake_shigowa. A hanzarce ya ɗauki wayar daga saman drawer, cike da mamaki. Wanene yake_kiranshi a irin_wannan lokaci? kuwa_lafiya?
Da ya duba allon wayar, sunan Aminina ya bayyana. Ya sauke ajiyar zuciya tare da ɗaga kiran. Tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo sautin harbin bindiga. A gigice ya furta, "Aminina!" Kafin ya ƙarasa rufe bakinsa, muryar Amininsa ta katse masa hanzari. A ruɗe_yake_faɗin, "Na bani na_lalace, shikenan tawa_ta_ƙare."
A firgice ya dakatar da shi. "Ka nutsu ka yi mini bayanin me ke faruwa?"
"Sun kama ni ina yi musu leƙen asiri. Yanzu haka_sun_biyo_motata, na san kasheni zasu yi, kaima kuma ba zasu_ƙyaleka ba. Ba na so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi. Don Allah, na roƙe ka, ka gudu kai da Angel. Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu yana cikin memory ɗina, ita kaɗai ce hujjar da za ta tona asirinsu..." Bai kai ƙarshen maganar ba, kiran ya ɗauke.
A gigice ya ƙara kiran, amma sai ya manta cewar wayar ta riga ta katse. Lokacin da ya sake kira, aka ɗaga cikin sa’a, amma abin da bai taɓa tsammani ba ya faru. Kururuwa mai razanarwa ta ji ta fito daga wayar, sannan wata murya ta ce, "Idan kana son sanin me ke faruwa, ka kalli allon wayarka."
Jikinsa na rawa, ya ɗago da wayar yana kallon allon yayin da suka canza kiran zuwa video call. Saboda tsananin firgici, a ruɗe ya diro daga gadon. Idanuwansa sun firfiro kamar ƙwayar idonsu za ta faɗo ƙasa. Motar Amininsa ta bayyana tana ci da wuta. Akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun Amininsa ta tagar motar. Wuta tana cin naman jikinsa. Zufa ta fara kwarara daga fuskarsa, a gigice yake faɗin, "No, no!" Suka katse kiran.
Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya darsu masa, ya zube gefen gadon. Bai san me yake yi masa daɗi a duniya ba. Yana cikin wannan yanayin, muryar Amininsa ta dawo masa: "Ka gudu kai da Angel, ba na so laifina ya shafe ku."
Tabbas za su dawo kansa ne don su kashe shi kamar yadda suka kashe Amininsa. Ba komai ya fi damunsa ba face ƴarsa ɗaya tilo da yake da ita, Angel. A matuƙar ruɗe, ya miƙe. Babu ko jallabiya a jikinsa, ya ɗauki key ɗin motarsa, cikin ruɗani wardrobe ya dosa a matsayin ƙofar fita. Har sai da kansa ya bugu kafin ya ankare. Ya nufi ainihin ƙofar da sauri, ya fito daga bedroom ɗinsa da ke a ƙasa ya nufi babban falon. Kai tsaye ya haura upstairs. A gigice yake tattaka matattakala, bai tsaya ko'ina ba sai ɗakin Angel.
Kurkukun kaddara hausa novel part 2
Bugu ɗaya ya yi ƙofar ɗakin ta buɗe. Duhu ya mamaye dakin, ya kunna hasken. Nan take haske ya gauraye ko’ina. Ya dubi Angel da ke kwance cikin lallausan bargo. A hanzarce ya ƙarasa, ya ɗaga ta yana kwala mata kira, "Angel, Angel my daughter! Azeezaty!" Babu alamun za ta farka. A hautsine ya ɗauke ta ya saba ta saman kafaɗarsa, da sauri ya fito daga ɗakin, ya sauko downstairs, kai tsaye ya fita waje wurin da motocinsu suke. Ya buɗe motar Range Rover, ya kwantar da Angel a baya, sannan ya zauna a gaban sitiyarin motar. A gaggauce ya ja motar, a bakin gate ya tsaya, ya fito ya buɗe gate ɗin sannan ya koma cikin motar ya ja da gudu.
Fitar motarsa ke da wuya, wasu danƙara-danƙaran motoci kusan su shida suka nufo shataletalen da zai kai gidan. Sun hango motarsa, suka fara bi da matsiyacin gudu. Hankalinsa ya tashi sosai, saboda ya hango motocin a cikin madubin motarsa. Hakan ya sa ya ƙara gudu, yana ambaton La'ila'ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Bai san inda zai dosa ba, sai kawai gudun ceton rai yake yi.
Shessheƙar kukan Angel ce ta dawo da shi cikin hayyacinsa. Ta farka sakamakon gudun da yake yi, har kanta ya bugu da jikin motar, hancinta ya fashe jini ya soma zuba...
A ruɗe take furta, "Daddy... me ke faruwa? Ina za ka tafi a cikin wannan duhun dare?"
Ƙaramar yarinya ce da ba za ta wuce shekaru goma sha ɗaya a duniya ba, kuma maganarta da ƙyar take fita saboda tsananin halin da take ciki. Hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana sanin shiga aikin jarida fiye da kowane tunani. Shi ne silar jefa kansa da yarinyarsa cikin wannan mawuyacin hali.
"Angel, am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya cetonki ba. Ba zan iya jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba," ya faɗa cikin kuka, yayinda ta sanya tafin hannunta ta dafe hancinta da ke zub da jini. Jinin_ya ɓata_fuskarta, cikin_kuka ta_ƙara cewa, "Daddy! Hancina yana zubar da jini, zan mutu." Gaba ɗaya ya rikice, ya rasa abin da zai yi. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya furta "sorry" kawai yake iya yi.
Har yanzu motocin da ke binsu na nan, lokacin da ya fara jin sautin alburushin bindiga a bayan motarsa, cikin gigice ya yi wanka da motar cikin wani daji mai duhu. Shi kansa bai san inda zai nufa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar. A ruɗe ya yi parking, ya fito da sauri ya zagaya motar, jiki na kyarma ya ɗauko Angel daga kujerar baya. Daga ita sai rigar bacci, sumar kanta ta rufe fuskarta. Da gudu ya shige dajin da ita a kafaɗarsa yayin da take saɓe a saman kafaɗarshi. Hasken motarsa da ya bari a kunne ne kawai ke haskaka gabansa.
Yayin da yake gudun nan, ba tare da ya lura ba, ya taka wani ƙarfe mai tsatsa da ke tsaye cikin ƙasa. Kaifinsa kamar wuƙa, ya shiga tafin ƙafarsa ya fito ta sama. Wani irin raɗaɗi mai tsanani ne ya ratsashi, tsikar jikinsa ta miƙe. Jini ya wanke ƙafarsa, amma ya kasa motsawa daga tsayen da yake. A hankali ya furta, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un," cikin rawar murya.
Kurkukun kaddara hausa novel part 3
Muryar Angel ce ta katse shi, "Daddy, mu koma gida, nan fa daji ne, akwai kura da zaki za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?" Ta yi tambayar tare da shassheƙar kuka.
Cikin sanyin murya ya amsa mata, "Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne." Ta zagayo da hannayenta ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa. "Daddy, to mu tashi-daga-mafarkin, Angel_tsoro take ji." Tamkar_zai fashe_da kuka_haka_yake ji.
A tsiyace suka cigaba da gudu cikin dajin. Lokacin da ya ji sautin alburushi daga baya, bai san lokacin da ya fisgi ƙafarsa daga ƙarfen ba, duk da cewa jini na kwaranya. Ya cigaba da jan ƙafarsa har ya ƙaraso kusa da wani rami mai zurfi wanda ke cike da ruwa. Zuciyarsa ta raya masa ya jefar da Angel cikin ruwan, ya fi son ta mutu cikin ruwa fiye da mutuwa a hannun miyagun da ke binsu, waɗanda ba su da imani. In suka kama mutum, fetur suke zuba masa su ƙone shi har lahira.
Ya yi zurfi cikin wannan tunani yayin da Angel ke cigaba da kuka. Jin ƙarar motocin miyagun yasa shi dawowa cikin hayyacinsa. Allah Sarki, yana jin sautin ƙarar motocinsu, cikin yanayin tsoro da tashin hankali, ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita cikin ruwan. Tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfi, yana jiyo sautin kururuwarta.
Ba ƙaramin tashin hankali ba ne ga uba ya zama silar mutuwar ɗiyarsa. Saboda tsananin kuka jikinsa har jijjiga yake yi. Ya tsani kansa gaba ɗaya. Don tuni ya cire rai da rayuwar duniya, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi. Jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin, wani irin jiri ne ya soma kwashe shi, nan take ya yanke jiki ya faɗi ya suma.
A lokacin ne motocin miyagun suka iso. Bayan sun yi parking, suka kewaye shi. Wasu samari ne manya-manya suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a fuskokinsu. Sun yi shigar baƙaƙen kaya, da alama bodyguards ne, suna tare da iyayen gidansu da suka fito daga motocin bayan sun buɗe musu ƙofar.